Saturday, May 11, 2019

Sharri Akai Wa Sheikh Dr. Isah Fantami. Be Zagi Kwankwaso Ba - Datti Assalafy
"Wata jaridar yanar gizo irin ta mutanen Kwankwasiyya a jiya ta wallafa wani labari kamar haka:
!
KWANKWASO JAHILI NE KOH SHARAR MASALLACI BAI CHANCHANTA YA SAMU BA BARE SHUGABAN KASA - Dr Isah Ali Pantami

Shahararren Malamin Addinin Muslinci A Nigeria sheikh Dr Isah Ali Pantami Ya Bayyana Cewa Kwankwaso Jahili Ne Wanda Baisan Me Yakeyi Ba,

Pantamin Ya bayyana hakanne Yayin Gabatar Da Tafsirin Watan Ramadana A Abuja ,Inda yace Shekaru Bakwai Baya Naji Da Kunne na Kwankwaso Yana Kalubalantar Me Yasa Allah Ya Halicci Sauro, Yanzu Irin Wadannan Mutane Sune zamu Bari su shugabanci Al'umma,

Sai Dai Tun Shekaru da yawa baya Engr Dr Rabiu musa kwankwaso yayi karin hasken akan wannan maganar inda Ya bayyana cewa sam Sam ba haka yake nufi ba mutane ne suka juya masa zancensa saboda siyasa

Shin Ko Menene Hikimar Pantami Akan Taso Da wannan Magana Da Ta Wuce Tun Tsawon Shekaru Bakwai ? Daga Jaridar Nageriyarmu A Yau"

Wannan shine abinda jaridar ta wallafa, ta kuma jingina ga Malaminmu na Sunnah Ash-sheikh Dr Isa Ali Pantami, mutum sama da dubu uku ne sukayi comment, duk zagin duniya da tsinuwa sai da wasu mutanen Kwankwasiyyah suka zage Malam Isah Ali tatas, sun zageshi da mafi munin kalmomin zagi da tsinuwa, ko maguzawa ba zasu yi irin wannan zagi ga Malami ba

To amma abinda ya tabbata gaskiya shine; wato a ranar hudu ga wannan wata na Ramadan  Malam ya gabatar da tafsiri, a al'ada yakan fara amsa tambayoyi kafin sai ya ci gaba da fassara, Malam ya amsa tambaya ce akan musulmi barawo ko 'dan fashi da aka kashe ko ya halatta musulmai su sallaceshi?

Malam yayi gamsasshen bayani har ya tabo tsohuwar al'ada da akeyi a shekarun baya kafin a fahimci addini, malam yace anyi lokacin da idan ka shiga masallaci jam'i ka tsaya a bayan Liman fitar da kai ake, domin akwai wadanda aka ware sune kadai suke tsayawa a bayan Liman, Malam yace amma yanzu duk wannan abin ya zama tarihi

Malam ya kara da cewa a shekarun bayane aka samu wasu manyan 'yan siyasa musulmai wadanda basu fahimci addini ba sai su kira sunan Allah suce "Sallallahu alaihi wa sallam", sai su kira sunan Annabi Muhammad suce "Subhanahu wa ta'ala", a cikinsu ne aka samu masu cewa cikin Annabawan Allah akwai Annabi Ummaru, kuma aka samu wani 'dan siyasa da yace me yasa Allah Ya halicci sauro? to wai irin wadannan 'yan siyasar ne da suka jahilci addini suke wakiltar Musulmai..

Har Malam ya kammala tafsirin gaba daya a wannan ranar Wallahi Billahi bai ambaci sunan wani 'dan siyasa ba ko guda daya, amma sai akace wai ya ambaci sunan kwankwaso, har yanzu akwai karatun yana nan a cikin whatsapp  group dina guda 13 da na saka, Malam bai ambaci sunan kowa ba, kuma babu shakka alhakkin zagi da tsinuwa da 'yan Kwankwasiyyah suka yiwa Malam zai kare a kansu ne da kuma wanda ya wallafa rubutun na karya da sharri

Wallahi ban taba ganin wasu mutane da aka renesu da son yin zagi da ashar da tsinuwa kamar wasu daga cikin magoya bayan Kwankwaso ba, duk wanda ya ambaci gwaninsu ko da bai zageshi ba to su kam zasu mayar da martani da mummunan ashariya da tsinuwa, wannan itace tarbiyyan da aka basu?, ko da yake ance kowa yana kyauta da abinda yake dashi ne

Allah Ya sauwake

No comments:

Post a Comment

Popular Posts