Thursday, May 30, 2019

Ayyuka 20 Da Shugaba Buhari Zai Yi Wa 'Yan Nijeriya Bayan An Rantsar Shi A Karo Na Biyu
Jiya ne ranar da aka rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari, yanzu haka dai har filin wasa na Eagle Square ya fara canja kala, yayin da za a rantsar da shugaban kasar a karo na biyu. Ana sa ran abubuwa da dama daga gurin shugaban kasar a wannan shekaru hudun da zai yi, kamar yadda ya ce, "wannan shi ne karo na biyar kuma karo na karshe da zai tsaya takara a Nijeriya."

Ga wasu daga cikin alkawuran da shugaban kasar yayi a lokacin yakin neman zabe:

1. Alkawarin kai Najeriya tudun mun tsira wato (NEXT LEVEL).

2. Samawa matasa miliyan 1 da suka kammala digiri aikin N-Power.

3. Koyawa 'yan Nijeriya miliyan 10 sana'ar hannu.

4. Bai wa manoma miliyan 1 iri da kayan aikin gona.

5. Kirkirar ayyuka miliyan daya da rabi a bangaren noma da kiwo.

6. Kirkirar ayyuka miliyan 5 a bangaren noma.

7. Samar da dala miliyan 500 don samar da ayyuka 500,000 ga 'yan Najeriya

8. Koyawa matasa 200,000 kasuwanci a fannin fasaha.

9. Gina wuraren shakatawa guda 6 a yankunwa 6 na fadin kasar nan.

10. Kara shirin ciyar da yara dalibai daga miliyan 9 zuwa miliyan 15.

11. Shirin ciyarwa don samar da karin ayyuka 300,000 ga masu karamin jari da manoma.

12. Kammala hanyar jirgin kasa ta Lagos zuwa Calabar, kammala aikin 2nd Niger Bridge, kammala hanyar Abuja zuwa Kano.

3. Kammala aikin titin jirgin kasa na Ibadan zuwa Kano, da kuma Port Harcourt zuwa Maiduguri.

 14. Kara karfin kafafe sadarwa zuwa kilomita 120,000 a fadin Najeriya.

 15. Kara karfin wutar lantarki zuwa 1000MW kowacce shekara.

16. Kara yawan raba wutar lantarki zuwa 7000MW, kirkirar jami'o'i guda 9, kasuwanni 300.

17. Aiwatar da shirin samar da wutar lantarki a yankunan karkara na dala miliyan 550.

18. Bayar da bashin miliyan 1 ga masu sana'ar hannu.

 19. Kara kudin TraderMoni daga miliyan 2 zuwa miliyan 10.

 20. Gina shaguna 109 ga hukumomin (CAC, NAFDAC, SON da sauran su).

Daga Salmanu Shehu Bagida

Zamu Bawa Nakasassu Ilimi Kyauta - Inji Gwamna Ganduje

2


Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya shelanta bayar da ilimi Kyauta ga nakasassun da ke cikin Jihar a dukkannin matakai.

Da yake jawabi a bikin karban mulkin Jihar a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu, Ganduje ya yi alkawarin bayar da ilimi kyauta ga dukkanin yaran Jihar da suka isa shiga makaranta.

Ganduje ya bayyana cewa, za kuma a yi rangwame sosai ga ‘yan asalin Jihar da suke cikin manyan makarantun Jihar, ya kara da cewa, gwamnatin na shi za ta yi amfani da nasarorin da ta samu a zangonta na farko a sassan ilimi, noma, manyan ayyuka da kuma sashen lafiya.

Ya ce, zangon mulkin na shi na biyu zai samar da wata sabuwar hukuma mai suna, Kano State Small Town Water Supply Agency, wacce za ta kula da samar da ruwa ga al’ummomin da suke a karkara.

Gwamnan kuma ya yi alkawarin habaka noma a Jihar, yana mai karfafa daukaka matsayin kananan manoma.

Ganduje ya sabunta aniyarsa ta yakar cin hanci da rashawa, ya kara da cewa, zangon mulkin na shi na biyu zai tabbatar da farfado da hukumar hana cin hanci da karbar rashawa ta Jihar ta yanda za ta yi aikinta sosai.

Ya kuma yi alkawarin gudanar da gwamnatin da za ta kunshi kowa da kowa ba tare da nuna bambancin jam’iyya ba, ya yi nuni da cewa, zamanin siyasa kuma ai ya wuce.

Me za Ku ce?

Wednesday, May 29, 2019

Dalilin Da Ya Sa Buhari Bai Gabatar Da Jawabin Komai Ba A Wajen Rantsar Da Shi

A yau ne aka rantsar da shugaban kasa Muhammad Buhari a matsayin shugaban kasar Nijeriya karo na biyu, da zai gudanar da shugabancin Nijeriya daga 2019 zuwa 2019

Sai dai a wajen rantsar da shugaban kasar na yau, shugaban kasar bai yi jawabin komai ga yan Nijeriya ba kamar yadda aka saba, wanda hakan ya jawo cece-kuce ga wasu yan Nijeriyar da suke ganin abin ya zo masu da bambara-kwai

Babban alkalin alkallan Nijeriya Mai Sharia Ibrahim Mohammed Tanko shi ne ya jagoranci bayar da kalaman rantsuwar ga shugaban kasar a filin taro na Eagle Square Abuja.

Sai dai wata majiya daga fadar shugaban kasar ta tabbatar mana da cewa shugaban kasa Buhari bai gabatar da jawabin nasa na yau ga yan kasar ba, sakamakon jawabin da zai gabatar a ranar 12 ga watan June, kamar yadda a kwanakin baya ya saka hannu wajen mayar da ranar ita ma ta zama ranar Dimokaradiya a


Daga, Ibrahim M Bawa

Dalilan Da Yasa Wasu Manyan Kasar Nan Ke Kiyayya Da Shugaba Buhari
Naji tausayin masoyina shugaba Buhari da yace manyan Kasar nan ba sa son shi, amma hakan sam bai dameshi ba

Jama'a akwai abin dubawa a wannan kalma da shugaba Buhari ya furta, lallai dole mu tausaya masa, kiyayya da manyan Kasarnan tamu Nigeria musamman mabarnata daidai yake da tarar aradu da ka, saboda girman sharri da makircin su

Kiyayyar da manyan kasa suke yiwa shugaba Buhari ba a kan komai bane face don ya tsayu akan gaskiya, su kuma wasu manyan kasar akan karya da mugunta da zalunci da danniya suka gina siyasarsu har suka girma suka zama manyan kasa

Kiyayyar da wasu manyan Kasa suke yiwa shugaba Buhari baya raba nasaba da kokarin shugaba Buhari na son kishin-kasa da zaman lafiya, wanda su kuma wasu manyan kasa imba ana zubar da jini ana rushe garuruwan talakawa ba, to burinsu bai cika ba, sun fi so talaka ya kasance cikin tashin hankali ya kasa fahimtar 'yancinsa da arzikin da Allah Ya shimfide a cikin Kasa ta yanda za'a mayar da hankali akan inganta arzikin kasa talaka zai mora

Kiyayyar da wasu manyan Kasa suke yiwa shugaba Buhari ba a kan komai bane face don ya toshe hanyar sata, wanda wasu daga cikin manyan Kasa da suke gaba dashi sun gina kansu ne har suka zama manyan kasa da kudin sata wanda suka sace daga baitul-malin Nigeria

Daga cikin manyan kasa da suke kiyayya wa shugaba Buhari idan an bincika za'a tarar da cewa irinsu ne suka mayar da siyasa babbar haja wanda babban burinsu shine su kai ga madafun iko, su mallaki makullin baitul-mali, suna kwasar kudi, daga su sai 'ya'yansu, da karuwai da kawalansu, sai kuma 'yan daudu, ta wannan hanyar ce suka zama manyan masu kudi a duniya.

Babban misali da tsohon shugaban Kasa Mr OO, ya fito daga gidan yari a shekarar 1998 ko 1999 kudin dake cikin asusun ajiyarsa na banki bai kai dubu 30 ba, amma yau yana daga cikin masu arzikin Nigeria, a ina ya samu kudin? daga baitul-malin Nigeria

Wasu daga cikin manyan kasa suna kin shugaba Buhari saboda baya cikin kungiyoyinsu na tsafi da shan jini, Shugaba Buhari ba matsafi bane kamar su ba, shugaba Buhari da Allah (SWT) ya dogara bai yarda da tsafi ba, bashi da wani malamin tsubbu ko boka da yake bashi umarni yana Luwadi ko cin naman jarirai da sauran sassan jikin 'dan-adam kamar yadda wasu manyan miyagun 'yan siyasa suke yi, a sanina addu'ah ake yiwa shugaba Buhari a ruwan zamzam ana bashi yana yin wanka don neman tsarin Allah daga sharrin matsafa

Wasu daga cikin manyan Kasa suna kin shugaba Buhari saboda bai yarda da alfarma wacce ba bisa ka'ida ba, kuma bai yarda a juyashi yadda aka ga dama ba, yayinda su kuma manyan kasa abinda suke so kenan wato haramtacciyar alfarma, su kawo wanda suke so a baiwa mukamin Minista ko babban darakta a wata ma'aikata, idan aka daura nasu, dole kamfanoninsu za'a dinga baiwa kwangila, ayi aiki kadan a ki karasawa ,a cinye sauran kudin kwangila, shugaba Buhari bai yarda da wannan ba, dole su nuna masa kiyayya

Akwai wasu daga cikin manyan kasa wadanda suka mayar da ayyukan ta'addanci a matsayin hanyar neman kudi, suka dinga yin amfani da wannan damar suna damfarar gwamnatin Nigeria, shugaba Buhari sai da aka kai matakin da ya fito ya yiwa 'yan Nigeria bayani akan irin wannan damfara da ake yi a dalilin ayyukan ta'addanci, yace dole yayi taka tsantsan, kunga kuwa duk wanda aka toshe masa hanyar neman kudi koda haramtacciyar hanyace dole yayi fushi

Shugaba Buhari ya karbi mulki a hannun mutanen da suka shafe shekaru 16 suna mulki suka kasa tsinana komai a cikin kasa, a lokacin da kudin gwamnatin Nigeria baya tafiya akan magance ayyukan ta'addanci idan aka cire gwamnatin Jonathan, Obasanjo shine ya samu dukkan dama da zai gina Nigeria amma ya kasa tsinana komai, haka Buhari yazo ya karbi mulki a hannunsu bayan sunyi kaca-kaca da arzikin kasa, ya karbi mulki a hannun mutanen da sau biyu ko sau uku suna murda zaben shugaban kasa da talakawan Nigeria suka masa, don haka ba abin m

Ban Mallaki Wata Kadara Ko Dukiya Ba, Tun Daga Shekara Hudu zuwa Yau - Inji Buhari
Shugaban kasa Muhammad Buhari, ya ce shi dai bai mallaki komai ba, tun daga lokacin da aka rantsar da shi mulkin Najeriya a shekara ta 2015 zuwa yanzu.

Buharin, ya ce, kadara da dukiyarsa da aka sani tun lokacin da ya bayyana su, yar yanzu hakan take ba ta sauya zani ba.

Menene raáyoyinku kan wannan furuci na Baba Buhari?

Tuesday, May 28, 2019

Takaitaccen Tarihin Sarkin Karaye Alh. Dr. Ibrahim Abubakar II.
An haifi mai martaba sarkin karaye a garin Karaye dake jahar Kano. Mai martaba sarki yayi karatunsa na elementary a karamar hukumar karaye, sannan yayi karatun sakandiren sa a garin Danbatta. Mai martaba sarkin yayi karatu a makarantar horon ma aikata ta jahar Kano (Kano state polytechnic) sannan ya wuce Kaduna state polytechnic ya cigaba da karatu. Mai martaba sarki yayi karatun digri dinsa na uku a Lincon university America
.
INDA YAYI AIKI:
.
Mai girma sarkin Karaye yayi ayyuka a wurare dabam dabam, cikin su akwai:
.
Mai aikatar ciniki da kasuwanci ta jahar Kano
.
Kamfanin motoci na steer dake Bauchi
.
NEPA
.
Director a Kano state ministry of Information
.
Kwamishina a ma aikatar kasuwanci da masana antu ta jahar Kano
.
SARAUTA
.
Mai martaba sarki ya zama yariman Karaye a shekara 1988, daga bisani kuma ya zama sarkin karaye a shekara 1998
.

NASABAR SA
.
Mai martaba sarki dane wajan
.
Sarkin Karaye Abubakar ii
.
Magajin gari Aliyu
.
Sarkin karaye Usman
.
Sarkin karaye Mohd
.
ALLAH YA KARAWA SARKI LAFIYA
.

Monday, May 27, 2019

Masu Kirana Da "Baba Go Slow" Zan Basu Mamaki A Next Level - BuhariShugaban kasa Buhari ya bayyana cewar da sannu masu kiran shi da sunaye daban daban na cin zarafi, kamar Baba Go Slow za su sha mamaki a zagaye na biyu na mulkin shi, kuma za su gani shin hakan ko kuwa.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa ta kai tsaye da aka yi da shi a babban Gidan Talabijin na kasa NTA a cikin daren nan.
Shugaba Buhari ya tabbatar da cewar gwamnatin shi ta samu gagarumar nasara kawar da Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin kasar nan, inda ya bayyana cewar kafin zuwan shi karagar mulki a shekarar 2015, Boko Haram sun rigaya sun mamaye jihar Borno inda kananan hukumomi 17 ke hannun su, amma zuwan gwanatin shi suka fatattake su gaba daya zaman lafiya ya dawo a yankin.

Dangane da batun masu satar mutane suna neman kudin fansa kuwa, Buhari ya tabbatar da cewar masu aikata wannan danyen aikin bakin haure daga wata kasa, kuma sun tsallako Najeriya da zimmar dagula kasa, amma da yardar Allah gwanatin shi na bakin kokarin ta wajen kawo karshen wannan matsala, inda ya bukaci 'yan Najeriya da taimakon gwamnati wajen fallasa miyagu da ke cikin su.

Shugaban kasa Buhari ya kuma yi karin haske dangane da wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sadarwa na zamani, inda aka nuno shugaban na gudu shi da wasu mutane a kasar Saudiyya, Buhari ya bayyana cewar ya je kasar Saudiyya ne domin ibadar Umrah, kuma daga cikin ayyukan ibadar Umrah akwai inda aka tanadi mutum ya yi gudu, saboda haka gudun da ya yi ibada ce ba wasan tsere ba.
Da Duminsa: Shugaban Kasa Na Ganawa Da Wasu Gwamnonin Arewa A Villa
A yanzun haka shugaban kasa Buhari na ganawa da wasu team Arewa a fadar shugaban kasa dake Aso Villa a yau Litinin din nan.

Daga cikin gwamnonin da suke ganawa da shugaban kasar akwai gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu, da kuma mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo

Duk da dai labarin abin da suke tattaunawa a kansa bai zo hannun manema labarai ba, amma ana hasashen zaman baya rasa nasaba da kai hare haren da yan ta'adda ke yawan kaiwa a jihohin Arewa da suka hada da Katsina, da Zamfara da Kaduna da Sokoto da sauransu

Buhari Ya Rattaba Hannu A Kan Kasafin Naira Tiriliyan 8.9 Na 2019
Tun daga yau 27 Ga Mayu, 2019, kasafin 2019 ya tabbata kuma ya zama a cikin doka kenan.

Ya sa wa kasafin hannu yau Litinin da karfe 11 na rana, a ofishin sa da ke Fadar Gwamnatin Tarayya, Aso Villa, Abuja.

Majalisar Dattawa da ta Tarayya ne suka amince da kasafin kuma suka mika masa domin ya sa masa hannu a zama doka.

Sun aika wa Shugaba Buhari kasafin bayan sun kara shi daga naira tiriliyan 8.826 suwa naira tiriliyan 8.916 a cikin watan Disamban 2018.
Majalisun sun yi wa kasafin karain naira bilyan 90 kenan.

Yayin da Buhari ke sa wa kasafin hannu, ya ce karin da Majalisun biyu suka yi wa kasafin zai shafi yadda za a aiwatar da shi, wajen gudanar da ayyuka.

Majalisun dai sun yi wa wasu bangarori karin kudi, yayin da kuma suka rage a wasu bangarorin.

Buhari ya sa kasafin hannu a gaban Kakakin Majalisa Yakubu Dogara, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu da kuma Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa a kan Kasafin Kudi, Sanata Danjuma Goje.

Daga baya Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya isa wurin a makare.

Friday, May 24, 2019

Zamfara: INEC Ta Bayyana Matakin Da Za Ta Dauka Akan Hukuncin Kotun Koli
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta yi magana kan abin da ya dace ta yi bayan da Kotun Koli ta soke nasarar da jam’iyyar APC ta yi a zabukan Jihar Zamfara.

A na ta jawabin, INEC ta bayyana cewa ta yi taron gaggawa domin duba hukuncin da kotun ta zartas.

Daga nan sai Hukumar Zaben Mai Zaman Kanta ta Kasa ta ce za ta dauki mataki na karshe a ranar Litinin mai zuwa.

“Biyo bayan hukuncin da Kotun Koli ta yanke, inda ta soke zaben Gwamna, na Majalisar Dattawa, na Tarayya da na Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, INEC ta gudanar da taron gaggawa domin tattauna lamarin.

“Kotun Koli ta ce ta watsar da dukkan kuri’un da aka jefa wa jam’iyyar APC a Zamfara, don haka dan takarar da ya zo na biyu, kuma ya samu yawan kuri’un da ake bukata, shine zai zama wanda ya yi nasara.

Don haka INEC za ta sake zama ranar Asabar, 25 Ga Mayu ta sake tattauna batun, sannan kuma a ranar 27 Ga Mayu, wato Litinin, INEC za ta yi wa jama’a jawabi.”

Kamar yadda hukumar ta fitar da bayani a yau Juma’a.

Idan ba a manta ba, tun da farko INEC ta haramta wa jam’iyyar APC shiga zabe a jihar Zamfara, a bisa dalilin cewa ba a yi zaben fidda-gwani a jihar a karkashin ita jam’iyyar APC din ba.

Zamfara: Nasarar Jam'iyyar PDP Ya Tabbatar Da Adalcin Shugaba Buhari
Ayau Duniya takara yadda   shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Adaline Mai Adalci Atsakanin Alummar Najeriya.

Tsabar gaskiyar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ce tasa jam,iyar  APC tarasa Mulkin jahar Zamfara.

Ayau kotun kolin Najeriya ta yanke hukuncin cewa jam,iyar PDP itace Wacce Ta Lashe Zaban gwamnan jahar Zamfara dana yan Majalisun jahar baki daya.

Abinda Zai Tabbatar ma da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Adaline Mai Adalci Atsakanin Alumma Shine PDP Basukai Kara kotu ba kuma basa Cikin Mutanan da Sukakai Kara kotu Amma Saboda Adalcin gwamnatin baba Buhari yasa Tami kama jam,iyar PDP Ragamar Mulkin jahar Zamfara Domin Sune Suka Chika Ka,idojin Tsayawa Takara Acikin jahar baki daya.

Muna Kara Rokon Ubangiji Allah ya tabbatar da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Akan gaskiya da Adalci.

Gwamna Ganduje Ya Bada Umarnin Sabunta Masarautar Bichi
Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya amince da gyara masarautar Bichi tare da fadada ta. Kafin a samar da sabuwar masurauta a cikin garin.

Da safiyar yau Juma'a ne dai Gwamnan ya tura kwamishinan ayyuka na jihar Kano Injiniya Aminu Ali Wudil tare da Dan majalisar tarayya mai wakital karamar hukumar Bichi Injiniya Abubakar Kabir Abubakar Bichi domin su duba wanna masaurauta da kuma filin da ya dace a yi sabuwar masaurautar da kuma duba filin masallacin idi na garin Bichi. Yadda za a kawata shi tare da fadada shi.

Haka zalika an duba babban titin zuwa masallacin yadda za a sabunta shi ya koma na zamani.

Daga nan an duba aikin zuba kwalta na cikin gari yadda yake tafiya.

Shugaban karamar Hukumar Bichi, Hon. Sani Makaddas Bardan Bichi ne ya jagoranci wannan tawaga ya kuma zagaya da su.

A nasa bangaren, Mai Martaba Sarkin Bichi Alh. Aminu Ado Bayero ya godewa Gwamna Ganduje da Dan majalisar tarayya Injiniya ABUBAKAR BICHI da Shugaban karamar Hukumar Bichi kan yadda suke kokarin taimakawa al'ummarsu.

Thursday, May 23, 2019

Wadanda Ba Su Da Zargin Cin Hanci Da Rashawa Ne Kadai Zamu Nada Kwamishinoni - Inji Ganduje
Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi jawabin bankwana ga shugaban ma’aikatan jihar Kano tare da kwamishinoni a cikin kwanakin da ya rage na  wa’adin mulkin gwamnan a zangon farko.

Ganduje ya bayyana jin dadin sa da godiya ga sakataren gwamnatin jiha, Alhaji Usman Alhaji bisa jajircewarsa a tafiyar da mulkin jihar Kano.

“Sakataren gwamnati muna godiya, anyi aiki tukuru, sosai da sosai, komai ya tafi dai-dai, banyi mamaki ba saboda kana da kwarewa a aiki na gwamnati.

Gwamna Ganduje ya godewa shugaban ma’aikata tare da yaba masa akan yadda ya rike kungiyar kwadago har aka kammala shekaru 4 ba tare da samun babbar matsala da ma’aikatan jihar ba.

Bugu da ƙari Gwamna Ganduje ya  godewa kwamishinoni tare da yaba musu akan yadda har suka kammala wa'adinsu ba’a same su da wani da zargin cin hanci da rashawa ba.

“Ina gode muku, har muka gama, ba’a zarge ku da cin hanci da rashawa ba, ba’a zargemu da nuna bambanci wajen sarrafa ma’aikata. Wannnan  ba karamin kokari bane.

A ƙarshe Gwamnan yace dole ne su tantance wadanda zasu kara baiwa aiki a jihar Kano, dole sai wanda yake mai amana tare da zama mai biyayya ga gwamnan, haka zalika wanda ba zai ci hanci da rashawa ba.

Wednesday, May 22, 2019

BUHARI YA LASHI TAKOBIN CETO JAHAR KATSINA DAGA MATSALAR TSARODaga Ibrahim M Bawa

Shugaban Kasa Muhammad a yau Laraba ya umurci sufeton yan sandan Nijeriya Muhammed Abubakar Adamu da shugaban tsaron Nijeriya (Chief of Defence Staff) General Abayomi Gabriel Olonisakin da su gaggauta samar da kyakkyawan tsaro a jihar Katsina da kuma kawo masa rahoton nasarar da suka samu ta tsaro a duk fadin jihar ba tare da bata lokaci ba.
.
A sakon shugaban kasar da aka fitar daga hannun babban mai taimaka shugaban kasar a fannin sha'anin yada labarai Malam Garba Shehu ya ce shugaban kasar ya kuma jajantawa al'ummar jihar Katsina bisa iftila'in kashe kashen da suka yi wa wadanda ba su ji ba su gani ba a jihar.
.
Ya kuma bayyana nuna damuwa da kaduwa a bisa abubuwan dake faruwa a jihar inda ya bayar da umurnin nan take da jami'an tsaron Nijeriya su kawo karshen abin ba tare da bata lokaci ba.

Jafaar Jafaar Ya Bayyana Hotunan Datti Assalafiy A Dandalin Facebook


Mawallafin jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar ya saki hoton marubucin harkokin tsaron nan da yayi suna a duniyar Facebook wato Datti Assalafi.

Mista Jaafar yace asalin sunansa Abdussamad Adam inda ake yi mashi inkiya da Datti Assalafi.

Assalafi dai Jami'in tsaro ne na farin kaya.

Assalafi ya shahara wajen rubutu kan sha'anin tsaro da Boko Haram kafin daga bisani ya koma rubuta ra'ayinsa kan sha'anin siyasa da rikita-rikitar jihar Kano.

Manuniya ta ruwaito an samu rashin fahimta tsakanin mawallafin Jaridar ta Daily Nigerian da Datti Assalafi, kodayake dai Malam Jaafar yace ya yafe masa amma zai kai rahoton shafukansa ga hukumar Facebook domin yadda yake saba dokokin dandalin sadarwar.

Jaafar ya zargi Assalafi da wuce gona da iri tare. Wannan dai shine karo na farko da hotunan Malam Datti Assalafi suka bayyana a shafukan sadarwa bayan shafe shekara da shekaru ana nemansu.


Tuesday, May 21, 2019

Hukumar Hisab Ta Kama Wasu Gandayen Samari Da Basa Yin Azumi
Rundunar hukumar Hisba reshen karamar hukumar Dambatta karkashin shugabancin babban kwamanda Mal. Salisu Muhd sun kama wasu mutum 2 gandaye da basa azumi a wani sumame da suka kai Sabuwar Unguwa Dambatta a yau Litinin 20-05-2019 da rana tsaka bisa jagoranci shugaban 'yan sintiri na Hukumar (OC Operation) Rabi'u Yunusa.

Mal. Salisu Muhd ya shaida mana Jami'an Hisba sun kama Rabbilu Sani dan garin Bani Bunbun Jamhuriyar Nijar mai shekaru 35 da kuma Umar Uban daba mai shekaru 30 dan asalin garin Kanya Babura Jihar Jigawa wadanda suke sana'ar tura kurar ruwa (Garuwa) a rijiyar 'yan garuwa ta Kurna Sabuwar Unguwa Dambatta, sun kuma kama su ne a gidan wani Alh. Shuaibu a Unguwar inda a nan ne suke da zama tare da cin karansu ba babbaka.

A tuhumar da Jami'an Hisbar suka yiwa wadannan mutane 2 sun ce ko azumi 1 babu wanda yayi a cikinsu a wannan shekara, haka azumin bara ma ya wucesu ba tare da sun yi koda guda 1 ba, suna kuma neman afuwa da yafiyar hukumar a wannan ta'asa da suka aikata a cewarsu sun yi nadama.

Mal. Salisu Muhd ya shaida mana za su cigaba da tsaresu tare da basu horo mai tsanani da kuma yi musu wa'azi domin su fahimci girman laifin da suka aikata, sannan za su kirawo wanda ya basu gida domin cigaba da bincike daga bisani kuma za su mayar dasu garuruwansu, a karshe kwamandan yayi godiya da yadda al'ummar gari ke bada hadin kai ga hukumar wajen ganin sun dakile aikin alfasha a fadin karamar hukumar.

Idan baku manta ba daf da shigowar wannan wata na Ramadan mun kawo muku yadda Jami'an Hisbar suka yi sumamen atisaye a cikin garin Dambatta Inda suka kama mata 8 masu zaman kansu tare da kayan maye kala-kala da suka hada da giya, madara da sholisho da sauransu, Allah ka shirya mu a kan hanya madaidaiciya amin.

Dambatta Reporters 07060792024.

Sunday, May 19, 2019

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar ganduja yayi fata-fata da jam'iyar PDP A kotu.
Mai girma gwamnan jahar kano ya gabatar Ma da kotu Shedar da take Nunama Duniya cewa Shine Wanda yayi Nasara Azaban gwamnan Wanda  Akayi Awatannin baya.

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya gabatarwa kotu takardun dake Nuni da cewa Shine Wanda Alummar jahar Kano Suka Zaba Amatsayin gwamnan jahar daga 2019 Zuwa 2023 Mai dauke da shafukaka 1,800 da kuma shaidu 203 da za su taimaka wurin gamsar da kotu nasararsa.

 A yayin da ya ke zantawa da manema labarai bayan gabatarwa kotun sauraron karrakin zabe hujjojin kare gwamnan, Musa Lawan, daya daga cikin lauyoyin gwamnan, ya ce babu gaskiya cikin karar da PDP ta Shigar

"Mun gabatarwa kotu takardun kare kanmu kuma mun kawo su a cikin lokacin da aka kayyade mana kuma muna fatan za muyi Nasara.

Tun farko, mun cema PDP Shigar da kara kotun da tayi ba shi da Amfani Awajan Ta domin Mune Mukayi Nasarar Lashe Zabe.Inji Lauyan APC.

Lauyan ya ce za su gabatarwa kotun muhimman shaidu 203 da za su bayar da shaida a kotun da zai nuna tabbas anyi zabe a Kano kuma hakan zai sa ayi watsi da zargin da jam'iyyar PDP keyi.

Muna Rokon Ubangiji Allah yakara taimakwan gwamnan jahar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje Akan Makiyan Shi.

Binciken Kwakwaf : Dalilin takun -saka tsakanin Ganduje da Sarkin Sanusi II
Rahoton Daily Trust

Idan baku manta ba a yan makwannin da suka gabata ne gwamnan Kano Dr.Abdullahi Umar Ganduje ya rattaba hannu akan dokar samar da karin masarautu a jihar Kano, batun da yasa tun daga wannan lokaci majiyarmu ta kaddamar da bincike domin gano ainihin silar rashin jituwar dake akwai tsakanin gwamnan na Kano da kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, wanda abinda ya janyo yin hakan kenan, ga kuma abinda mukayi bincike muka gano.

Wata majiya dake da alaka da gwamnan Kano ta shaida mana cewa sau 5 sarkin na Kano na ganawa da shugaban kungiyar Kwankwasiyya, kuma tsohon gwamnan Kano Kwankwaso da kuma dan takarar sa na PDP Abba Kabir Yusuf, wanda kuma wadannan ne manyan yan adawar gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, domin daukar matakan da duk suka kamata na ganin cewa PDP ta samu nasarar darewa kujerar gwamnan Kano.

Sa’annan wata majiyar kuma ta daban ta bayyana mana cewa Sarki Sanusi ya umarci dukkanin dagatai da hakiman sa akan cewa lallai su tabbatar jama’iyyar APC bata kai labari ba a zaben gwamnan da ya gabata, kana kuma yayi amfani da kusancin sa da manya wajen tara kudade masu yawan gaske da PDP zatayi amfani dasu a zaben domin tabbatar da samun nasarar ta,

Sarkin bai tsaya haka nan ba, a ranar da za'ayi zabe a ranar 23 ga watan Fabrairu, sarkin ya tara dukkanin jama'ar dake a fadar masarautar jihar Kano kana ya umarci su dangwalawa jama'iyyar PDP wanda kuma hakan akayi, har ya kasance PDP ce taci akwatun dake gidan sarki gabadaya a sakamakon umarnin da ya bayar.

Kai abin bai tsaya iya nan ba, hatta kuri'ar sarkin ma an gano cewa PDP ya dangwalawa, sabanin wani irin abu da tsohon sarkin Kano Ado Bayero keyi, na dukunkune kuri'ar in yayi zabe ya jefa akwatu ta yadda baza'a taba gane me ya zaba ba.

Baya ga nan an gano cewar Sarkin ya umarci dagatai da masu unguwanni dasu gabatar da rahoton cewa akwai tashin hankali ga hukumomin tsaro a tsakanin zaben gwamna zagaye na farko da zagaye na biyu don ganin cewar ba'a gudanar da zaben a zagaye na biyu ba, inda wasu masu unguwannin suka ki bin wannan umarni.

Baya ga nan Sarkin ya taka rawa wajen gabatar da jawabai ta kafafen watsa labarai wadanda ke nuna cewar Gwamnatin jihar Kano ta hayo baki 'yandaba daga kasashe makwabta da wasu jihohi domin sabbaba rashin zaman lafiya a jihar Kano a daf da shiga zabe a Karo na biyu

Ba wai a iya nan kawai lamarin ya tsaya ba, ku biyo mu a nan gaba kadan zamu karasa baku wannan rahoto domin saida takai har fadar shugaban kasa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II yaje domin ganin Ganduje bai sake samun nasara ba.

Saturday, May 18, 2019

TAKAITACCEN TARIHIN GARIN KANO

KANO sunan babbar kasar Hausa ce kuma
masarauta ce mai kwarjini a cikin kasashen Hausa da kewaye. Haka kuma Kano gari ne babba wanda ya kunshi kabilu masu yawa tare da harkokin arziki. Gari ne mai manya manya
malamai kamar su mallam Nasiru Kabara , Shehu Abubakar Atiku , Shek Ja'afar Mahmud
Adam . Sanna Garine Mai tarin Ya'nkasuwa kamar su Aliko Dan Gote , Aminu Alhasan
Dantata ,Mallam Isyaka Rabi'u da dai sauran su.

Yawan mutanen da suke garin Kano yakai
kimanin mutane Miliyan Goma (10,000,000) akidayar da aka yi a shekara ta 2006. Kano
tana da matukar tasiri a yawan mutane a
Najeriya, saboda ita ce ta fi kowace jiha yawan
mutane a Najeriya. Idan ka zo Kano zaka samu
mutane daga ko'ina a fadin duniya, tun daga
na kudancin Najeriya, zuwa kasashen dake makwabtaka da Najeriya, haka kuma za ka tarar da mutanen Sin, da kuma na kasashen Larabawa kamar Sudan, Misira ( Egypt ),
Lebanon , da kuma mutanen kasashen Turai.

Kano ta yi suna wajen kasuwancin da ta bunkasa a kai, har ya zamana ana cewa da ita
Cibiyar Kasuwanci, haka kuma tarihin Kano ya
nuna daman can Kano tana da suna wurin cinikayya tsakaninta da mutanen gabas ta
tsakiya. Jihar Kano tana da iyaka da misalin
jihhohi hudu su ne :-

*. Jihar Kaduna
*. Jihar Katsina
*. Jihar Jigawa
*. Jihar Bauchi

Kano tanada kananan hukumomi guda 44 sune :-

*. Dala
*. Kano
*. Kumbotso *. Nasarawa
*. Rimin-Gado
*. Tofa
*. Doguwa
*. Tudun Wada
*. Sumaila *. Wudil
*. Takai
*. Albasu
*. Bebeji
*. Rano
*. Bunkure *. Karaye
*. Kiru
*. Kabo
*. Kura
*. Madobi
*. Gwarzo *. Shanono
*. Dawakin Kudu
*. Tsanyawa
*. Bichi
*. Dambatta
*. Minjibir *. Ungogo
*. Gezawa
*. Gabasawa
*. Bagwai
*. Gaya
*. Dawakin Tofa *. Warawa
*. Fagge
*. Gwale
*. Tarauni
*. Ajingi
*. Garko *. Garun Mallam
*. Rogo
*. Makoda
*. Kibiya
*. Kunchi.

Ana wa garin Kano Kirarin da "Kano jalla babbar Hausa, ta dabo tumbin giwa ko
da me ka zo amfika".

wannan shine kirarin da akewa wanna
katafaren gari. Idan ana zancen suwane
sukafara zama a kano to a tarihi zai iya cewa
kamar yanda Allah subhanahu wata'ala yayi mutane a sauran sassan Duniya hakama ya ajiye bayin sa a garin Kano .

Akwai Kabilu a garin kano da dama sun
zo kasar kano kamar su Madatai da Dala.
zuwan wadannan kabilu yakara habaka garin
Kano kabilar Madatai ta riga Kabilar Dala zuwa
Kano, da suka zo wannan gari mai Albarka sun
sami wasu kabilu masu yawa a Kano Amma ana ce da su Kabilun Kwararrafa .

 Wannan Tarihi a takaice kenan.

Dafatan kowa yasha ruwa lafiya.
Allah yasa mu dace.

Tuesday, May 14, 2019

Ƙarin Masarautu A Jahar Kano Ya Rage Farin Jinin Kwankwasiyya
A bayyana ta ke ɗariƙar kwankwasiyya ɗariƙar Siyasa ce wacce ta ke da tarin matasa Maza da mata, sai dai kuma duk da irin yawan na su, yawan bai cika amfanarsu ba. Domin idan ka yi nazari tare da tsaida hankali waje guda za ka tarar baki ƴan cirani mazauna birnin Kano su na da matuƙar yawa a cikin wannan ƙungiya.

Bugu da ƙari ɗariƙar kwankwasiyya ƙungiya ce da ta ƙware wajen cin Mutunci tare da keta alfarmar masu mutunci. Amma hakan bai zama abin mamaki ba musamman idan ka san tarihin Madugun ɗariƙar ta kwankwasiyya.

Abin ya zama tamkar wutar daji musamman Idan aka yi la'akari da yadda ƴan kwankwasiyya a jihar Kano su ke nuna tsananin adawa da karin masarautu da gwamnatin jihar Kano ta yi.

Kafafen sada zumunta musamman dandalin fasebuk ya zama wata mahada ta cin mutuncin gwamna Abdullahi Umar Ganduje Tare da Sarakunan Masarautar Bichi, Rano, Ƙaraye, da Gaya. Amma hakan ba zai zo da mamaki ba, domin mafi yawan masu wanna tijarar baki ne mazauna Kano, ma'ana ba asalin mutanen Kano ba ne cirani ya kawo iyayensu.

Abin da ƴan kwankwasiyya su ka kasa fahimta shi ne yadda su ke daɓawa kansu wuƙa ba tare da sun sani ba, ma'ana bisa wannan adawar da cin mutuncin da su ke wa waɗannan Sarakunan, hakan ta sanya su ke kara rasa dimbin masoyansu a faɗin jihar Kano, musamman a yankunan waɗannan masarautu.

Domin kawo yanzu dubban ƴan kwankwasiyya sun yi adabo da wannan ƙungiya bisa dalilin yadda su ka nuna bakin cikinsu a fili akan cigaban yankunan su, domin sun yadda mahaifarsu ta fi ƙungiyar Siyasar kwankwasiyya.

Karshen saƙon shi ne kullum kwankwasiyya kara haduwa ta ke da masifar zagwanyewar dimbin magoya baya tare da dushashewar hasken madugunsu, amma rashin fahimta da makauniyar soyayya ta hanasu fahimtar hakan.

Ku biyoni cikin rubutuna na gaba.

'Yan Bebeji Sun Yi Zanga-Zanga Lumana Ta Neman A Chanja Musu Hakimin Su
Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya tura wakilcin Kwamishinan Labarai Hon Mohammed Garba da mai ba shi shawara akan harkokin yada labarai Salihu Tanko Yakasai domin sauraron koke koken yan asalin karamar hukumar Bebeji karkashin Jagaorancin Umar A Baba jagoran Bebeji Local Government Concerned Citizens, sun gudanar da zanga zangar lumana bisa nuna goyon bayan su ga Sabon Sarkin su na Rano wanda Gwamnatin jiha tayi bisa jagorancin Gwamna Ganduje da kuma kin amincewar su da neman a cire musu hakimin su na Bebeji saboda rashin zaman sa a garin na Bebeji da kuma kin kulawa da al'ummar sa. Kwamishinan Labarai yayi alkawarin isar da sakon su ga mai Girma Gwamna.

Salihu Tanko Yakasai
Special Adviser Media
Government House Kano
May 14, 2019.

Sunday, May 12, 2019

Hotuna: Ganduje Ya Jagoranci Tawagar Gwamnati Zuwa Mikawa Sarkin Rano Sandarsa


Mai girma Gwamnan jihar Kano *Dr. Abdullahi Umar Ganduje* ya jagoranci tawagar Gwamnati ciki har da mataimakinsa *Dr. Nasiru Yusuf Gawuna* da sanatan Kano ta Kudu *Arc. Kabir Ibrahim Gaya* da sanatan Kano ta Arewa *Barau Jibrin Maliya* da sifika *Kabiru Alhassan Rurum* zuwa mikawa mai martaba Sarkin Rano *Alh. Tafida Abubakar Ila* sandarsa ta mulki mai girman daraja ta daya, inda anan take dukkan hakiman dake karkashin masarautar ta Rano suka karaso gaban Sarki tare da gabatar mubaya'arsu ga wannan nadi mai albarka.
Ayau Lahadi 12/5/2019.
📸✍🏾:-- *Abbakar DK*
S.A na Mataimakin Gwamnan Kano.

Saturday, May 11, 2019

Sharri Akai Wa Sheikh Dr. Isah Fantami. Be Zagi Kwankwaso Ba - Datti Assalafy
"Wata jaridar yanar gizo irin ta mutanen Kwankwasiyya a jiya ta wallafa wani labari kamar haka:
!
KWANKWASO JAHILI NE KOH SHARAR MASALLACI BAI CHANCHANTA YA SAMU BA BARE SHUGABAN KASA - Dr Isah Ali Pantami

Shahararren Malamin Addinin Muslinci A Nigeria sheikh Dr Isah Ali Pantami Ya Bayyana Cewa Kwankwaso Jahili Ne Wanda Baisan Me Yakeyi Ba,

Pantamin Ya bayyana hakanne Yayin Gabatar Da Tafsirin Watan Ramadana A Abuja ,Inda yace Shekaru Bakwai Baya Naji Da Kunne na Kwankwaso Yana Kalubalantar Me Yasa Allah Ya Halicci Sauro, Yanzu Irin Wadannan Mutane Sune zamu Bari su shugabanci Al'umma,

Sai Dai Tun Shekaru da yawa baya Engr Dr Rabiu musa kwankwaso yayi karin hasken akan wannan maganar inda Ya bayyana cewa sam Sam ba haka yake nufi ba mutane ne suka juya masa zancensa saboda siyasa

Shin Ko Menene Hikimar Pantami Akan Taso Da wannan Magana Da Ta Wuce Tun Tsawon Shekaru Bakwai ? Daga Jaridar Nageriyarmu A Yau"

Wannan shine abinda jaridar ta wallafa, ta kuma jingina ga Malaminmu na Sunnah Ash-sheikh Dr Isa Ali Pantami, mutum sama da dubu uku ne sukayi comment, duk zagin duniya da tsinuwa sai da wasu mutanen Kwankwasiyyah suka zage Malam Isah Ali tatas, sun zageshi da mafi munin kalmomin zagi da tsinuwa, ko maguzawa ba zasu yi irin wannan zagi ga Malami ba

To amma abinda ya tabbata gaskiya shine; wato a ranar hudu ga wannan wata na Ramadan  Malam ya gabatar da tafsiri, a al'ada yakan fara amsa tambayoyi kafin sai ya ci gaba da fassara, Malam ya amsa tambaya ce akan musulmi barawo ko 'dan fashi da aka kashe ko ya halatta musulmai su sallaceshi?

Malam yayi gamsasshen bayani har ya tabo tsohuwar al'ada da akeyi a shekarun baya kafin a fahimci addini, malam yace anyi lokacin da idan ka shiga masallaci jam'i ka tsaya a bayan Liman fitar da kai ake, domin akwai wadanda aka ware sune kadai suke tsayawa a bayan Liman, Malam yace amma yanzu duk wannan abin ya zama tarihi

Malam ya kara da cewa a shekarun bayane aka samu wasu manyan 'yan siyasa musulmai wadanda basu fahimci addini ba sai su kira sunan Allah suce "Sallallahu alaihi wa sallam", sai su kira sunan Annabi Muhammad suce "Subhanahu wa ta'ala", a cikinsu ne aka samu masu cewa cikin Annabawan Allah akwai Annabi Ummaru, kuma aka samu wani 'dan siyasa da yace me yasa Allah Ya halicci sauro? to wai irin wadannan 'yan siyasar ne da suka jahilci addini suke wakiltar Musulmai..

Har Malam ya kammala tafsirin gaba daya a wannan ranar Wallahi Billahi bai ambaci sunan wani 'dan siyasa ba ko guda daya, amma sai akace wai ya ambaci sunan kwankwaso, har yanzu akwai karatun yana nan a cikin whatsapp  group dina guda 13 da na saka, Malam bai ambaci sunan kowa ba, kuma babu shakka alhakkin zagi da tsinuwa da 'yan Kwankwasiyyah suka yiwa Malam zai kare a kansu ne da kuma wanda ya wallafa rubutun na karya da sharri

Wallahi ban taba ganin wasu mutane da aka renesu da son yin zagi da ashar da tsinuwa kamar wasu daga cikin magoya bayan Kwankwaso ba, duk wanda ya ambaci gwaninsu ko da bai zageshi ba to su kam zasu mayar da martani da mummunan ashariya da tsinuwa, wannan itace tarbiyyan da aka basu?, ko da yake ance kowa yana kyauta da abinda yake dashi ne

Allah Ya sauwake

Dalilan Da Suka Na Kafa Sababbin Masarautu A Jahar Kano - Ganduje
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano yace ya yanke shawarar samar da sabbin masarautu hudu ne a jihar saboda ya kai jihar zuwa mataki na gaba wato ( Next Level) .

A ranar Laraba, 8 ga watan Mayu ne majalisar dokokin jihar ta gabatar da wata doka na kacaccala masarautar Kano zuwa gida biyar.Kuma Ganduje ya sanya hannu sannan ya aiwatar da dokar a wannan ranar.

Mutane da dama na ganin Ganduje ya samar da sabbin masarautun don ya rage iko da mulkin Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, kan banbancin siyasa.

Sai dai, da yake jawabi ga manema labarai a fadar Shugaban kasa, Ganduje yace mutanen da ke Allah wadai da hukuncin “na da damar nuna ra’ayinsu amma za mu kai Kano zuwa mataki na gaba ne sannan muna bukatar tsarin al’ada tsayayye wanda za a dama dasu, musamman a bangarorin ilimi, tsaro da noma.”

Yayi bayanin ne a gefe guda na taron karammawa na kungiyar gwamnoni da ke gudana a fadar Shugaban kasa, Abuja.

Yace an rarraba masarautar ne saboda jihar Kano ‘na bukatar jjircewar sarakunan gargajiya.

"Ta hanyar raba tsarin, muna bin tarihi ne. Shekarun baya tunma kafin shekaru 800 da kuke magana a kai, lamarin ba haka yake ba.

"Don haka idan an kafa abu shekaru 800 da suka gabata, abubuwa na ci gaba yanzu kuma za a samu wasu shekaru 800 anan gaba. Don haka ku duba tarihin.
"Don haka, ba muzgunawa bane, bana adawa dashi. Duba, kamata yayi ma ya dunga tattaunawa da shugaban karamar hukuma, bisa ga kundin tsarin kasar Najeriya.

Friday, May 10, 2019

Gobe Za Ai Bikin Mika Takardar Nadin Sababbin Sarakuna A Kano
Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR na gaiyatar al'ummar jihar Kano zuwa bikin mika takardar nadin sababbin Sarakuna na yanka masu daraja ta daya da suka hada da:

1- Sarkin Rano Alhaji Tafida Abubakar Ila
2- Sarkin Gaya Alhaj Ibrahim Abdulqadir Gaya
3- Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero
4- Sarkin Karaye Alhaji Dr Ibrahim Abubakar II

Zaai wannan taro ne a dakin taro na Sani Abach dake Kofar Mata gobe asabar 11 ha watan May da misalin karfe 12 na rana. Allah ja da ran Sarakunan mu. Amin.

Salihu Tanko Yakasai
Special Adviser Media
Government House Kano
May 10, 2019.

Ku Tabbatar Da Yan Najeriya Suna Yin Bacci Da Idanunsu Biyu A Rufe - Sakon Buhari Ga Hukumomin Tsaro
 kasa Muhammadu Buhari ya umarci shugabannin hukumomin tsaro da su kara zage dantse domin kawo karshen kalubalen tsaro dake damun sassan kasar nan.

Da yake magana da shugabannin hukumomin tsaro yayin ganawar su a ranar Alhamis, shugaba Buhari ya fada musu cewar akwai bukatar 'yan Najeriya suke bacci da idonsu biyu a rufe, cikin kwanciyar hankali.

Ibok Ekwe Ibas, shugaban rundunar sojojin ruwa, ne ya bayyana hakan yayin gana wa da manema labarai a fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala ganawar su da Buhari da misalin karfe 3:00 na yammacin ranar Alhamis.


Yace " Babban dalilin ganawar shine domin sanar da shugaban kasa halin da kasa ke ciki dangane da harkarvtsaro bayan kammala hutun kwana 10 da ya yi a kasar Ingila .
Buhari da shugabannin hukumomin tsaro

" Shugabannin hukumomin tsaro sun sanar da shi abinda ke faruwa, musamman a bangaren yaduwar kananan makamai a hannun farar hula da irin kokarin da hukumomin tsaro ke yi domin dakile matsalolin da hakan ke haifar wa.

"Ya bamu umarnin cewar mu yi iya bakin kokarin mu domin tabbatar da cewar 'yan Najeriya sun kwanta bacci sun tashi cikin kwanciyar hankali ba tare da fargabar matsalar rashin tsaro ba," a cewar sa.

A ranar Alhamis ne shugaba Buhari ya sake ganawa da shugabannin hukumomin tsaro a karo na biyu bayan dawowar sa daga hutun kwana 10 da ya yi a kasar Ingila.

Sun fara ganawar ne da misain karfe 11:00 na safe, wacce ta kai su har karfe 3:00 na rana.

Muhimman Batutuwa 10 Game Da Rayuwar Shareef Rabi'u Usman Baba
Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, da sanyin safiyar Alhamis, 9 ga watan Mayu wanda yayi daidai da 4 ga watan Ramadan Allah Ya yi ma fitaccen sha'irin nan mai wakokin begen Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, Sherif Rabiu Usman Baba rasuwa.

Da wannan ne majiyarmu ta kawo mana wasu muhimman bayanai game da wannan bijimin mawakin bege dan asalin jahar Kano daya shahara musamman a tsakanin shekarun 1980 zuwa 2000, kamar haka;

Shariff Rabiu Usman Baba

1- A shekarar 1965 aka haifi Shariff Rabiu Usman Baba

2 - Dan asalin unguwar Gwammaja ne, amma yana zama a Janbulo

3 - Shine shugaban kungiyar masu bege ‘Shu’ara’ul Islam’

4- Shi ya fara zamanantar da wakokin bege da kade kade

5- Shekarunsa 54 Allah Yayi masa rasuwa

6- Rabiu Baba yayi fama da ciwon kafa wanda yayi ajalinsa

7- Da Asubahin ranar Alhamis ya rasu

8 - Ya rasu yana da Mata 4

9 - Ya rasu ya bar yaya 18

10 - Da yammacin Alhamis aka yi jana’izarsa

A zamaninsa, marigayi Rabiu Usman Baba ya ciri tuta wajen rera wakokin yabo ga Manzon Allah da Iyalansa,

Wasu daga cikin fitattun wakokinsa sun hada da :-  Tauhidi Babu tantama, Mutuwa, Tsumagiya, Sha yabo, Majalisi, Wakar Sadiya, Zumunci, Tambaya, Sharifai, Fadima, Garkuwa, Batijaniya, Bakadiriya, Fiyayya, Sayyadil Wara da Zuma.

Har zuwa yanzu jama’a da dama na cigaba da bayyana alhininsu game da mutuwar babban sha’irin, tare da jimamin rashinsa, musamman duba da yadda wakokinsa suka yi tasiri a tsakanin mabiya darikar Tijjaniyyah da Kadiriyya.

Da fatan Allah Ya jikansa da gafar, da dukkanin Musulman da suka rigamu gidan gaskiya, Amin.

Gwamna Ganduje Ya Nada Sabon Alkalin Alkalai A Jahar Kano
Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya nada mai sharia Nura Sagir a matsayin sabon Alkalin Alkalan jahar Kano, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN, ta bayyana.

Majiyarmu ta ruwaito Sagir ya kwashe tsawon shekaru hudu yana rike da wannan mukami amma a matsayin mukamin rikon kwarya, har sai a ranar Alhamis, 9 ga watan Mayu da gwamnan ya tabbatar dashi.

Dayake jawabi a fadar gwamnatin jahar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana sabon Alkalin Alkalan a matsayin mutumin da yayi suna wajen jajircewa a bakin aiki, tare da nuna kwarewa da kokari a duk aikin daya sanya a gaba.

Haka zalika gwamnan ya shawarci sabon Alkalin Alkalan daya zage damtse tare da karkatar da hankalinsa wajen ganin ya samar da tsarin da zai gaggauta kammala sharia tare da yanke hukuncin adalci cikin kankanin lokaci.

Bugu da kari gwamnan yace gwamnatinsa zata cigaba da hada kai da bangaren sharia don ganin ta inganta sha’anin walwalar ma’aikatan sharia, tare da samar musu da yanayin aiki mai kyau.

Shima a nasa jawabin, Alkali Sagir ya bayyana godiyarsa ga Gwamna Ganduje bisa amincewa da yayi da cancantarsa ta nadashi wannan mukami, sa’annan yayi alkawarin rike amanar rantsuwar aiki daya dauka.

Daga karshe sabon jojin ya bukaci gwamnan jahar Kano daya kara nada wasu sababbin Alkalai a kotunan jahar domin ta haka ne kadai za’a iya gaggauta kammala shari’u tare da yanke hukuncin adalci cikin kankanin lokaci.

Thursday, May 9, 2019

Zanga-Zangar Adawa da Kirkiro Sababbin Masarautu a Kano Batai Armashi Ba
A yaune wata Kungiya mai suna Kano First mai adawa da Kirkiro Masarautun Rano, Karaye, Gaya da Bichi ta aiwatar da wata zanga-zanga domin nuna rashin amincewa da Kirkiro Sababbin Masarautun, sai dai a iya cewa Zanga-zangar batai armashi ba, domin la'akari da karancin mutanen da suka hakarci Zanga-zangar ya nuna cewar mutane suna goyon bayan Kirkiro Masarautun.

Tun a jiya ne dai kungiyar ta Kano First karkashin jagorancin Dr Rabiu Yusif taketa kwayayaton gayyatar al'umma zuwa Zanga-zangar amma sai gashi mutane sunki amsa kiran na Kano First.

Tun da farko a sanarwar da kungiyar ta bayar tace za'a hadu a gidan Murtala yayin daga nan za'a huce majalisar dokoki ta kano, domin yin koken rashin amincewa da dokar Kirkiro Sababbin Masarautun, to sai dai karacin mahalartar Zanga-zangar yasa ala tilas suka hakura da zuwa majalisar dokoki, sai dai suka daga 'yan kwalaye da rubuce-rubuce a jiki suka kama gabansu.
Kuskure 10 Da Samari Ke Yi Da Suke Sawa 'Yammatan Su Rabuwa Da Su
A wani nazari da majiyarmu ta yi ta gano yawaitar rabuwa tsakanin masoya, musamman a yankin kasar Hausa, hakan ne ma yasa majiyarmu ta binciko wasu dalilai guda 10 da suke kawo rabuwa a tsakanin masoyan

Idan kana mamakin yadda aka yi budurwarka ta rabu da kai, watakila kana bukatar yin tunani da irin soyayyar da ke tsakanin ka da ita.

Yi la'akari da wasu dalilai wadanda 'yammata da yawa ba sa so, wanda zai iya kawo karshen soyayyarku.

Soyayya ta gaskiya, ta na bukatar yarda da juna, da kuma hakuri ta kowacce hanya.

Amma idan ka aikata daya daga cikin wadannan kurakuran, to akwai yiwuwar soyayyarku ta kusa zuwa karshe.

Ga Kusakurai 10 da samari ke yi da suke sawa 'yammatan su rabuwa da su kamar haka -


1. Rashin sanin yadda zaka tarairayi budurwarka, ko ka dinga saka ta farin ciki.

2. Babu abinda ka iya sai tura mata sakonni ta waya,

Eh an yadda cewa sako yana da amfani a wasu lokutan. Amma kuma idan har tattaunawar da zaku yi ta na da yawa, abinda ya kamata kayi shine ka kirata.

3. Ba ka bata hakuri idan kayi mata laifi.

4. Rashin fada mata kalaman soyayya,

Da yawan 'yammata suna son kalaman soyayya, suna so saurayi ya dinga koda su.

5. Yawan yi mata karya,

Maza da yawa suna yi wa 'yammata karya, suna ganin kamar 'yammata sun fi kaunar mutum idan ya yi musu karya. Hakan ba dai dai bane saboda duk ranar da ta gano ka, to karshen soyayyarku ya zo kenan.

6. Rashin damuwa da sanin kawayenta.

Ba dole sai ka so kawayenta ba, amma ya na da kyau ka girmama alakar da ke tsakaninta da su, ya kamata su ma ka girmama su, saboda sune ginshikin soyayyarku a wasu lokutan.

7. Ba ka yi mata tambayoyi idan ta na magana da kai,

Yin shiru idan ta na magana ya na da kyau, saboda ya na nuna mata cewa hankalinka ya na wurinta, amma kuma rashin yi mata tambayoyi shi ma wata matsala ce a wurinta.


8. Rashin buri a rayuwa.

Babu wata mace da ke son namiji wanda ba shi da buri a rayuwarsa.

9. Yawan ba ta uzuri,

Irin su, baka tashi da wuri ba, cunkuso ya rike ka da dai sauransu, mata ba sa son irin wannan uzurin.

10. Yawan yi mata maganar tsohuwar budurwarka.

Duk namijin da ya fiya yiwa mace maganar tsohuwar budurwarsa, to ya tabbata cewa soyayyarsu ta kusa karewa da budurwarsa.

Monday, May 6, 2019

Majalisar Dokoki Ta Jahar Kano Zatayi Dokar Fadada Masarautar Kano Inda Zata Maida Tsarin Sarakunan Yanka.

Zaman Gaggawa a Majalissar Dokokin  Kano

Majalisar Dokoki Ta Jahar Kano Zatayi Dokar Fadada Masarautar Kano Inda Zata Maida Tsarin Sarakunan Yanka.

Wasu Lauyoyi Sunnemi Majalisar Dokoki Ta Jahar Kano Datayi  Dokar Dawo da Darajar Sarakunan yanka Na Jahar Wanda Kowanne Sarki Dajarsa Daya Da Sarkin Kano.

Masarautun Sune Kamar Haka.

Masarautar Rano
Masarautar Gaya
Masarautar Karaye
Masarautar Bichi .

Azamanta Na Yau Yan Majalisun Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Wanan Al'amari.

Kuma Nan Take Majalisa Ta Kafa Kwamitin Dazai Kawo Mata Rahoto A Gobe...


Saturday, May 4, 2019

Gwamnatin Kano Ta Dauki Nauyin Kayan Daki Da Kudin Sadaki Ga Matan Da Zata Aurar
A ci gaba da kokarin tallafawa jama'arsa, ta bangaren raya Sunnar Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam), Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sahale ga gwamnatinsa za ta yi bikin daura auren mata su Dubu Daya Da Dari Biyar (1,500) ga mazaje Dubu Daya Da Dari Biyar (1,500), wanda za a gudanar a dukkanin kananan hukumomi 44 da ke jihar.

Wannan gagarumi kuma shahararren biki za a yi shi ne Gone Lahadi 5 ga Watan Mayu, 2019, watakila a na gobe Azumin Watan Ramadhan kenan. Kuma an yi kyakkyawan tsari da shiri na gudanar da wannan gagarumin biki cikin tsafta da nutsuwa a dukkan kananan hukumomin.
Haka nan gwamnatin ce za ta biya sadaki na kudi Naira Dubu Ashirin (N20,000) ga kowace amarya a madadin ango. Wanda kudin ya kama Naira Milyan Talatin kenan (N30m), ga daukacin amare 1,500.

Hak1a nan kuma saboda a saukakawa ma'auratan, gwamnati ta dauki nauyin siyen kayan daki gaba daya tun daga kan gado da madubin daki da durowa, wajen ajiye kaya, da katifa da labule da kuma ledar daki.

Wannan kyakkyawan shiri ya nuna yadda gwamnatin Ganduje ta ke kulawa da jin dadi da kuma walwalar jama'arta. Musamman kan abinda ya shafi magancewa masu bukatar aure samun auren cikin sauki kuma kyauta kamar yadda wannan shirin ya yunkuro zai yi.

Sa'annan kuma za a bayar da kujeru gaba dayansu saboda gwangwajewar ango da amarya. Misali akwai kujera mai wajen zama na mutum uku da kuma ragowar kananan kujeru, kamar yadda a ka saba gani a gidajen amare. Cikin rufin asiri dai da kuma samun nutsuwa.

Akwai kuma shaddodi da za a rabawa angwaye, saboda su yi shigar sababbin kaya a matsayinsu na angwaye. Hakan zai kara ba su damar fitowa fes-fes cikin walwala da annashuwa a fuskokinsu tsakankanin 'yan uwa da abokai da kuma masu fatan alheri.

Wannan shirin yin wannan gagarumin biki da zai kewaye dukkan kananan hukumominmu tun farko dama ya samu wata kulawa ta musamman daga gwamna Ganduje. Saboda dama can ya kafa kwamiti na musamman da zai gudanar da wannan abin alheri.

Shi wannan kwamiti kuma ya kunshi mutane kwararru daga bangarori daban-daban. Daga ciki, baya ga malaman Addinin Musulunci, akwai kuma likitoci. Wadanda sun taka rawar gani wajen ganin an duba lafiyar wadannan mutane. Da kuma ganin kowane mutum ya dace da abinda ya zabarwa kan sa ko a likitance ne.

Auwal Wadata Sansan

Anwar  Babban Sakataren Yada Labarai Na Gwamnan Jihar Kano ne ya rubuta.

Wednesday, May 1, 2019

SHUGABA BUHARI YA QARA MAGANA AKAN SABAN ALBASHIN MA'AIKATA
A karo na biyu shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake magana akan sabon albashin ma'aikatan Najeriya.

 Ya ce babu gudu ba ja da baya gwamnatinsa sai ta biya sabon albashin ga kowanne ma'aikaci a kasar nan
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta na nan akan bakan ta na fara biyan ma'aikata sabon albashin da ya sanya hannu a watan Afrilun da ya gabata.

Shugaban kasar ya amince da sanya hannu akan dokar sabon albashin a watan Afrilun da ya gabata. A bisa dokar da shugaban kasar ya sanyawa hannun, za ta bai wa ma'aikatan Najeriya damar daukar albashin N30,000, daga tsohon albashin N18,000
 da suke dauka a da.

Shugaban kasar wanda mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ya wakilce shi a wurin taron ranar ma'aikata da aka gabatar a filin wasa na Eagle Square dake babban birnin tarayya Abuja, ya tabbatar wa da ma'aikatan kasar nan cewa gwamnati za ta biya sabon albashin da ta sanar cewa za ta fara biya.

Ya kuma tabbatar wa da ma'aikatan cewa gwamnatinsa za ta cigaba da samar da ingantaccen yanayi ga daukacin ma'aikatan kasar nan.

TO ALLAH YA SA A FARA A SA'A.

Popular Posts