Wednesday, June 19, 2019

Kashi 60 Cikin Dari NaTsoffin Kwamishinonin Ganduje Ba Za Su Dawo Ba 

Jaridar Daily Trust ta gano cewa kashi 40 cikin dari na tsoffin kwamishinonin jihar Kano ne kawai za su dawo matsayinsu a wa'adin mulkin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na biyu. 

Wata majiya mai tushe da ke da kusanci da gwamnan, wadda ta nemi kar a bayyana sunanta, ta bayyana wa jaridar cewa kashi 60 ciki dari na kwamishinonin da suka kammala wa'adinsu a 'yan kwanakin baya ba za su dawo kujerunsu ba a zangon mulkin gwamnan na biyu. 

A dangane da jawabin majiyar, da yawan kwamishinonin ba za su dawo ba sakamakon gaza yin abin a-zo-mu-gani a zangon mulkin gwamnan na farko. 

Ya ce, " A yanzu dai, mutum dari ne ke takarar cike guraben kujerar kwamishina. Wadannan mutanen sun fito daga bangarori daban-daban. Wasu daga cikin 'yan takarar na daga bangaren tsohon gwamna, Malam Ibrahim Shekarau, wasu na daga bangaren tsohon mataimakin gwamna, Farfesa Hafiz Abubakar, sannan kuma wasu sun fito daga bangaren tsohon kwamishin kasa da safiyo, Architecture Aminu Dabo." 

Ya kara da fadin cewa Gwamna Ganduje ya dauki lokaci mai tsaho domin zaben wadanda suka fi cancanta ga jihar. Gwamnan ya shimfida sharudda na zabar kwamishinonin kuma yana bin su cikin tsanake domin gudun zaben tumin dare.


Daga Wakilinmu Yaseer Kallah 

No comments:

Post a Comment

Popular Posts