Friday, June 21, 2019

Cin Zarafin Gwamna Ganduje A Cikin Waka Ya Janyo Wa Sanannen Mawaki Daurin Shekaru Biyu 
Wata kotun majistare ta yanke wa wani mawaki mai suna Muhammad Yusuf hukuncin daurin shekara biyu a gidan kaso sakamakon keta haddin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a cikin wata waka. 

Muhammad Yusuf, wanda aka fi sani da AGY, ya rera wata waka da sunan yabon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II amma ya bige da yi wa Gwamna Ganduje zambo a kan zargin cin kudi, kirkirar sabbin masarautu a jihar Kano da kuma zargin magudin zabe.

A cikin wasu baitukan wakar ne har yake ikirarin cewa Gwamnan zai iya sayar da mai dakinsa (Gwaggo) saboda kudi. 

Jami'an 'yan sanda sun damke mawakin a daren Litinin tare da gurfanar da shi a gaban Mai Shari'a Aminu Gabari na kotun Noman's Land.

Yayin da take gabatar da shari'ar a ranar Laraba, kotun ta sami AGY da laifika uku: sakin wakar ba tare da amincewar hukumar tace finafinai da dabi'u ta jihar Kano ba, sakin bidiyo ba tare da amincewar ita dai hukumar ba, da kuma cin zarafi da bata wa Gwamna Ganduje suna.

A kan laifi na daya da biyu, kotun ta yanke wa mawakin daurin shekara daya, watanni shida  a kan kowanne laifi ko kuma ya biya Naira 100,000, shi ma N50,000 a kan kowanne laifi. Amma a kan laifi na uku, ta yanke masa daurin shekara daya ba tare da zabin tara ba.

Daga Wakilinmu Yaseer Kallah 


No comments:

Post a Comment

Popular Posts