Friday, May 24, 2019

Zamfara: INEC Ta Bayyana Matakin Da Za Ta Dauka Akan Hukuncin Kotun Koli
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta yi magana kan abin da ya dace ta yi bayan da Kotun Koli ta soke nasarar da jam’iyyar APC ta yi a zabukan Jihar Zamfara.

A na ta jawabin, INEC ta bayyana cewa ta yi taron gaggawa domin duba hukuncin da kotun ta zartas.

Daga nan sai Hukumar Zaben Mai Zaman Kanta ta Kasa ta ce za ta dauki mataki na karshe a ranar Litinin mai zuwa.

“Biyo bayan hukuncin da Kotun Koli ta yanke, inda ta soke zaben Gwamna, na Majalisar Dattawa, na Tarayya da na Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, INEC ta gudanar da taron gaggawa domin tattauna lamarin.

“Kotun Koli ta ce ta watsar da dukkan kuri’un da aka jefa wa jam’iyyar APC a Zamfara, don haka dan takarar da ya zo na biyu, kuma ya samu yawan kuri’un da ake bukata, shine zai zama wanda ya yi nasara.

Don haka INEC za ta sake zama ranar Asabar, 25 Ga Mayu ta sake tattauna batun, sannan kuma a ranar 27 Ga Mayu, wato Litinin, INEC za ta yi wa jama’a jawabi.”

Kamar yadda hukumar ta fitar da bayani a yau Juma’a.

Idan ba a manta ba, tun da farko INEC ta haramta wa jam’iyyar APC shiga zabe a jihar Zamfara, a bisa dalilin cewa ba a yi zaben fidda-gwani a jihar a karkashin ita jam’iyyar APC din ba.

No comments:

Post a Comment

Popular Posts