Friday, June 21, 2019

Alkawura 30 Da Shugaba Buhari Ya Dauka A Wa'adin Mulkin Shi Na Next Level
Cibiyar ’Yan Jarida ta Kasa da Kasa (IPC), ta fitar da bayanai na alkarurran da Shugaba Muhammadu Buhari ya dauka a kamfen din zaben shugaban kasa a 2019.

Cikin jawabin da wannan kungiya ta fitar wanda Jami’in Shirye-shirye, Sanmi Falobi ya sa wa hannu, ya ce Buhari ya yi wadannan alkawurra a lokutan kamfen din sa.

Wadannan alkawurra IPC ta tsakuro su ne daga jaridun The Nation, The Punch, Daily TRUST, Vanguard, This Day, Leadership da kuma Nigerian Tribune.

ALKAWURRA 30 DA BUHARI YA SAKE DAUKA ZABEN 2019

1. Za a dauki wadanda suka kammala digiri su milyan 1 a karkashin N-Ppower, sannan kuma a koya wa wasu milyan 10 sana’o’i a karkashin hadin guiwa da kamfanoni masu zaman kan su.

2. Za a kara yawan daliban da ake ciyarwa daga milyan 9.3 zuwa milyan 15. Za a kara samar wa masu sayar abinci har su 300,000 ayyukannyi kenan.

3. Za a kammala titin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano, wanda aka faro daga Lagos da nufin karasa shi zuwa Kano.

4. Za a kammala titin jirgin kasa daga Fatakwal zuwa Maiduguri.

5. Za a kammala titin jirgin kasa daga Itakpa zuwa Warri ya zarce Abuja ta hanyar Lokoja.

6. Za a kammala aikin gadar Kogin Neja ta biyu da babban titin da ya hade Warri, Jihar Delta zuwa Oron a Jihar Akwa Ibom zai bi ta Kaiama da Fatakwal a jihar Bayelsa da Ribas.

7. Za a kafa Bankin Al’umma mai suna Moni Bank.

8. Za a gina tsarin bayar da lamunin da ya kai naira milyan daya ga kananan ‘yan kasuwa ko ‘yan tireda

9. Za a kara yawan masu cin moriyar Trader Moni, Market Moni da Farmer Moni daga su milyan 2.3 zuwa milyan 10.

10. Za a kara yawan mata a cikin gwamnati, ta yadda yawan su zai kai kashi 35 bisa 100.

11. Za a kara daukar matasa a matsayin hadimai ga ministoci da kuma ta fannin saka su a gurabun wasu nade-nade a hukumomin gwamnati.

12. Za a kirkiro wani shirin cicciba matasan da suka kammala sakandare ta hanyar yin amfani da matasan da aka dauka aiki a karkashin ofishin ministoci da sauran ma’aikatu.

13. Za a sake tsarin manhajar karatu da inganta fasalin tunanin koyo da koyarwa.

14. Za a ci gaba da rike malamai masu koyarwa a makarantun gwamnati na firame da sakandare tare da samar da tsarin amfani da kwamfutoci wajen ilmantarwa.

15. Za a rika gyara makarantu 10,000 tare da saka musu kayan koyarwa na zamani a duk shekara.

16. Za a kammala titina 365 da aka fara a fadin kasar nan.

17. Za a samar da kayan more rayuwar al’umma tare da inganta tattalin arziki.

18. Za a karasa yi wa Boko Haram kwaf-daya tare da kawar da sauran matsalolin tsaro.

19. Za a kawar da cin rashawa da habbaka tattalin arziki.

20. Za a kafa wuraren sarrafa kayayyakin masana’antu a dukkan shiyyoyin kasar nan shida.

21. Za a kafa cibiyon aikin masana’antu na musamman 109 fadin kasar nan, inda za a kafa daya a kowace shiyyar mazabar sanata daya.

22. Za a inganta hanyoyin gaggauta fitarwa da sayar da kayan da ake sarrafawa zuwa kasashen ketare.

23. Za a inganta hanyoyi da dabarun korar fatara da yunwa.

24. Za a tabbatar da an kammala aikin Madatsar Ruwan Samar da Hasken Lantarki da Mambila da Gadar Mambilla.

25. Za a tabbatar da an gina titin jirgin kasa daga Makurdi zuwa Maiduguri.

26. Za a kammala ginin gadoji a yankunan Kogin Benuwai cikin karamar hukumar Ibi.

27. Za a ci gaba da inganta harkokin noma ta hanyar bin matakan bai wa ayyukan gona muhimmanci. Tare da samar da takin zamani a wadace ga manoma.

28. Za a farfado da Masana’antar Karafa ta Ajaokuta.

29. Za a tabbatar da kammala Tashar Hasken Lantarki ta Zungeru.

30. Za a nada mutane sahihai, nagari ba gurbatattu ba a mukaman ministoci.

Buhari ya sa hannu kan wata sabuwar doka da za tayi maganin barayin gwamnati
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka hannu kan dokar hadin gwiwa wurin yakar masu laifi wato 'Mutual Assistance in Criminal Matters Act, 2019' domin inganta yaki da rashawa a Najeriya da kasashen ketare.

Ita Enang, babban mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan ayyukan Majalisar Tarayya ne ya bayar da sanarwar a ranar Juma'a a Abuja.

A cewarsa, an kafa sabuwar dokar ne domin Najeriya da kasahen duniya su rika taimakawa juna wurin kama masu laifi kamar gano idan suka boye, neman shaidu da wasu takardun da za su taimaka wurin gano masu laifin.

Ya ce wasu daga cikin dalilan da yasa aka kafa dokar sun hada da: 

"Binciko kayayaki da kadarorin da masu laifi suka sace, kwato kayayakin sata da wasu laifukan.

"Gano sakonni da masu laifi ke aikawa junansu da sa ido kan su."
"Karbo kadarorin da aka kwace da kuma neman taimako daga kasashen ketare muddin bai saba dokar kasashen ba.

"Attorney-Janar na kasa shine ke da wuka da nama wurin karbar bayyanai daga wasu kasashe da kuma neman alfarma wurin kasashen kan duk wani abu da ya shafi wannan dokar."

Hadimin shugaban kasar ya ce dokar za ta fara aiki daga ranar 20 ga watan Yunin 2019.

Cin Zarafin Gwamna Ganduje A Cikin Waka Ya Janyo Wa Sanannen Mawaki Daurin Shekaru Biyu 
Wata kotun majistare ta yanke wa wani mawaki mai suna Muhammad Yusuf hukuncin daurin shekara biyu a gidan kaso sakamakon keta haddin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a cikin wata waka. 

Muhammad Yusuf, wanda aka fi sani da AGY, ya rera wata waka da sunan yabon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II amma ya bige da yi wa Gwamna Ganduje zambo a kan zargin cin kudi, kirkirar sabbin masarautu a jihar Kano da kuma zargin magudin zabe.

A cikin wasu baitukan wakar ne har yake ikirarin cewa Gwamnan zai iya sayar da mai dakinsa (Gwaggo) saboda kudi. 

Jami'an 'yan sanda sun damke mawakin a daren Litinin tare da gurfanar da shi a gaban Mai Shari'a Aminu Gabari na kotun Noman's Land.

Yayin da take gabatar da shari'ar a ranar Laraba, kotun ta sami AGY da laifika uku: sakin wakar ba tare da amincewar hukumar tace finafinai da dabi'u ta jihar Kano ba, sakin bidiyo ba tare da amincewar ita dai hukumar ba, da kuma cin zarafi da bata wa Gwamna Ganduje suna.

A kan laifi na daya da biyu, kotun ta yanke wa mawakin daurin shekara daya, watanni shida  a kan kowanne laifi ko kuma ya biya Naira 100,000, shi ma N50,000 a kan kowanne laifi. Amma a kan laifi na uku, ta yanke masa daurin shekara daya ba tare da zabin tara ba.

Daga Wakilinmu Yaseer Kallah 


Wednesday, June 19, 2019

Kashi 60 Cikin Dari NaTsoffin Kwamishinonin Ganduje Ba Za Su Dawo Ba 

Jaridar Daily Trust ta gano cewa kashi 40 cikin dari na tsoffin kwamishinonin jihar Kano ne kawai za su dawo matsayinsu a wa'adin mulkin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na biyu. 

Wata majiya mai tushe da ke da kusanci da gwamnan, wadda ta nemi kar a bayyana sunanta, ta bayyana wa jaridar cewa kashi 60 ciki dari na kwamishinonin da suka kammala wa'adinsu a 'yan kwanakin baya ba za su dawo kujerunsu ba a zangon mulkin gwamnan na biyu. 

A dangane da jawabin majiyar, da yawan kwamishinonin ba za su dawo ba sakamakon gaza yin abin a-zo-mu-gani a zangon mulkin gwamnan na farko. 

Ya ce, " A yanzu dai, mutum dari ne ke takarar cike guraben kujerar kwamishina. Wadannan mutanen sun fito daga bangarori daban-daban. Wasu daga cikin 'yan takarar na daga bangaren tsohon gwamna, Malam Ibrahim Shekarau, wasu na daga bangaren tsohon mataimakin gwamna, Farfesa Hafiz Abubakar, sannan kuma wasu sun fito daga bangaren tsohon kwamishin kasa da safiyo, Architecture Aminu Dabo." 

Ya kara da fadin cewa Gwamna Ganduje ya dauki lokaci mai tsaho domin zaben wadanda suka fi cancanta ga jihar. Gwamnan ya shimfida sharudda na zabar kwamishinonin kuma yana bin su cikin tsanake domin gudun zaben tumin dare.


Daga Wakilinmu Yaseer Kallah 

Monday, June 17, 2019

Allahu Akbar! Abubuwa 15 Game Da Shugaba Muhammad Mursi.1- An haifi Mursi a jihar Sharqiyya a Masar a shekarar 1951 ya rasu 2019 (shekaru 68). Ya na da mata daya da 'ya'ya biyar, maza hudu mace daya.

2- yayi digiri na farko a fannin Engineering a shekarar (1975), da na biyu a shekarar (1978) a kan Metals Engineering duk a Jami'ar Alkahira (Cairo University).

3- Ya tafi Amurka inda ya yi digirinsa na uku a Jami'ar (Southern California University) a shekarar 1982, inda ya karantar a Jami'ar har zuwa shekarar 1985

4- Bayan dawowarsa ya karantar a Jami'ar Zaqaziq a Masar daga shekarar 1985 zuwa 2010. , inda ya rike bangaren (Materials Engineering) a Jami'ar.

5- Ya shiga cikin kungiyar 'Yan'uwa Musulmi a shekarar 1977 inda ya rike makamai da dama a cikin kungiyar.

6- Mursi ya cigaba da gwagwarmayar siyasa, inda ya yi takara lokuta da dama a matakin majalisa ta kasa. ya zama dan majalisa a shekarar 2000.

7- Kungiyarsa ta 'Yan'uwa Musulmi ta tsaida shi a matsayin dan takarar matakin shugaban kasa, inda aka kara tsakanin manyan yan takara guda biyar a kasar bayan boren da ya yi awon gaba da shugaba Muhammad Husni Mubarak a shekarar 2011

8- Mursi ya ci nasarar zama shugaban kasa na farko bayan lashe zaben da ya yi da kashi 52% a kan babban abokin hamayyarsa Ahmad Shafiq a shekarar 2012 , a zaben da ya zamto  mafi tsafta  a tarihin Masar.

9- Ministan tsaron da ya nada Abdulfattah al-Sisi ya yi awon gaba da shi bayan zanga-zangar da 'yan adawa da shi  musamman (secularists) su ka yi akan dole ya sauka ya shirya wani zaben cikin gaugawa su na masu zarginsa da kokarin cusa musulunci a tsarin gwamnatinsa da karawa Kansa karfin iko.

10- Sisi wanda ya samu cikakken goyon baya daga wadansu daga cikin gwamnatocin kasashen waje na larabawa da da Isra'ila ya yi amfani da damar wajen shirya juyin mulki ga shugaba Mursi a shekarar 2013

11- Magoya bayan Mursi sun cigaba da gudanar da zanga-zangar lumana ta nuna rashin amincewarsu da juyin mulkin da Sisi  ya yi wa zababben shugabansu, kuma ya ke cigaba da tsare shi, tareda wadansu dubban magoya bayansa, da kashe wasu, da tilastawa da dama daga cikinsu yin gudun hijira zuwa kasashen ketare. Sisi ya aiwatar da kisan kiyashi ga magoya bayan Mursi, wanda mafi muni shine kisan da sojoji su ka yi wa magoya bayan Mursi mutum 2000+ da su ka taru su ka yi  zaman dirshen a dandalin Rabia da ke Nasr city a cikin birnin Alkahira.

12- A shekara daya da yayi yana mulki, Mursi ya samu kauna ta ban mamaki daga al'ummar larabawa da sauran musulman duniya, wanda su ke ma kallon jagoran da zai dawo musu da kimarsu a duniya, musamman yanda ya ke nuna damuwarshi da al'ummar musulmi da yadda ya ke nuna goyon bayan shi ga mutanen Palastinu da Zirin Gaza.

13- A daya daga cikin zqman da aka yi bayan gabatar da shi a kotu, Mursi ya bayyanawa kotu cewa rayuwarshi na cikin hatsari, amma ba a dau wani mataki ba.

14- Gidan talabijin din  Masar ya sanar a ranar litinin 17/6/2019 cewa Mursi ya rasu a kotu yayin da ake masa shari'a , amma wasu na ganin wannan shiri ne kawai na boye hakikanin dalilin rasuwarshi, musamman da ya ke an hanashi magani a kurkuku.

15- Dr. Muhammad Mursi cikakken mahaddaci Alkur'ani ne mai kishin addininsa da al'ummarsa, wanda ke kokarin baiwa al'ummarsa da addinin sa kariya duk inda ya samu kansa kuma ya Samu dama.

Muhammad Mursi daya ne daga cikin miliyoyin musulmai a duniya da ke gwagwarmayar dawowa al'umma da karfinta da izzarta ta kowane bangare, kuma su ke bada jinanensu a matsayin farashin wannan aiki, kuma ba za su taba juya baya ba har sai hasken Allah ya cika.

Muna Rokon Ubangiji Allah yakai haske Kabarin shi.

Sunday, June 16, 2019

GWAMNA GANDUJE ZAI KIRKIRI MA'AIKATAR SHA'ANIN ADDINAI A KANO.Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya baiyana cewa Gwamnatin sa zata kirkiro sabuwar maaikatar shaanin addinai domin inganta al'amuran da suka shafi addini da kuma tattara hukumomin shaanin addinai na jihar a karkashin rumfa daya.

Gwamna Ganduje yayi wannan bayanin ne lokacin da aka gabatar da wata adduah ta musamman domin neman Allah Ya kara zaunar da Kano lafiya Ya kuma kare mu daga matsaloli da fitintinu da suke addabar wasu sassa na kasar nan musamman na arewacin Najeriya.

Yanzu haka dai Kano tana daya daga cikin jihohi da suke da tsaro da zaman lafiya fiye da sauran. Da fatan Allah kara zaunar da mu lafiya Ya kuma kare mu baki daya Amin.

Salihu Tanko Yakasai
16 June, 2019.

Garkuwa Da Mutane, Da Ta'addanci Na Gab Da Zuwa Karshe A Katsina Da Sauran Wurare - BuhariShugaban Kasa Muhammad Buhari ya yi wa al'ummar jihar Katsina da sauran wuraren dake da matsalar tsaro a Nijeriya albishir din cewa masu garkuwa da mutane da kuma yan ta'adda na gab da zuwa karshe a cikin kasar nan.
.
Shugaban ya ce gwamnatin tarayya na fafutuka gami da aiki tukuru wajen tabbatar da samar da kyakkyawan tsaro a Nijeriya da kuma, kai harehare ga yan ta'addan wanda kuma gwamnati ce ke cin galaba a kansu
.
Shugaban kasar ya fadi haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen bikin yaye dalibai karo na 4 a Jami'ar Gwamnatin Tarayya dake Dutsinma.
.
Shugaban da ya sami wakilcin tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar, ya kuma kalubalanci jami'o'in Nijeriya da su yi kokari wajen samar wa kawunansu da kudaden shiga, ba wai tsu tsaya jiran sai abin da gwamnatin tarayya ta basu ba kadai na kudaden tafiyar da jami'o'in.
.
Jam'iar ta yaye dalibai 430, daga cikinsu dalibai 24 sun fita da sakamakon jarabawa mafi daraja wato (First Class) sai kuma dalibai 181 suka fita da sakamakon jarabawa mafi daraja na biyu wato (Second Class Upper) a inda kuma dalibai 178 suka fita da sakamakon jarabawa mafi daraja Kashi na biyu  ( Second Class Lower) sai kuma 47 suka fita da sakamakon jarabawa mai daraja ta karshe (Third Class)

Daga, Ibrahim M Bawa

Friday, June 14, 2019

Ya Kamata Sarki Sunusi Ya Bawa Gwamnati Da Jama'ar Kano Hakuri A Bayyane - Inji Muhammad Garba
Bayan da gwamnatin jihar Kano ta samu rahoton Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa da korafe-korafen al’umma ta jihar, kan sakamakon binciken almundahana da ake zargin Masarautar Kanon da yi, karkashin jagorancin Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi na biyu, ta aika sakon neman jin bahasi ga Sarkin ta ofishin sakataren gwamnatin jihar ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni.

Inda ta bukaci Sarkin ya yi bayani kan zarge-zargen da ake masa, da zummar saurarensa bisa adalci kafin daukar wani mataki.

Idan za ku tuna, wata kungiya da aka fi sani da ‘Concerned Friends of the Kano Emirate’ ta aika wa hukumar da ke yaki da cin hanci ta jihar wasika tana zargin cewa masarautar Kano ta yi almubazzaranci da Naira biliyan 3.4 wajen siyan abubuwa daban-daban da goyon bayan Sarkin.

Hukumar ta kwashe shekara uku tana duba wannan batu; kuma sai kwanan nan ta kammala binciken, sannan ta yi ta mika sakamakon binciken ga gwamnatin jihar Kano.

Abin dubawa a nan shi ne, hukumar mai yaki da cin hancin mai zaman kanta, na aiki ne da ka’idojin dokar hukumar ta 2008 wato Kano State Public and Anti-Corruption Commission Law 2008.

Shugaban hukumar, Barrista Magaji Rimingado ya bayyana wa ‘yan jarida ranar 10 ga watan Yuni cewa, : ”Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, bai yi katsalandan a binciken ba, kuma ba zai taba yi ba.

Ya nuna cewa bisa tanadin da bangare na 8 na kundin tsarin hukumar yaki da cin hancin, wanda ya ayyana hukumar ta yi aiki ba tare da an yi mata ko wane irin kutse ba.

Don haka, duk wani wanda ya san yadda ake tafi da harkokin gwamnati ba zai soki takardar neman bahasi ga Sarki Muhammadu Sanusi da gwamnatin jihar kano ta mika masa ba.

Sai dai abin mamaki, Sarki Sanusi ya bi ka’ida ya amsa takardar ya kuma bayar da bahasin.
A bisa haka ne, na yi mamakin dalilin wata makala da aka buga a shafin karshe na jaridar Daily Trust ta Juma’a 7 ga watan Yuni mai taken “Wasika zuwa ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.”

Marubucin makalar, Jibrin Ibrahim ya bukaci Gwamna Ganduje ya janye neman bahasin, inda a ra’ayinsa, ya ce bai kamata a bayar da takardar neman bahasin ba ma tun farko!
Haka kuma, takardar neman bahasin ta soki kirkirar Masarautar Bichi da sabunta wasu masarautun na Gaya da Rano da Karaye inda ya bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na rage tasirin Sarki Sanusi.

Jibrin ya danganta wannan da abubuwan da suka biyo bayan kirkirar masarautu hudu na Auyo da Dutse da Gaya da Rano da marigayi Abubakar Rimi ya yi ranar 1 ga Afrilu na 1981.

Sai dai abin dubawa a nan shi ne tsohon Gwamna Rimi ya kirkiri wadannan masarutun ne ba tare da taimakon majalisar dokokin jihar ba, da sauran abubuwan da suka kunshi kirkirar masaurautu, wanda Abdullahi Ganduje ya bi daki-daki kafin sabunta masarautun Karaye da Gaya da Rano da kuma kirkirar Bichi.

Ya kamata Jibrin ya tuna cewa, ba Gwamna Ganduje ne ya assasa kirkirar sabbin masarautun ba. Haka kuma ba shi ya kai maganar majalisar jiha ba. Abin kawai da ya yi shi ne yin aikin da ya rataya a wuyansa na sa hannu kan doka.”

An kirkiri sabbin masarautun hudu wato- Rano da Gaya da Bichi da Karaye, Idan za a tuna, Mista Ibrahim Salisu Chamber ne ya bayar da shawarar a kirkiri sabbin masarautun wanda ya ce a ba su kima daya da Masarautar Kano. A ganinsa, kirkirar sabbin masarautun zai kawo ci-gaba a jihar.

Ya jaddada cewa hakan zai janyo mutane kusa da gwamnatin jihar, kuma a cewarsa wannan zai tabbatar da tsaro a jihar.

Bari in dan mayar da mu baya mu duba tarihi. Daliban tarihi za su san cewa masarautar Gaya ta girmi ta Kano a zahiri.

Daga farko, makeran Gaya sun fara yada zango ne a Dutsen Dala lokacin da suke neman karfe.
Zamansu a nan ya sa kananan unguwanni suka kafu jefi-jefi, kuma daga baya suka zama garin Kano. Ko da aka yi Jihadin Dan Fodio, Gaya ta ci gaba da zama masarauta mai cin gashin-kanta.

Sai dai a shekarar 1914, Turawan mulkin mallaka suka rage wa masarautar girma aka mayar da ita gunduma.

Masarautar Karaye kuwa ta dade da kafuwa, tsawon daruruwan shekaru a matsayin masarauta mai zaman kanta.

Ita ma ko bayan Jihadin ta ci gaba da cin gashin-kanta, sai dai Turawan mulkin mallaka sun rage mata karfi zuwa gunduma.

An kafa Masarautar Rano tun shekara ta 1000 A.D kalandar miladiyya.

Ita ma dai masarauta ce mai zaman kanta kuma sarakuna da yawa sun mulke ta. Kuma Rano na cikin sanannun kasashen Hausa da a tarihi ake ce wa Hausa Bakwai, wadanda Bagauda ya kafa.

Sai dai kamar sauran masarautun, Turawan mulkin mallaka sun cire Rano daga matsayin masarauta a shekarar 1908.

Ita kuwa sabuwar masarautar Bichi, an kwashe shekaru ana kokarin kafa ta. Kuma matsayinta da girmanta a jihar Kano ya sa ta cancanci a bata masarauta.

Don haka abin takaici ne, mutum kamar Jibrin Ibrahim ya zama mai kira a yi tashin hankali a Kano don shi da iyalinsa ba a nan suke da zama ba.

Kuma ba kamar yadda ya ce ba ne, don kuwa babu zaman dar-dar a Kano tun 8 ga watan Mayu don ko mazauna garin da baki ma za su shaida cewa babu tashin hankali ko wani zaman dar-dar a jihar, kamar yadda take tun hawan Gwamna Ganduje mulki ranar 29 ga watan Mayun 2015.

Ko a lokutan da makwaftan jihar ke fama da rikice-rikice, Kano ta ci gaba da zama cikin kwanciyar hankali da lumana.

Ya kamata Jibrin Ibrahim ya gane cewa an wuce lokacin daukar matasa masu zaman kashe-wando don bangar siyasa, yayin da ‘ya’yansu ke kasashen waje suna karatu.

Shirye-shiryen gwamnati na taimaka wa matasa, da manufofin samar da ilimi kyauta da gwamnatin Ganduje ta kaddamar sun samar wa matasanmu mafita daga wannan aikin wahalar.

Jibrin Ibrahim ya sani cewar wannan wani sabon babi ne, kuma dole ne Kano ta dau hanyar sauyi ita ma.”

”Bai kamata a sauya manufar kirkirar sabbin masarautu a Kano ba, zuwa cewa ana so a tarwatsa masarautar Kano da martabarta ba.
Kawai wani mataki ne na fadada al’adun Kano da kuma kai ci gaba ga mutane. Sabbin masarautun Bichi da Gaya da Rano da Karaye sun kafu kenan.

Babu abin da Gwamna Ganduje zai iya yi ya sauya hakan. Doka ce ta ce haka. Shugaba kuma dan-kasa mai bin dokoki irin Gwamna Ganduje ba zai iya maida hannun agogo baya ba kan sabbin masarautun.

Daga karshe, dole a jinjina wa ‘yan Najeriya da suka taka rawa wajen yin sulhu tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Mai martaba, Sarki Muhammadu Sanusi na biyu.

 Wannan mataki ne da Gwamna Ganduje mai son zaman lafiya zai karba hannu bibbiyu.

Sai dai fa kamata ya yi Sarki Sanusi ya bai wa Gwamna Ganduje da daukacin al’ummar Kano hakuri a bayyane, bisa kunyata masarautar Kano da yayi da kuma cakuda ta da siyasa.

Haka kuma, mutuncin Sarki Sanusi shi ne ya janye duk wata karar gwamnatin jihar Kano da aka kai da yake tallafawa.

Wannan zai nuna matsayinsa na son zaman lafiya da yafiya don ci gaban Kano da al’ummarta.

Abu mafi muhimmanci shi ne, Sarki Sanusi ya janyo sarakunan Karaye da Rano da Gaya da Bichi jikinsa, kuma ya nuna cewa a shirye yake ya hau matsayin shugaban majalisar sarakunan jihar Kano.

Haka kuma, ana sa rai zai yi amfani da kwarewarsa ya koyar da sauran sarakunan, ya kuma tabbatar da cewa sun yi dukkan mai yiwuwa wajen ciyar da jihar Kano gaba.
A lokacin da aka yi duka wannan ne, sulhun zai kayatar kuma ya zama mai riba.”

Malam Muhammad Garba shi ne tsohon Kwamishinan watsa labarai da matasa da al’adu na jihar kano.

Daga Mu'azzam Yakubu Sanka

Sulhu Tsakanin Gwamna Ganduje Da Sarki Sunusi Lamido SunusiGwamnan jahar Kano Dr,  Abdullahi Umar ganduje ya bayyana wasu sharudda da yace dole sai Sarki Sanusi ya bi Su kafin su yi sulhu.

Kadan daga Cikin Sharudan da Gwamnan jahar Kano Dr, Abdullahi Umar ganduje ya ce dole Sarkin Kano Muhammad Sunusi Lamido Sunusi zaibi Kafin Ayi Sulhu.

1 Yazama Dole Sarki ya fito ya nemi gafara a gurinsa

2 Yazama Dole Sarki yanemi Afurwar  al'ummar jahar Kano Akan Abubuwan da yayi Masu

3 Yazama dole Sarki yafara Aiki da sabbin masarautu da aka kirkiro.

Mudai Muna Rokon Ubangiji Allah ya Sulhun ta Tsakanin ganduje da Sarki Sunusi.

Dani Akayi gwagwarmayar Tabbatar Da Najeriya Kasa Daya - Inji Shugaba Kasa Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu buhari yace Dashi Akayi gwagwarmayar tabbatar da Najeriya kasa daya al’umma daya, don haka ya sadaukar da sauran abinda ya rage Mishi Na Rayuwar Duniya domin ganin Najeriya ta zauna cikin hadin kai da kuma inganta rayuwar Alummar  Najeriya.

Acikin Jawabin Shugaban Najeriya Muhammadu buhari Na Murnar Cikar Najeriya Shekara 20 da dawowar demokaradiyya Acikin Najeriya Shugaban Najeriya Muhammadu buhari ya tabbatar da cewa Dashi Akayi gwagwarmayar tabbatar da Najeriya kasa daya Alumma daya Don haka ya Sadaukar da Ragowar Rayuwar da tarage Mai Domin ganin Hadin kan Alummar Najeriya.

Muna Rokon Ubangiji Allah ya taimake ka wajan daidai ta Kasar Mu Najeriya baba buhari.

Thursday, June 13, 2019

Akwai Wasu Mutane da Basasan Najeriya ta Zauna Lafiya - Inji Shugaban Kasa BuhariShugaban Najeriya Muhammadu buhari yace Yazama Dole yama Alummar Najeriya bayanin Mutanan dake Assasa Rikice Rikice Acikin Najeriya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yace duk matsalolin Rashin tsaron da Najeriya ke fama da Shi a yanzu ya samo asali ne daga wajen shuwagabannin addinai da kuma manyan yan Siyasar Najeriya domin biyan bukatar kansu.

 Yawancin rikicin da ake fama dashi tsakanin jama’a ko rikicin addini suna samo asali ne daga wajen yan siyasa dake daukan nauyin hare haren ta,addanci ko kuma malaman addinan dake tunzura mabiyansu, ko kuma shuwagabannin kabilu dake umartar yan kabilarsu su kashe wasu Domin  Su gurgunta kasarmu Najeriya.

Dan haka shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yace ya dauki alkawarin tabbatar da Najeriya ta zauna a matsayin kasa daya al’umma daya, tsintsiya madaurinki guda,

Domin yan kasa su zauna cikin hadin kai ba tare da nuna bambamci ko wariya ga wani ba.

Shugaban Najeriya Muhammadu buhari yakara da cewa Dani aka yi gwagwarmayar tabbatar da Najeriya kasa daya al’umma daya, don haka zan sadaukar da sauran abinda ya rage min a rayuwata domin ganin Najeriya ta zauna cikin hadin kai da kuma inganta rayuwar yan Najeriya.

Muna Rokon Ubangiji Allah ya Zaunar Mana da Kasar Mu Najeriya Lafiya.

Ubangiji Allah kadaura Shugaban Najeriya Muhammadu buhari Akan Makiya Zaman Lafiyar Kasar Mu Najeriya.

Wednesday, June 12, 2019

Tsarin Ganduje Yafi Na Kowanne Gwamna A Kasar Nan - Inji Tawagar Turai Kan Dimokaradiyya


An bayyana jawaban Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, na rantsuwar kama ragamar mulki a karo na biyu, A matsayin na farko a jawaban gwamnonin Najeriya na ranar rantsuwar 29 ga watan Mayu, 2019.

Wata Tawagar sanya ido kan harkar Dimokuradiyya ta Duniya dake da matsuguni a kasar Turai, ita ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta aikewa Gwamnan Kano, da sa hannun Shugabanta Maxwell Brown Junior, takardar da aka rabawa manema Labarai dauke da sa hannun babban Sakataren watsa Labarai na Gwamna Ganduje, malam Anwar, ta bayyana jawaban Gwamnan a Matsayin, kammalalle, mai daukar hankali da basira da ya dace akan lokaci.

Takardar ta bayyana cewa, mambobin sanya ido kan Dimokuradiyya na duniya sun gamsu da kokarin Gwamnan bisa jajircewa tare da alakanta jawaban shekarar 2019 da wanda yayi a shekarar 2015.

Takardar ta zayyano wasu daga jawaban Gwamnan na shekara ta 2019 dake cewa,  "Zaku iya tunawa a lokacin rantsar dani a Matsayin Gwamnan jahar mu abar kauna a ranar 29 ga watan Mayu, 2015, na zaiyyana alkibilar wannan gwamnati a jawabina na farko, cewa zan karasa ayyukan gwamnati dana gada tare ingantasu da kuma kirkiro da sabbin ayyyuka da shirye shiryen inganta rayuwar Jama'ar jahar mu."

Da wannan, takardar ta bayyana Gwamnan a Matsayin Shugaba da yake da zummar hada kudirin Gwamnatin sa ta baya da ta yanzu. "hakan kuma zai bashi dukkan damar samun gobe mai kyau" cewar takardar.

Takardar ta Kara da cewa mambobin sanya idon, sun nuna farin cikin su kan bayanan Ganduje, daki daki cewa,  gwamnati da dukkan Al'ummar Kano ke da hakkin mayar da jahar Tauraruwar rayuwa.

"Kada mu manta cewa an kammala zabuka, yanzu abun daya rage mana shine yin aikin da kowa zai mora. Zan sanya kowa cikin gwamnatina. Batare da La'akari da banbancin siyasa ba, zamu sanya Kano tayi muku aiki," alkawarin Ganduje kenan.

Abun da yaja hankalin yabawa jawaban Ganduje shine, kudirin daya zaiyyana zai gudanar cikin shekaru 4 masu zuwa na wa'adinsa na biyu.

Wadanda suka hada da burin martaba al'ummarsa. Sai ya Kara da cewa zai jajirce wajen gina jahar na karfafa fannin lafiya da ilimi,  garambawul wa sashen noma da kasuwancin noma.

Sai kuma kayata biranen Kano, samar da karin ayyukan yi ga Jama'a, tabbatar da tsaro da zaman lafiya don habaka tattalin arziki da ciyar da jahar gaba.

Tawagar sanya idon kan Dimokradiyar dake kasar Turai, ta kara jinjinawa Gwamnan na tsarinsa don tunkarar sashe bayan sashe da zummar nausa jahar ga tudun natsira, Kamar yadda ya fara a wa'adin mulkinsa na farko.

A sashen ilimi kan burin Ganduje, ya nuna karara, gun da yake cewa, kuma takardar ta zayyana "A farkon jawaban samun nasarata, gwamnati zata bayar da ilimin firamare dana gaba dashi kyauta kuma dole ga 'yan asalin jahar Kano, Sannan a bangaren ilimin manyan makarantu kuwa zai kasance cikin rahusa.

A game da ilimin Kawai,  daga yau ya zama kyauta ga nakasassu a dukkan matakai hadi da manyan makarantu. Dokokin da zasu tabbatar da haka daga gwamnati za a fitar dasu nan bada jimawa ba."

"Wadannan bayanai na baya dana yanzu kan kokarin samar da rayuwa mai inganci, tsarin Dr Abdullahi Umar Ganduje kan ilimi zai kasance na farko da yafi kowanne tsari a fadin Najeriya a wannan karnin 2019 zuwa 2023. Haka zalika sauran bangarorin, nuna kulawarsa ta kwarai ta sanya mana kaunarsa gaba dayanmu," Kamar yadda takardar ta tabbatar.

Haka zalika a sashen lafiya Ganduje yace zaiyi yaki da cutar Sankara data addabi yawancin mata a jahar,  Inda yace ya bayar da kwangilar gina cibiyar kula da masu cutar Sankara a Asibitin kwararru na Muhammadu Buhari kan tsabar kudi naira biliyan biyu da digo hudu, wadda cibiyar zata kasance ta farkon tarihin Asibitocin gwamnati a fadin Najeriya.

Gwamna Ganduje ya kuma bada tabbacin inganta fannin noma fiye da kowanne lokaci a fadin jahar Kano.

Sai yace gwamnati zata sanya naira biliyan daya da digo takwas a fannin noman adduga cikin shekaru hudu a Kananan Hukumomi Talatin da biyu da aka zaba a jahar.

Takardar da tawagar ta aikewa Gwamna Ganduje, ta karkare da zayyana jawabinsa kan harkokin tsaro "Dole a magance barazanar tsaro da ake fuskanta a jahar nan. Domin sake maido da martabar jahar baki daya, Gwamnatin mu ta fara gina da kuma sanya kayan aiki a cibiyar samar da tsaro a Bompai, cikin hedikwatar Rundunar 'yan sanda ta jahar Kano.

Tare da hadin gwiwar jami'an tsaro da yunkurin Al'umma za a kawo Karshen matsalar tsaro a makwabtan jahar.

Gwamnati na kokarin kashe bikin hawan Daba,  Jagaliya da zaman majalisa da Matasa keyi ta hanyar wayar da kansu da kuma samar musu da abunyi.
Daga Uzairu Dauda Bauchi

Cikakken jawabin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari A bikin Ranar DamokaradiyyaShugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabinsa a wajen taron bikin ranar Damokradiyya wanda ke gudana yau a Abuja 12 ga watan Yuni. 2019

Buhari ya bayyana cewa babban burinsa a matsayinsa na Shugaban kasar Najeriya shine ya ga ya hada kan Alummar Najeriya guri daya.

Shugaban Najeriya Muhammadu buhari ya kuma yi tsokaci akan lamarin tsaro wanda ke ci ma kasar kwarya a tuwa inda ya bayyana cewa lamarin baya tsorata su illa ma kara masu kwarin gwiwa da hakan ke yi.

Ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci aikin duk wanda ke so ya tsokani ko yi wa al'adun kasar ba'a ba ko kuma ya kawo wa tsaron kasa cikas.

"Bambancin 2015 da 2019 dangane da harkar tsaro shi ne cewa a wannan karo muna yin aiki tare da jam'ian tsaro masu yawa da bayanan sirri da kuma kayan aiki.

"Ba mu tsorata da kalubalen da ke gabanmu ba sai dai ma sun kara mana kwarin gwiwa ne.

"Shirye-shiryenmu na habbaka rayuwar 'yan kasa (N-power da ciyar da 'yan makaranta) abin koyi ga sauran kasashen duniya.

"A matsayina na shugaban komitin farfado da tafkin Chadi zan jagoranci zama na musamman don kawo karshen matsalolin tsaro a yankin.

"Ina mika godiya ta musamman ga 'yan kasuwa wadanda suka gina wuraren kasuwanci kamar layukan wayar hannu da kuma sauran wurare wadanda suka bai wa matasanmu aikin yi.

"Wannan gwamnati ba za ta yadda da aikin duk wanda yake so ya tsokani ko yi wa al'adunmu ba'a ba ko kuma ya kawo wa tsaron kasa cikas.

"Daga yau na mayar da sunan babban filin wasa na kasa da ke Abuja Moshood Abiola.

Muna Rokon Ubangiji Allah yama Shugaban Najeriya Muhammadu buhari jagora Acikin Mulkin shi.

Monday, June 10, 2019

Kotu Tayi Watsi Da Karar Kalubalantar Nasarar Buhari A Zaben 2019


Kotun da ke sauraren karan zaben shugaban kasa ta yi watsi da karar da gamayyar jam’iyyu na C4C ta shigar gaban ta tana kalubalantar nasarar da Buhari yayi a zaben 2019.

Lauyoyin dake kare Buhari da jam’iyyar APC, Wale Olanipekun da Lateef Fagbemi sun bayyana wa kotu cewa basu ga takardar janye karar da C4C suka ce sun mika wa kotu ba sannan su kan su ba a mika musu ba.

A dalilin haka kuwa suna kira ga kotu da tayi watsi da wannan kara.

Sai dai kuma kafin kotu ta jefar da wannan kara a kwandon shara, lauyan wadanda suka shigar da kara ya bayyana cewa a ranar Litinin ne suka mika takardar janye karar sai dai kuma ba su samu daman iya samu ya kaiga lauyoyin wadanda suke kara ba.

Alkalan wannan kotu su biyar cikin jagorancin mai shari’a Mohammaed Garba yayi watsi da wannan kara.

Saturday, June 8, 2019

Rundunar Yan Sandan Jahar Kano ta Haramta Gudanar da Tarurruka a Fadin Jihar.Rundunar Yen sandan jahar Kano ta bada sanarwar haramta duk wani taro na zanga-zanga na lumana, ko goyon baya, ko fadakarwa akan kowani fanni na rayuwa har sai baba ta gani.

Wata sanarwa da Jami'in Hulda da jamaa na rundunar DSP Abdullahi Haruna ya Sanya wa hannu kuma aka rabawa manema labarai, yace wannan matakin ya zamo dole ganin yadda wasu ke son amfani da kuma rura wutar rashin fahimta da aka samu tsakanin masarauta  da gwamnati wajen kawo hargitisi da rashin zaman lafiya a jahar.

Yace hakkin rundunar ce kare dukiya, martaba da rayukan al'umma, don haka yake gargadin kungiyoyi, na gwamnati, ko na saka kai ko masu rajin kishin alumna da su guji gudanar da duk wani taro na zanga zanga a ciki da wajen jahar, Wanda kin bin wannan doka ka iya kawo daukar mataki tsatsaura akan duk Wanda aka samu da hannu a ciki.

Daga karshe sanarwar tace an janye duk wata dama da aka baiwa kungiyoyi a baya na gudanar da tattaki a fadin jahar har sai sanda rundunar ta janye wannan doka.

Friday, June 7, 2019

Shugaban Kasa Buhari Ya Sulhunta Gwamna Ganduje Da Sarki Sunusi IIAyau Adalin Shugaban Najeriya Muhammadu buhari yakawo Karshen Rikicin dake tsakanin gwamnan jahar Kano Dr. Abdullahi Umar ganduje da Sarkin Kano Muhammad Sunusi Lamido Sunusi.

Shugaban Najeriya Muhammadu buhari ya Sulhunta Gwamnan jahar Kano Dr. Abdullahi Umar ganduje da Sarkin Kano Muhammad Sunusi Lamido Sunusi Wanda Siyasa ta hada

Majiyar Mu ta Sanar Mana cewa yanzu haka gwamnan jahar Kano Dr. Abdullahi Umar ganduje yafasa tsige Sarkin Kano Muhammad Sunusi Lamido Sunusi daga Masarautar Kano

Amma Kukasance damu domin jin Cikakken Labarin

Muna Rokon Ubangiji Allah ya tabbatar da wannan Sulhun. el

Buhari ya amince zai shiga tsakanin Ganduje da Sarkin Kano Sanusi
Bayan abubuwa sun rinchabe rahotanni suna bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya amince ya tsoma baki a rikicin da ke faruwa tsakanin Gwamna Ganduje da Sarkin Kano Sanusi.

Majiyar Manuniya ta ruwaito Shugaba Buhari ya gayyaci Ganduje da Sarkin Kano zuwa Abuja domin dinke barakar dake tsakaninsu.

Majiyar tace Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ne ya fara yiwa shugaban kasar bayani akan batutuwan tsaro da suka addabi yankin a inda Mista Buhari ya umurci shugaban tsaron farin kaya DSS ya hada masa Gwamnonin yankin sannan kuma ya gayyato masa sarkin Kano da sakataren masarautar Kano.

Thursday, June 6, 2019

An Bawa Sarki Sunusi Awa 24 Ya Amsa Tuhume-Tuhumen Da Ake Masa
Tataburza dake tsakanin gwamnatin jahar Kano da fadar masarautar Kano ta kara zafafa, inda a yanzu Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da tsare tsaren tsige mai martaba Sarki Muhammadu Sunusi II daga kujerar sarauta.


Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan ya aika ma Sarki wata takarda dake kunshe da dukkanin tuhume tuhumen da gwamnati ke masa dangane da almubazzarancin kudade, inda ya bukaci ya bashi amsa cikin sa’o’I 24.

 Idan za’a tuna a ranar Litinin data gabata ne hukumar yaki da rashawa da sauraron koke koken jama’a ta jahar Kano ta kama Sarki Sunusi da laifin barnatar da kudi naira biliyan uku da miliyan dari hudu, har ma ta baiwa gwamna shawarar ya dakatar da Sarkin.

Shugaban ma’aikatan fadar Sarkin Kano, Munir Sunusi ya tabbatar da samun takardar da gwamnan Kano ya aiko ma Sarki ta hannun sakataren gwamnati, inda yace a ranar Alhamis takardar ta iso fada, kuma masarauta tana yin nazari game da takardar. Bugu da kari rahotanni sun bayyana cewa a tuni gwamnatin ta kammala shirya kwamitin da za tayi nazarin duk amsar da Sarkin Kano ya baiwa gwamnati, inda ake sa ran kwamitin ne zata yanke hukuncin daya dace da Sarkin.

Sai dai majiyoyi daga fadar gwamnatin jahar Kano sun tabbatar da cewar duk ta kare Gwamna Ganduje zai yi awon gaba da rawanin Sarki Muhammadu Sunusi II ne, musamman tun bayan samun rahoton binciken hukumar yaki da rashawa ta jahar Kano a karkashin jagorancin Muhyi Magaji Rimin Gado.

Idan za’a tuna hukumar ta koka kan yadda wasu na hannun daman Sarkin guda hudu suka ki amsa gayyatar da tayi musu yayin da take gudanar da bincike akan zargin almubazzarancin, inda hukumar ta zargi Sarkin da hana mutanen nasa gurfana gaban hukumar. A hannu guda kuma, Walin Kano ya musanta dukkanin tuhume tuhumen da ake yi ma Sarkin Kano da masarautar gabaki daya, inda yace masarautar Kano bata gaji naira biliyan 3.4 ba balle ma har ta almubazzarantar dasu. Read more:

TY Danjuma, Zamani Lekwot Da Wasu Manyan Kiristocin Najeriya Sun Kai Karar Buhari Turai
Tsohon ministan tsaron Najeriya, Laftanar Janar TY Danjuma mai Ritaya da tsohon gwamna a jihar Ribas a lokacin mulkin soja, Janar Zamani Lekwot mai Ritaya da kuma Cif Solomon Asemota mai lambar kwarewa ta (SAN), sun gayawa majlaisar dokokin kasar UK cewar shugaban kasar Najeriya Buhari na neman kawo Jihadi a Najeriya domin ya musuluntar da Kiristocin Najeriya ne, ba wai yana kokarin kawo karshen ta’addancin Boko Haram da kuma rikicin Fulani makiyaya da manoma a Najeriya ba.

Tsofaffin Janar-Janar din sojan guda uku, wato Janar T.Y. Danjuma, Janar. Joshua Dogonyaro, Janar Zamani Lekwot, da kuma Ambasada Moses Ihonde sai kuma Solomon Asemota na wannan furuci ne karkashin kungiyar Tsofaffi kuma Kiristocin Najeriya (NCEF), wanda kuma cikin kungiyar akwai Janar Joshua Dogonyaro mai Ritaya, da kuma Jostis Kalajine Anigbogu, da kuma Mathew Owojaiye, da kuma Dakta Kate Okpaleke sai Moses Ihonde dukkan su a matsayin mambobin kungiyar.

Kungiyar Tsofaffin Kiristocin, wanda suka zargi Lord Lugard da shuka rikice-rikicen addinau dana bangaranci da rarrabuwar kai tsakanin Arewaci da Kudancin Najeriya.

Sun kuma yi kira da babbar murya kan a karfafa Dimokuradiyya tare da nuna kin amincewar su da Shari’ar musulunci a Najeriya, a cikin wata takarda da suka rubuta ranar 3 ga watan Yuni kuma suka aike da ita ga kungiyar gamayyar jam’iyyu na majalisar dokokin kasar UK (APPG) domin bawa kowa damar bautawa addinin da yayi imani da shi a Najeriya ba tare da neman musuluntar da Najeriya da Buhari ke yi ba.

Wednesday, June 5, 2019

Sarki Sanusi II Ya Janye Hawan Dorayi Ya Kira Taron Addu'ar Shekara 5 Da Rasuwar Ado Bayero
 *Akwai Iyuwar Ganduje Zai Dakatar Da Shi A Gobe

Kana kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya janye hawan Dorayi an maye gurbinsa da yi wa tsohon Sarkin Kano Marigayi Ado Bayero addu'ar cika shekaru biyar da rasuwa. Tare da addu'ar cikar Sarki Sanusi II shekaru biyar a mulki.

Kazalika Dan jarida Nasiru Salisu Zango ya rubuta a shafinsa na facebook cewa, akwai iyuwar fitar da wata sanarwa a goben dangane da Sarkin.

Lamarin da ya sa wasu rahotanni dake yawo a gari ke hasashen cewa akwai iyuwar a goben Ganduje zai iya bayar da sanarwar dakatar da Sarki Muhammadu Sanusi II.

Gwamatin Jahar Kano Ta Soke Hawan Nasarawa
Gwamnatin jihar Kano karkashi jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje ta soke hawan Nassarawa wanda bisa ga al'ada sarkin Kano kan kaiwa gwamna ziyara a gidan gwamnati.

Wannan dai na kunshe ne cikin wata takarda da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin Kano.
Subhanallahi: Gobara Ta Lashe Kayan Tallafin 'Yan Gudun Hijira A Barno
Da jijjifin safiyar yau Laraba ne gobara ta lashe kayyakin tallafin masu gudun hijira na milyoyin nairori, a wani babban rumbun ajiyar kayan agaji da ke kan titin Baga, cikin Maiduguri.

Rumbun ajiyar dai mallakar Kwamitin Rabon Kayan Agaji na Shugaban Kasa ne.

An ruwaito cewa wutar ta kama da misalin karfe 6 na fiyar yau Laraba, kuma ta cinye kimanin katifu 400, ta lashe wata mota da kuma kayyayaki masu tarin tarin yawa.

Jami’an Sintiri na NSCDC, ‘yan sanda, kwana-kwana da kuma makwabta sun garzaya wajen kai dauki domin taimakawa a kashe wutar.

Kakakin Hulda da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Barno, Ambursa Pindar, ya tabatar da tashin gobarar, tare da cewa jami’an su sun kai daukin gaggawa.

Ya ce gobarar ba ta ci rayuka ko daya ba, amma ta ci kayyaki da wata mota kirar Jeep da ta dade ajiye a wurin.

Har zuwa yanzu dai ba ta tantance musabbabin tashin gobarar ba, wadda ta ci kayayyakin.

Sannan kuma ba a kai ga tantance ainihin asarar kaya da kayan abincin da suka salwanta ba. Amma dai an kiyasta sun kai na milyoyin nairori, kamar yadda aka tabbatar.

Binciki: An Gano Hanya Mafi Sauki Ta Rage 'Kiba Ba Tare Da Ansha Magani Ba
Ko kun san cewa kuka da hawaye wajen karfe 7 zuwa 10 na dare na rage kiba? - Bincike

Masana sun  gano wata hanya mafi sauki da mutum zai bi idon har yana son rage yawan kiba maimakon shan magunguna ko abubuwan da za su zame masa illa.

Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa kuka mai tsuma zuciya na iya taimaka wa mutum wajen rage kiba. Binciken ya nuna cewa hakan na kasancewa ne saboda akwai alaka tsakanin kuka da tantanin halitta da ke taimakawa kan hakan.

Wadanan tantanin halitta zai taimaka wajen rage kiba da zaran mutun sanya abun tausayi a zuciyarsa sannan ya fara kuka.

Baya ga haka wani masanin fannin gwaje-gwaje Willaim Frey ya gano cewa wahalar da ke tattare da hawaye na iya cire duk wasu abubuwa da ke dauke da guba daga jikin dan Adam. Don haka a lokacin bacin raid a gajiya, jiki kan fitar da wadannan guba ta hanyar kuka.

Ka Nada Ni Mai Bada Shawara A Kan Man Fetur - Sakon Guru Maharaja Ga Buhari.
Babban matsafi nan kuma Shugaban gidauniyar One Love Family, Sat Guru Maharaj ji, a ranar Talata, 4 ga watan Yuni yayi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya nada shi a matsayin mai bashi shawara na tsarkin jiki.
.
Ya ce akwai bukatar hakan saboda sauran kungiyoyin addini da shuabanninsu sun gaza.
.
Maharaji ya gabatar da wannan bukata ne a lokacin wani taron manema labarai.

An gudanar da taron ne a kauyen Maharaj ji da ke hanyar babban tikin Lagos/Ibadan.
Ya ce daga cikin abubuwan da ya ke sanya rai shi ne Shugaban kasar ya nada sa a matsayin wanda zai jagoranci ma’aikatun ruwa, noma, mai da gas a mulkin Buhari na biyu.
.

Tuesday, June 4, 2019

Matasan Kano 120,000 Za Su Samu Ayyuka Na Musamman A Gwamnatin Buhari
Akalla matasa marasa aiki yi guda dubu dari da ashirin, 120,000, da suka fito daga jahar Kano ne zasu tagomashin aikin yi daga gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Majiyarmu ta ruwaito mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne ya bayyana haka a ranar Litinin, 3 ga watan Yuni yayin wata ziyara daya kai jahar Kano, inda yace gwamnatin zata kara daukan matasan Kano 120,000 aiki a karkashin tsarin N-Power.

Osinbajo ya bayyana haka ne ta bakin hadimin shugaban kasa, Isma’eel Ahmad, wanda ya wakilci Osinbajo a taron gudanar da addu’o’I na musamman da wasu mutane da suka ci moriyar tsarin tallafin gwamnatin Buhari suka shirya.

“A cikin shekaru hudu masu zuwa zamu sake daukan matasan Kano 120,000 a karkashin tsarin aikin N-Power, haka zalika zamu kara adadin jama’an dake cin gajiyar tallafin N5000 a kowanne wata daga kananan hukumomi 15 zuwa kananan hukumomi 44.

“Hakanan shima tsarin bashin TraderMoni, zamu baiwa yan kasuwan Kano miliyan biyu bashi mai saukin ruwan a wannan shekarar 2019.” Inji shi.

Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tsalin bada aikin N-Power da na tallafin Buhari sun bayyana farin cikinsu da dacewa da wannan tagomashi, sa’annan sun yi addu’ar Allah Ya kara ma Buhari lafiya, hikima da tsawon kwana mai albarka don cigaba da aikin alherin da yake yi.

A yanzu haka dai akwai matasa fiye da 18,000 dake cin gajiyar tsarin N-Power a jahar Kano, mutane 51,000 dake samun tallafin naira dubu biyar biyar a duk wata a jahar, ga kuma tsarin ciyar da daliban firamari da kuma bashin Trader Moni.

Sakon Barka Da Sallah Daga Mataimakin Gwamnan Kano Dr. Nasiru Yusif Gawuna.
Mai girma Mataimakin Gwamna Dr. nasiru Yusif Gawuna. na taya mai girma Shugaban Kasar Nijeriya Gen. muhammad Buhari. da Maigirma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje da sauran mukarraban gwamnatin jihar Kano baki daya, barka da sallah tare da fatan an sha ruwa lafiya.

Dadin dadawa mataimakin Gwamna yana yi wa daukacin ilahirin Al'ummar musulman Kano, dana duniya gaba daya barka da sallah da rokon Allah Ya karbi ibadunmu da muka gabatar a cikin watan Ramadan din da ya kammalu a jiya Litinin

Takabbalallah Minna Wa Minkum.

Sunday, June 2, 2019

Gwamnatin Ganduje Za Ta Samar Da Hukumar Kula Da Lamuran Addini.
Gwamnatin Jihar Kano ta kafa Kwamiti na musamman don samarda Hukumar kula da lamuran Addini(Ministry for religious affairs)  a Jihar Kano.

Dr. Muhammad Tahar Baba impossible shine zai Jagoranci Kwamitin, Mal. Muhammad Albakary Mikail, Sheik Abdallah Pakistan da sauran Mallaman Kano na kowanne Bangare suna cikin Mambobin Kwamitin.

Babu shakka wannan cigaba ne abin Alfahari ga masu Kishin Muslinci.

Allah yashiga cikin wannan lamari.

Harin Ta'addanci: Aisha Buhari Ta Yi Kira Da A Kawo Karshen Ta'addanci A Kasar Nan
Uwar gidan shugaban kasa Aisha Buhari ta koka game da yawan hare-haren da ake kaiwa cikin jihar Katsina da sauran sassan Nijeriya baki daya.
.
Uwar gidan ta bayyana cewa har in dai ba a dauki matakin gaggawa ba game da lamarin hakika babu wanda zai sha game da harin yan ta'addan.
.
"A lokacin da Sakataren gwamnatin jihar Katsina ya koka game da maganar tsaro, na tura sakon zuwa sassa daban-daban na rundunar tsaron Nijeriya, na kuma gaya masu, ko dai su je su kai dauki, ko kuma su yi sake a kashe mu gaba daya" inji Aisha Buhari
.
" Ya zama wajibi mutane su yi magana a kan abin da ake aikatawa wanda ba dai-dai ne ba, komin dacinsa dole a fito a yi magana a kansa" inji ta
.
 Bayanan hakan sun biyo bayan lokacin da ta kai ziyarar gani da ido a sansanonin yan gudun hijira dake Katsina wadanda yan ta'adda suka tarwatsa a garuruwansu

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Katsina ta bayyana cewa akwai yan gudun hijira har  1,707 a karamar hukumar Katsina; sai karamar hukumar Batsari 18,544, a Kurfi suna da 135,  Faskari, kuma na da 1,440, a  Kankara akwai 2,426,  Danmusa, na da 513, sai Jibia – 616, sai kuma karamar hukumar Safana, na sa  607
.
Uwar gidan shugaban kasar kuma ta ce gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan 500 domin kudaden bayar da tallafi, a don haka hukumar ta karkato jihar Katsina da bayar da tallafin domin akwai mabukatan da suke bukatar tallafin sosai domin rage radadin halin da suke ciki

Saturday, June 1, 2019

Hotuna: Hajiya Aisha Buhari Ta Tallafawa 'Yan Gudun Hijira Da Kayan Masarufi
Ayau Uwar Gidan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta farantama Yan gudun hijira Rai Acikin jahar Katsina.

Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta tallafama yan gudun hijira da kayan Masarufi Wanda yan Ta,adda Suka tarwatsa Masu garuruwan Su.

Uwar Gidan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Hajiya Aisha Muhammadu Buhari taje Sansanin yan gudun hijira dake jahar Katsina inda ta Raba Masu kayan Masarufi Acikin wajan.

Muna Rokon Ubangiji Allah yasaka Mata da Alkairin duniya da Lahira.

Popular Posts