Monday, June 17, 2019

Allahu Akbar! Abubuwa 15 Game Da Shugaba Muhammad Mursi.1- An haifi Mursi a jihar Sharqiyya a Masar a shekarar 1951 ya rasu 2019 (shekaru 68). Ya na da mata daya da 'ya'ya biyar, maza hudu mace daya.

2- yayi digiri na farko a fannin Engineering a shekarar (1975), da na biyu a shekarar (1978) a kan Metals Engineering duk a Jami'ar Alkahira (Cairo University).

3- Ya tafi Amurka inda ya yi digirinsa na uku a Jami'ar (Southern California University) a shekarar 1982, inda ya karantar a Jami'ar har zuwa shekarar 1985

4- Bayan dawowarsa ya karantar a Jami'ar Zaqaziq a Masar daga shekarar 1985 zuwa 2010. , inda ya rike bangaren (Materials Engineering) a Jami'ar.

5- Ya shiga cikin kungiyar 'Yan'uwa Musulmi a shekarar 1977 inda ya rike makamai da dama a cikin kungiyar.

6- Mursi ya cigaba da gwagwarmayar siyasa, inda ya yi takara lokuta da dama a matakin majalisa ta kasa. ya zama dan majalisa a shekarar 2000.

7- Kungiyarsa ta 'Yan'uwa Musulmi ta tsaida shi a matsayin dan takarar matakin shugaban kasa, inda aka kara tsakanin manyan yan takara guda biyar a kasar bayan boren da ya yi awon gaba da shugaba Muhammad Husni Mubarak a shekarar 2011

8- Mursi ya ci nasarar zama shugaban kasa na farko bayan lashe zaben da ya yi da kashi 52% a kan babban abokin hamayyarsa Ahmad Shafiq a shekarar 2012 , a zaben da ya zamto  mafi tsafta  a tarihin Masar.

9- Ministan tsaron da ya nada Abdulfattah al-Sisi ya yi awon gaba da shi bayan zanga-zangar da 'yan adawa da shi  musamman (secularists) su ka yi akan dole ya sauka ya shirya wani zaben cikin gaugawa su na masu zarginsa da kokarin cusa musulunci a tsarin gwamnatinsa da karawa Kansa karfin iko.

10- Sisi wanda ya samu cikakken goyon baya daga wadansu daga cikin gwamnatocin kasashen waje na larabawa da da Isra'ila ya yi amfani da damar wajen shirya juyin mulki ga shugaba Mursi a shekarar 2013

11- Magoya bayan Mursi sun cigaba da gudanar da zanga-zangar lumana ta nuna rashin amincewarsu da juyin mulkin da Sisi  ya yi wa zababben shugabansu, kuma ya ke cigaba da tsare shi, tareda wadansu dubban magoya bayansa, da kashe wasu, da tilastawa da dama daga cikinsu yin gudun hijira zuwa kasashen ketare. Sisi ya aiwatar da kisan kiyashi ga magoya bayan Mursi, wanda mafi muni shine kisan da sojoji su ka yi wa magoya bayan Mursi mutum 2000+ da su ka taru su ka yi  zaman dirshen a dandalin Rabia da ke Nasr city a cikin birnin Alkahira.

12- A shekara daya da yayi yana mulki, Mursi ya samu kauna ta ban mamaki daga al'ummar larabawa da sauran musulman duniya, wanda su ke ma kallon jagoran da zai dawo musu da kimarsu a duniya, musamman yanda ya ke nuna damuwarshi da al'ummar musulmi da yadda ya ke nuna goyon bayan shi ga mutanen Palastinu da Zirin Gaza.

13- A daya daga cikin zqman da aka yi bayan gabatar da shi a kotu, Mursi ya bayyanawa kotu cewa rayuwarshi na cikin hatsari, amma ba a dau wani mataki ba.

14- Gidan talabijin din  Masar ya sanar a ranar litinin 17/6/2019 cewa Mursi ya rasu a kotu yayin da ake masa shari'a , amma wasu na ganin wannan shiri ne kawai na boye hakikanin dalilin rasuwarshi, musamman da ya ke an hanashi magani a kurkuku.

15- Dr. Muhammad Mursi cikakken mahaddaci Alkur'ani ne mai kishin addininsa da al'ummarsa, wanda ke kokarin baiwa al'ummarsa da addinin sa kariya duk inda ya samu kansa kuma ya Samu dama.

Muhammad Mursi daya ne daga cikin miliyoyin musulmai a duniya da ke gwagwarmayar dawowa al'umma da karfinta da izzarta ta kowane bangare, kuma su ke bada jinanensu a matsayin farashin wannan aiki, kuma ba za su taba juya baya ba har sai hasken Allah ya cika.

Muna Rokon Ubangiji Allah yakai haske Kabarin shi.

No comments:

Post a Comment

Popular Posts