Monday, April 1, 2019

Martani: Mu Hadu A Kotun, Allura Ce Zata Tono Galma - Sakon Ganduje Ga PDP
Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyaa cewar a shirye ya ke domin fuskantar jam'iyyar PDP a gaban shari'a, wacce tayi ikirarin kalubalantar nasarar da ya samu a gaban kotu

Da yake magana a kauyen Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa yayin karbar dubban masoya da suka yi tururuwa domin taya shi murna, Ganduje ya ce, "kafin a gudanar da zabe na biyu da muka lashe, sun tafka magudi da sauran laifukan zabe da muka gano daga baya
" Su na son haka kabarin da za a binne su ne a ciki ba tare da sun sani ba.

"Dole yanzu a gudanar da bincike a kan kuri'un da suke ikirarin sun samu, hakan kuma zai tona asirin irin magudin da suka tafka a wasu wuraren yayin zaben gwamna da mambobin majalisar dokoki ."

Ganduje ya bayyana cewar an gudanar da zabe sahihi na adalci a zagaye na biyu, zaben da gwamnan ya ce jam'iyyar PDP ba ta samu damar yin cushe da aringizon kuri'u ba kamar yadda tayi a zaben farko.

Da yake bawa jama'a tabbacin cewar zai cigaba da gudanar da aiyukan gina Kano da ya fara a zangon sa na biyu, Ganduje ya yi tinkahon cewar: " duk wanda ya zo Kano zai shaida yadda garin ke bunkasa.

" Zamu dora sannan mu rubanya a kan aiyukan da muke yi .

Gwamnan ya yi godiya ga dandazon jama'ar da suka zo domin taya shi murnar nasarar da ya samu a zabe tare da basu tabbacin cewar gwamnatinsa zata cigaba da aiki domin mayar da Kan daya daga cikin jihohi mafi zaman lafiya a kasa.
 " Muna godiya ga wadanda suka zabe mu, da wadanda basu zabe mu ba da ma wadanda basu yi zabe ba gaba daya, " a cewar Ganduje.

No comments:

Post a Comment

Popular Posts