Monday, April 29, 2019

SHUGABA BUHARI YA BA DA UMARNIN CETO RAYUWAR ZAINAB ALIYU

Kamar yadda rahotanni su ka tabbatar, Zainab Habib Aliyu,
‘daliba ce ‘yar asalin Jihar Kano da ta gamu da iftila’i
inda jami’an tsaron ‘kasar Saudiyya su ka kamata da
zargin safarar miyagun ‘kwayoyi ya yin da ta je aikin
Umrah!
Kuma rahotanni sun shaida dacewar wasu gurbatattun
mutane ne a filin saukwa da tashin jiragen sama su ke
sakawa duk wanda tsautsayi ya fada masa ‘kwayoyi cikin
jakarsa, kamar yadda su ka yi wa Zainab.
Sai dai, tuni mai girma Shugaban ‘kasar Nageriya, Malam
Muhammadu Buhari ya ba wa babban lauyan gwamnatin
tarayya umarnin yin duk mai iyuwa domin ganin an samu
nasarar ceto rayuwar Zainab daga kisa.
Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin babban mai
taimakawa Shugaba Muhammadu Buhari kan harkokin
‘kasashen waje.

Wednesday, April 24, 2019

MASU GARKUWA DA MUTANE SUN YI DIRAR MIKIYA A JAHAR KANO
Wasu masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wani matashi bayan sun so amfani da shi gurin ya kira musu kawunsa daga cikin gida domin su sace shi.

Masu garkuwa da mutanen sun je gidan darektan da ke kula da ayyukan ma'aikata (DPM) na karamar hukumar Dawakin Kudu, Alhaji Rabi'u Alasan, da ke garin Durun, karamar hukumar Kabo, jihar Kano, tsakanin karfe daya zuwa biyu na dare, dauke da bindigogi domin yin garkuwa da shi.

Majiyarmu, wadda ba ta bari a ambaci sunanta ba, ta yi rahoton cewa masu garkuwar sun tarar da dan yayan darektan mai suna Nazifi Abdullahi a kofar gidansa. Ganin Nazifi a kofar gidan ya sanya suka so yin amfani da shi gurin fito da kawun nasa.

Nan take suka tursasa shi ya je kofar gidan kawun nasa ya kwankwasa inda suka tsaya da shirin yana fotowa su damke shi. Sai dai cikin ikon Allah yana zuwa kofar sai yai zargin ba Nazifin kawai ne a bakin kofar ba. Nan take ya haura ta baya da ya fuskanci masu neman garkuwa da shi ne.

Ganin hakansu bai cimma ruwa ba, sai masu garkuwar suka fara harbe-harben bindiga a gurin domin razana mutane kafin kuma daga baya su gudu.

Sai dai sun tafi da dan yayan nasa, Nazifi, wanda aka ce matashi ne da har ya yi bautar Kasa. Har ya zuwa yanzu kuma ba su sake shi ba.

Tuesday, April 23, 2019

Kishi: Ya Kashe Matarsa Saboda Ta Ce Idan Ya Mutu Zata Auri Wani
Wani magidanci a jihar Naija da jami'an tsaro suka kama da laifin kashe matarshi me suna, Uwani Danjuma ya amsa laifinshi inda yace ya kashe matar tashi, Uddu ne saboda ce mai da tayi daya mutu zata auri wani mijin a lokacin da yayi wata rashin lafiya a baya.

Uwani Danjuma ya kara da cewa, na ji takaicin maganar data gaya min cewa wai idan na mutu zata auri wani mijin. wannan yasa na sassareta da adda a wuya wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwarta.

Uwani Danjuma ya kara da cewa be yi nadamar kashe matar tashi ba tunda so take ya mutu, ya kashe ta ne saboda kada ta samu damar yin aure bayan ya mutu, be kamata ta gaya min irin wannan maganar ba dan haka yasa dole ta mutu kuma nasan Allah zai saka ta a wuta saboda abinda ta gaya min", - inji shi.

Bola Ahmad Tinubu Yayi Magana Akan Tsayawarsa Takara A 2023
Tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a jam'iyyar APC,Bola Ahmad Tinubu ya fito ya karyata rade-radin da ake watsawa cewa wai yana yin kakagida ne wajan ganin an nada mutanenshi a mukamai masu tsoka dan ganin ya samu zama shugaban kasa a zaben 2023.

Tinubu yace wannan magana ba gaskiya bace sannan masu watsa wannan magana kamata yayi su lura da cewa ko tsakiyar shekarar 2019 ba'a shigaba amma suna maganar zaben 2023 sannan wannan magana rashin girmama shugaban kasa, Muhammadu Buharine.

Tinubu yace yana tare da shugaban kasa, Muhammadu Buhari kuma yana bin duk wani abu da shugaban yake dan ganin ci gaban kasar nan dan bashi goyon baya

Wednesday, April 17, 2019

CP Muhammad Wakili Ya bayyana Dalilin Daya Sa Aka Daina Jin Duriyarsa

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano CP Mohammed Wakili ya shaida wa BBC abin da ya sa aka yi kwana biyu ba a ji duriyarsa ba.

Ya ce yana nan daram dam kuma suna aikinsu yadda ya kamata.

"A baya an rika jin duriyata saboda lokacin zabe ne," kamar yadda ya shaida wa wakilinmu Khalifa Dokaji a Kano ranar Laraba.

"Ana gwagwarmayar neman zabe akwai abubuwa da dama wadanda na tsaro ne wanda yake dauke hankalin jama'a.

"Saboda haka yana bukatar a ji tabbacin cewa za a yi lafiya a gama lafiya...wanda yake duk yanzu babu su," in ji shi.

Daga nan ya ce yana nan lafiya lau kuma yana aikinsa yadda ya kamata.

Batun shaye-shaye a jihar Kano
CP Wakili ya ce tun da aka kammala zabe zuwa yanzu sun kama 'yan daba wadanda suke kurkuku fiye da 930.

Ya ce masu tu'ammali da miyagun kwayoyin sun sauya salo, "amma a yanzu haka muna binciken wani muhimmin batu."

Atiku Zai Gayyato Gwararru Daga Amurka Don Su Tabbatar Da Nasarar Sa
Dan takarar shugabancin Najeriya a Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya ce ya na gab da gayyato kwararru daga Kamfanonin fasaha na Microsoft da IBM da kuma Oracle don tabbatar da zargin sa na cewa shi ne ya lashe zaben kasar na watan Maris.

Atiku Abubakar dai ya yi ikirarin cewa hatta shafin hukumar zaben Najeriyar mai zaman kan ta INEC ya tabbatar da cewa ya doke Muhammadu Buhari na APC da kuri’un da yawansu ya kai miliyan 1 da dubu dari 6.

Kalaman na Atiku na zuwa ne bayan martinin INEC kan ikirarin sa cikin makon jiya na cewa ya gano shi ke da nasarar, inda hukumar ta INEC ta ce ba daga shafin ta ya samu bayanan sa ba.

Sai dai Atiku Abubakar ya ce sakamakon wanda aka yiwa suna da INEC_PRES_RSLT_SRV2019 na kunshe a wani kundi mai adireshi kamar haka 94-57-A5-DC-64-B9 da lambar tantancewa ta ID 00252-70000-0000-AA535.

A cewar Atiku Abubakar sakamakon da ke kunshe cikin Kundin ya nuna ya samu kuri’u 18,356,732 wanda ya kayar da shugaba Muhammadu Buhari na APC wanda ya samu kuri’u 16,741,430.

Friday, April 12, 2019

Gwamnatin Kano Tayi Karin Haske Game Da Biyawa Dalibai Kudin NECO
Gwamanatin jihar Kano ta bayyana cewa ɗaliban da suka samu darusa 5 ko fiye da suka hada da Turanci da kuma lissafi ne kawai za su ci gajiyar biyan kudin jarrabawar kammala sakandare ta NECO a wannan shekara da gwamnatin za ta biya.

kwamishiniyar ilimi ta jihar Kano Hajiya Aisha Jafar ce ta bayyana hakan a yau yayin taron manema labarai, tana mai cewa muhimmancin da ilimi ke da shi ne ya sanya gwamnatin daukar wannan mataki na biya wa wadanda suka ci darussa 5 kudin na NECO.

Idan za'a iya tunawa dai a makon jiya ne Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bada sanarwar ɗaukar nauyin ɗaliban jihar waɗanda ba su yi nasarar cin jarabawar kwalafayin ba, inda gwamnati za ta biya masu kuɗin jarabawar NECO.

Gwamnan wanda ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba ya aikewa manema labaru a daren jiya, ya gargadi shugabannin makarantun sakandiren da su guji karɓar kuɗi daga hannun ɗaliban.

Sanarwar ta ce matakin na daga cikin ƙudirin gwamnatin jihar na taimakawa iyayen yara su biyawa yaran su kuɗin jarabawa.

Sannan kuma, sanarwar ta ce matakin, na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na tabbatar da cewa an samar da ingantaccen ilimi ga talakawan jihar.

Mun Shirya Tsaf Don Gabatar Da Dokar Tsarin Tazarar Haihuwa A Kano - Sarkin Kano
Sarkin Kano Muhammad Sanusi II, ya bayyana cewa sun gama shirye-shirye tsaf na gabatar da dokar tsarin tazarar haihuwa ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje, domin mai da tsarin doka a jihar Kano.

Sarkin ya bayyana hakan jiya, a wurin wani taron tattaunawa da suka gabatar a Kano, ya ce za a gabatar da tsarin ne don magance kalubalen da ake fama dashi a kasar Hausa na tsarin iyali, da kuma matsalar tsaron da ake fama da ita a yankuna da dama na kasar nan.

Sarkin ya ce ya fahimci cewa al'umma ba za su fahimci inda ya sa gaba ba akan wannan ra'ayi nashi, shi ne yasa ya yanke shawarar kafa kwamiti na lauyoyi da malamai domin gabatar da kudurin nashi.

Ya ce ko da yake a yanzu ya samu kashi 80 cikin 100 na dokar da ya ke so ya kafa din, amma idan har aka shigar da tsarin cikin dokar kasa, zai magance matsalolin tattalin arziki a jihar Kano.

Sarki Sanusi ya yi fatan gwamna Ganduje ya samu ya shawo kan 'yan majalisarsa don tabbata da shigar da tsarin ya zama doka a jihar, ya kara da cewa shugaban kasar Jamhuriyar Niger ya ziyarce shi, inda ya bayyana cewa shima yana jira ne a gabatar da dokar domin ya fara amfani da ita a kasar shi.

Sarkin ya bayyana cewa idan ba dauki mataki akan matsalar talaucin da ke addabar kasar nan ba, Najeriya da Jamhuriyar Demokiradiyar Congo za su dauki kashi 40 cikin dari na mutanen da ke fama da talauci a fadin duniya nan da shekarar 2050.

Sarkin ya bayyana cewa a shekarar 2050, nahiyar Afirka za ta kasance da kashi 86 cikin dari na mutanen da ke fama da matsanancin talauci a duniya, kuma Najeriya za ta dauki rabi a cikin kashi 86, inda za ta zamanto kasar da tafi kowacce kasa talauci a duniya.

A karshe Ya danganta matsayin da ake ciki yanzu na yawan haihuwa da ake, inda zaka taradda mace ta haifi 'ya'ya takwas ita daya, idan kuma mijin mata hudu ne dashi a karshe sai ka ganshi da yara 32, wadanda za su taso cikin talauci da yunwa.

Wednesday, April 10, 2019

Masu Tattaki Domin Taya Ganduje Murna Sun Samu Kyakykyawar Tarba
Wasu matasa da sukai tattaki daga Zaria Zuwa Jahar Kano domin taya Maigirma Gwamnan Dr. Abdullahi Umar Ganduje Murnar cin zabe da kuma karbar Certificate, sun samu kyakykyawar tarba daga maigirma gwamna.


Matasa wadanda suka shafe tsahon kwanaki 4 suna tattakin, sun iso Kano cikin koshin lafiya, kuma nan take bayan isowarsu aka sada su da maigirma Gwamna, inda suka taya shi murnar cin zabe.Maigirma Gwamna ya nuna jin dadinsa da wannan namijin kokarin da matasan sukai, na tahowa tun daga Zariya Zuwa Kano a kafa domin su taya shi murna, inda nan take ya bada umarnin aje a kama musu Hotel domin su huta zuwa ranar da zasu koma gida.

Haka nan an bawa matasan mota domin suyi amfani da ita wajen yawon bude ido, da ganin irin ayyukan da Gwamna Ganduje yake wa al'ummar jahar Kano.

Ga dukkan alamu de burin matasan ya cika, Na ganin Gwamna Ganduje tare da taya shi murna.


Rundunar 'Yan Sandan Jahar Kano Ta Hana Hakar Ma'adanai A Jahar

Rundunar Yansanda Najeriya Reshen Jahar Kano Sun Tabbatar da Dokar Hana Hakar Maadainan Kasa a Jahar...

A wata sanarwa da kakakin Rundunar DSP Abdullahi Haruna yafitar yace: Bisa Umarnin da Gwamnatin Tarayya ta Bayar na Hana Hakar Maadainai a wasu sassan Kasar nan sakamakon Matsalar Tsaro, Rundunar Yansandan ta Kano a Yau Talata, 9/4/2019 ta ziyarchi  wurin hakar Maadanai na Rimi dake Karamar Hukumar Sumaila Domin tabbatar dacewa dokar ta Fara Aiki.

Rundunar tace ta baza Jamianta a wajen domin tabbatar doka da order, haka nan ta gargadi Mutane dasu kaurachewa wajen,  har zuwa lokachin da Gwamnatin Tarayya zata Ayyana cewa akoma acigaba da Hakar ko kuma wata sanarwa ta Musamman.Tuesday, April 9, 2019

Buhari Zai Ja Ragamar Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya

 kasa Muhammadu Buhari ya sanya damuwa tare da daura damarar tunkarar kalubale na rashin tsaro musamman kawo karshen ta'addanci da ya yi kaka-gida a jihar Zamfara kamar yadda Sufeto janar na 'yan sanda Muhammadu Adamu ya bayyana.

Babban Sufeton na 'yan sanda ya bayyana hakan ne yayin sharhi a kan yadda matsaloli na ta'addanci da shugaban kasa Buhari ya dukufa wajen kawo karshen su a wasu sassa da ya shafa cikin kasar nan.

Sufeto Adamu wanda ya ziyarci jihar Zamfara a ranar Talata ya bayyana cewa, ziyarar sa ta wajaba da manufa ta samun sahihan rahotanni daga tushe na asali domin gano ainihin bakin zaren da zai yi tasiri wajen shimfidar matakai da daurin damara.

Babban jami'in na 'yan sanda ya bayyana cewa, hukuncin da gwamnatin tarayya ta zartar na haramta hake-haken albarkatun kasa a jihar Zamfara na da nasaba ta kusa ko nesa wajen kawo kawo karshen ta'addanci a yankunan ta.

A yayin da babban jami'in na 'yan sanda ya bayyana shirin kawo duk karshen duk wani nau'i na ta'addanci a jihar Zamfara, Gwamna Abdulaziz Yari cikin bayyana damuwa ya ce tun daga mafarar ta mummunar ta'ada a jihar ta salwantar da rayukan kimanin Mutane 3,262 yayin da Mutane 8,900 suka rasa muhallan su.

Monday, April 8, 2019

Yadda Akai Na Kayar Da Jam'iyyar PDP - Inji Gwamna GandujeGwamnatin Buhari Ta Dauko Hanyar Magance Matsalar Tsaron Jahar ZamfaraBayan wani ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi da manyan-manyan jami'an tsaron na kasa, a fadar shi dake Bila, a zaman Suncire sabon salo da tsarin yaki da ta'addanci dazai taimaka wajen magance matsalar rashin tsaro a jihar Zamfara.

Zuwa yanzu Sojojin Najeriya sun fara kaddamar da sumamen dabarar yakin kwantar Bauna domin fatattakar yan ta'addan da suke Salwantar da rayukan al'ummah da dukiyoyin su, zuwa yanzu jami'an tsaro sun kai samame a sansanin  yan ta'addan dake cikin daji.


Ta bangare guda kuma Shugaban Hukumar Yan Sanda na kasa, ya cire sanarwar hana haqan ma'adanai da yan wata kasa suke a wasu yankunan Jihar Zamfara, hukumar leqen asiri na kasa, suma sun fara kaddamar da aikin leqen asirin abun da yake janyo matsalolin rashin tsaro da garkuwa da ake da mutane a jihar Zamfara da Kaduna.

A jawabin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jajantawa al'ummar jihar Zamfara, ya nuna rashin farin cikinsa akan zub da jinin al'ummah da ake a jihar, ya kuma yi alwashin kawo karshen aiyukan ta'addanci fadin kasar nan baki daya.

Yobe State Secretary
BUHARI NEW MEDIA CENTRE

Sunday, April 7, 2019

Saboda Tsaro: Gwamnati Ta Haramta Hako Ma'adanai A Jahar Zamfara
A yau Lahadi, 7 ga Watan Afrilun 2019, gwamnatin kasar nan ta bada sanarwar cewa an dakatar da duk wani aiki da ya shafe hake-haken kayan arzikin kasa a Zamfara, a dalilin rikicin da ake ta fama da shi a jihar.

Shugaban ‘yan sandan kasar, IGP Mohammed Adamu ya bayyana wannan matsaya na gwamnatin Najeriya ne a babban birnin tarayya Abuja dazu lokacin da yake ganawa da manema labarai da ke cikin fadar shugaban kasa.

Mohammed Adamu yace gwamnati ta gano cewa akwai alaka tsakanin masu tada kafar baya a jihar Zamfara da kuma wadanda ke hako ma’adanai a boye. Wannan ya sa aka hana kowa cigaba da hake-hake a fadin jihar.

Bayan nan kuma gwamnatin Najeriyar tayi umarni ga duk mutanen kasar waje da ke hakon kayan arzikin kasa da su tattara su bar wadannan yankuna da ke dauke da alatu na arzikin gwal da kuma sinadarin karfe na kirar lid.

Wadanda ke nan a lokacin da aka dauki wannan mataki sun hada da babban Hadimin shugaban kasa watau Malam Abba Kyari da kuma Darektan hukumar DSS, Yusuf Bichi da shugaban hukumar NIA na kasa watau Ahmed Rufai.

Sai An Dauki Shekaru 10 Kan A Gyara Barnar 'Yan Boko Haram - Inji Buhari
A ranar Asabar din da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fayyace girman barnar da kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram ta haifar a kasar nan ta Najeriya da gyaran ta ba zai yiwu cikin sauki ba.

Shugaban kasa Buhari kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, ya ce za a dauki tsawon shekaru aru-aru a kasar nan gabanin gyara barnar da kungiyar ta'adda ta Boko Haram ta haifar a kasar nan.

BBuhari ya yi wannan furuci yayin gabatar da jawaban sa a taron tattalin arziki na duniya da aka gudanar a kasar Jordan inda ya fayyace girman barna da ta'addanci ya haifar wajen durkushewar Najeriya.


Cikin kalamin sa, shugaban kasa Buhari ya ce barna ta salwantar da rayuka, asarar dukiya da kadara da kungiyoyin ta'adda irin su Al Qaeda, ISIS da kuma Boko Haram suka haifar, za a dauki tsawon fiye da shekaru goma gabanin farfadowa.

A yayin da Najeriya ke ci gaba da murna ta kasancewar ta mafi girman tattalin arziki a nahiyyar Afirka, shugaban kasa Buhari ya yi kira na neman shugabannin duniya a kan hada gwiwa da juna wajen inganta jin dadin rayuwar al'ummar su domin saukaka radadi na tashin-tashina da tarzoma.

Shugaban kasa Buhari ya kuma bayyana farin cikin sa tare da godiya ga kasashen duniya da suka bayar da tallafi gami da gudunmuwa wajen yakar annobar ta'addanci da ya yi ma ta katutu musamman daular kasar Jordan karkashin jagorancin Mai Martaba Abdullahi II bin Al-Hussein.

Kashe-Kashe Da Garkuwa Da Mutane Na Matukar Sani A Cikin Damuwa - Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ta bakin mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu, yace za a kawo karshen masu kashe mutane da kuma garkuwa nan gaba kadan cikin gaggawa, ya kara da cewa kashe kashen dake faruwa lamari ne daya shafe shi kai tsaye.

Wannan matsala tana saka rayuwata cikin damuwa, kuma nake ta kokarin tattaunawa da shugabannin tsaro kowanne sati, duk saboda kawo karshen matsalar.

Baba yace yana jajantawa dukkan wadanda suka hadu da wannan matsalar, Gwamnatin ba zata zuba idanu ba.

Saturday, April 6, 2019

Garabasar MTN: Yadda Za Ka Sai 1GB A Naira #200 Kachal

Ina "yan uwana ma'abota amfani da yanar gizo, musamman masu amfani da shafukan sada zumunta na Facebook, WhatsApp, Instagram, Telegram, Youtube, da kuma masu downloadin na bidiyo da kum "yan uwana Bloggers.

Ga wata garabasa daga kamfanin sadarwa na MTN, domin kuwa wannan kamfanin ya fito mana da wata hanya mai sauki da amfani domin sayen data mai yawa da "yan kudi kadan. Shine zaka iya siyen  (1GB) akan kudi N200 kacal.

Sai de wannan Garabasar Masu tsarin MTN Pulse ne kawai zasu mori wannan tsarin,Kuma wannan datar Sati daya ne take karewa.

YADDA AKE KOMAWA MTN PULSE.

Idan kana so ka koma tsarin MTN Pulse sai ka shiga Masaage ka rubuta 406 ka turawa 131.

Ko kuma ka danna *123*2# sai ka danna kira za su watso maku tsarinkan sai ku zabi Pulse.

YADDA AKE SIYAN DATAR.

Idan zaka sai datar sai ka danna *131*65# sai ka danna kira zasu watso makaIdan suka watso maka sai ka zabi lamba 2  sai kayi Send zasu sake watso maka.Idan suka watso maka Sai ka danna lamba 1 (process) shike nan ka siya datar.


Wanda ke da tambaya ko karin bayani sai yayi.

@Usman Alkanawy.

Labari: Ganduje Ya Halarci Wajen Taron Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass
Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya halarci wajen taron Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass karo na 19 wanda Kungiyar Maj'ma'u Ahbabu Sheikh Ibrahim Inyass tare da Iyalan Marigayi Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu suka shirya a Filin wasa na Sani Abacha da ke Kano a yau Asabar 6 ga watan Maris.

Taron wanda ake gudanar dashi Garin Kano da kuma Abuja. Wannan dai shine zai zama Karo na 33 irin sa a Jere ba tare da tsallakewa ba.

Mauludin na wannan Karon an kawo shi ne Garin Kano don girmamawa ga babban Shehin Malamin nan Marigayi Khalifa Sheikh Isyaka Rabi'u kamar yadda shuwagabannin taron su ka tabbatar. Sun ce a wannan Karon taron zai zama kashi biyu ne Watau bangaren Maulud da kuma addu'a ga ruwan Marigayin(Khalifa Sheikh Isyaka Rabi'u).

Alhaji Rabi'u Isyaka Rabi'u ne Ya tabbatar da hakan tare da nuni da Cewa ahalin marigayin ne ma suka dauki dawainiyar Mauludin na Kanon.

Idan ba a manta ba dai Khalifa Sheikh Isyaka Rabi'u babban malami ne na addinin musulumci da ya shahara wajen hidimtawa Alkur'ani.

 Wannan yunkurin hidimar ne ma Ya sa ya zama mutumin farko da ya gina jami'ar Alkur'ani a Kano.  Allah ta'ala Ya sabunta masa rahama, Amin.

Daga karshe muna musu Fatan gama wannan taro lafiya. Allah ta'ala Ya maida kowa gidan sa lafiya.

Friday, April 5, 2019

Gwamna Ganduje Ya Bayanna Cewa Gwamnatinsa Za Ta Yi Tafiya Da MatasaMatasa.
Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewar sabuwar gwamnatinsa da za ta fara daga 29 ga Watan Mayu, 2019, za ta yi tafiya da matasa wajen gudanar da gwamnati. Bisa la'akari da irin gudummawar da matasan suke bayarwa wajen cigaban kasa.

Ya ce ya tabbatar matasan wannan jiha ba abinda yake gabansu illa ganin an samu cigaba  mai dorewa a wannan jiha. Ya ce saboda haka "Ina yi musu albishir da cewa wannan sabuwar gwamnati mai shigowa za ta tafi da su ka'in da na'in."


Gwamnan ya yi wannan albishir ne lokacin da shugabannin Majalisar Matasa Ta Kasa, wato "National Youth Council of Nigeria" karkashin jagorancin shugabansu na kasa, Bello Bala Shagari, ta kai masa ziyarar taya murnar sake samun nasarar zama gwamna a karo na biyu, a gidan gwamnatin jihar kano.

Ya ce saboda amincewa da yadda matasa ke kokari wajen ganin an samar da al'umma ta gari, hakan ta sa gwamnatinsa ke kokarin ganin an tallafi tafiya da kuma rayuwar matasan.

"Ina mai tabbatar muku da cewa mun ga irin kokarin da matasanmu na wannan jiha su ka yi lokacin zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma zaben gwamna da zabubbukan 'yan Majalisar Tarayya da na jiha," in ji shi.

Ya ci gaba da cewa "Kasancewar irin wannan jajircewa da matasanmu su ka yi, ya nuna a fili cewar sun yunkuro sun nunawa duniya cewar lallai za a iya gogayya da su wajen gudanar da shugabanci na gari wanda zai amfani dukkan al'umma. Za mu yi wannan tafiyar da su saboda mu na da tabbacin cewa sun yunkuro saboda su bayar da ta su gudummawar wajen raya kasa da al'umma."


Gandujen ya kara da cewa, saboda irin namijin kokarin da matasan su la nuna wajen kara samun tabbatuwar zaman lafiya, bayan kammala zabubbukan da a ka kammala kwanan nan, ya zama karin karfafa gwuiwa idan a ka nuna matasan su na da muhimmanci wajen gina kasa.

Wannan maganar ta gwamna Ganduje, kamar yadda shugaban Majalisar Matasan Na Kasa, Bello Bala Shagari ya bayyana, tabbatuwar gagarumar nasara ne da gwamnatin jihar Kano ke son assasa shi a wannan bangare na wannan kasa. Wanda kuma zai iya bazuwa zuwa ga dukkan sasaa na wannan kasa.

Shugaban ya kara da godewa gwamna Ganduje saboda hobbasa da gwamnan ya yi ta yi har sai da a ka samu tabbatuwar samar da shugabancin wannan Majalisar Matasan na farko daga yankin Arewa Maso Yamma na wannan kasa.

Ya kara yabawa Ganduje ganin yadda gwamnan ya rungumi harkokin Majalisar da matukar muhimmanci. "Haka nan kuma Alhamdulillah mun ga yadda Maigirma gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya samar da mukamai ga matasa a wannan zubin farkon na mulkinsa," in ji shi.

Ya kara wata godiyar sabuwa jin cewa ga maganar da gwamnan ya yi wajen kara samar da gurabe ga matasa a juyowa ta biyu ta mulkinsa.

Ya ce "Maigirma gwamna tun ma kafin mu zo wannan waje, mun tabbatarwa da kan mu cewar za mu zo wajen gwamnan da ya dauki matasa da muhimmancin gaske. Alhamdulillah sai ga shi kuwa ka fitar da mu kunya ka tabbatarwa da kowannenmu cewar haka kake."

Shagarin ya kara yabawa da ayyukan cigaban kasa da gwamnan Kanon yake jajircewa a kai, da yawun Majalisar Matasa ta Kasa din. Ya ce "Wannan Majalisa ta mu ta na mai tabbatar maka da goyon bayanmu kowane lokaci domin samun dorewar wannan mulki cikin nasara da kwanciyar hankali."

Anwar shine Babban Sakataren Yada Labarai Na Gwamnan Jihar Kano

Daga Abba Anwar

Thursday, April 4, 2019

Nafisa Abdullahi Ta Soki Shugaba Buhari Akan Kisan Zamfara
Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood na Hausa, Nafisa Abdullahi ta caccaki shugaban Najeriya, Muhammadu Buhai saboda yadda ya yi gum da bakinsa game da kashe-kashen da ake yi wa al’umma a wasu kauyuka da ke jihar Zamfara.

Jarumar ta soki shugaban ne biyo bayan sakon ta’aziya da ya aika ta shafin Twitter ga iyalan wani matashi, Johnson Kolade da jami’an ‘yan sanda suka kashe shi a birnin Lagos.

A martani
n da ta mayar wa Buhari, Nafisa ta ce, “ka yi magana game da daruruwa da dubban mutanen da ake kashewa a Zamfara da sauran sassan arewacin kasar kafin kisan da aka yi wa Kolade, ko kuma ka magance matsalar a lokaci guda."

Jarumar ta kara da cewa, shugaban na tsoron tsokaci kan kashe-kashen da ake yi a arewa, amma ya yi magana game da kisan da ya faru a kudancin kasar a cewarta.

Da Alama Abba K. Yusuf. Bashi Da Hujjojin Da Zai Tunkari Kotu Dasu.
A Yau Alhamis 4/4/19 ne Kotun daukaka karar zabe ta (Tribunal Court)  ta fara zamanta a jahar Kano kan zaben da ya gudana na shekara ta 2019.

Babban Alkalin kotun da ya Jagoranci Alkalai Uku 3 a zaman na yau wato Justice Nayai Aganaba ya ce sun kar6i kundin korafin zabe (Petition) guda 33 na koken 'yan takarkarin majalissun jahar da kuma na tarayya.

Justice Aganaba ya ce sai dai ba wata jam'iyar da ta kawo masa korafin zabe a matakin gwamna.

Bayan haka Alkalin kotun ya gargadi lauyoyin jam'iyu da su mutunta lokaci a zaman da za a sake nan gaba.

Wannan ne ya tabbatar mana Abba K. Yusuf bashi da hujjojin dazai tunkari kotun da su kasancewar har wannan bana bai gabatar da korafin da ya ke ta yama didi dashi ba.

Wasu Matasa Suna Tattaki Daga Zaria Zuwa Kano Domin Taya Ganduje Murna
Wasu Matasa Sun fara tattaki daga Zaria zuwa Kano Domin taya maigirma Gwamnan Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Murnar Karbar Certificate.

Matasan Daya Mai Suna UMAR HALLIRU SABO daya kuma mai suna ANAS G SOBA. sun fara tattakin ne daga jiya Laraba,

Matasan sun fara tattakin ne daga Zaria domin zuwa jahar Kano, yayin da dare yayi musu sai suka kwana a Tashar Yari.

Bayan gari ya waye sun cigaba da wannan tattakin, wanda ake sa ran a wannan Rana ya Alhamis zasu iya isowa wa.

Hausawa de sunce sa kai yafi bautawa ciwo.

Allah ya kawo su Lafiya, ya kuma maida su gida lafiya.

Wednesday, April 3, 2019

PDP Ta Kauracewa Taron Bada Takardun Shaidar Cin Zabe A Kano
Jam’iyyar PDP  a ranar yau, 3 ga watan Afrilu ta kauracewa taron gabatar da takardar shaidar cin zabe wanda hukumar zabe mai zaman kanta tayi akan abunda ta bayyana a matsayin ‘dalilai na tsaro’.

INEC ta gabatar da takardar shaidar cin zabe ga Ganduje mataimakinsa, mambobin majalisar wakilai da mambobin majalisar dokokin jihar 30 cikin 40 a wani taro mai kayatarwa da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha.


PDP a wata wasika zuwa ga INEC ta nuna adawa akan zabar wajen taron gabatar da takardun shaidar cin zaben ga zababbun mambobin majalisar na jam’iyyarta.

A wani jawabin manema labarai dauke da sa hannun kakakin kamfen din PDP a jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, yayi bayanin cewa wajen gudanar da taron bai yiwa mambobinta ba.

Dawakin Tofa ya bayyana cewa
“kamata yayi a zamo tsaka-tsaki wajen zabar wurin taron, yan PDP ba za su samu tsaro ba wajen wanda ke Kofar Mata.

Al'umma Nayi Wa Gawuna Fatan Ya Gaji Gwamna Ganduje A 2023
Al'umma da dama ne suke ta fatan alkhairi ga maigirma Mataimakin Gwamna Dr. Nasiru Yusif Gawuna, na Allah ya bashi kujerar lamba daya a kakar zabe ta 2023 daga cikinsu har dani Usman Alkanawy.

Kamar yadda kowa ya sani, yanzu Gwamna Ganduje yana kan Tenure dinsa ta biyu, kuma da alama idan ya gama babu wani wanda ya chanchanta da kujerar sama da mataimakinsa Gawuna. Duba da chanchantarsa ta kowanne fanni.

Idan Har ana Maganar Ilimine, To Gawuna Yana da Ilimin dazai Jagoranci wannan jaha tamu.

Gawuna Yana zaune da Kowa Lafiya Kuma Ya samu Kyakykyawar Sheda Daga Ciki Da wajen Wannan jahar Wannan Dalili ne ya kara sawa mutane suke ganin lalle ya chanchanta.

Bayan haka kuma Dr. Nasiru Yusif Gawuna mutum ne wanda kowa yake yabon sa domin shike iya kokarin sa wajen kyautatawa al'umma, sannan ya shahawara wajen taimakon al'umma domin inganta rayuwarsu.
.
Gawuna bashi da sa'a a fannin kyautatawa talakawa, hakika duk wata jaha zata so ta samu kamarsa a matsayin gwamnanta.

Gawuna duniya tayi masa shaida mai kyau wajen mu'amalar sa da mutane ba tare da girman kai ko fariya ba, a koda yaushe ya kasance mai hakuri da juriya wajen jagoranci.

Daga karshe ina masa fatan alkhairi, tare da fatan Allah ya cika masa burinsa na Alkhairi.

Allah ya tabbatar mana dashi a matsayin Gwamnan a 2023.

Daga naku Usman Alkanawy.

Tuesday, April 2, 2019

Gobe INEC Zata Bawa Ganduje Certificate Tare Da Zababbun 'Yan Majalisun Jaha

A Gobe ne Labara 3/04/2019 Hukumar zabe ta kasa INEC ta sanya a matsayin ranar da zata bawa Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje Tare Da Mataimakinsa Dakta Nasiru Yusuf Gawuna da yan majalisar jiha 40 shaidarsu ta cin zabe.

Inec zata bada wannan shaidar ne a rufaffen dakin taro dake Sani Abacha Stadium dake birnin Kano da misalin Karfe. 10:00am na safe.

A baya de 'yan adawa sun tayi magana game da jinkiri na bada wannan shaida, inda suke fadin Inec taki bashi certificate dine sakamakon ta gano anyi akwai rashin gaskiya a cikin zaben.
Sai de tun kafin zance yayi ni INEC ta fitar da sanarwa cewa ta sanya ranar 3/4/2019 a matsayin ranar da zata bawa ganduje tare da zababbun 'yan majalisa certificate.


Daga Karshe Jam'iyyar APC ta jahar kano na gayyatar kafatanin yayan ta zuwa wajen bada wannan certificate da hukumar INEC za tayi, jam'iyyar APC tace bata daukewa kowa ba.

CP Wakili Ya Kama Masu Sha Da Sayar Da Miyagun Kwayoyi Su 200Rundunar’yan sanda ta jihar Kano ta ce za ta cigaba da tsaftace jihar Kano ta hanyar cigaba da kame masu hannu wajen aikata sha da sayar da miyagun kwayoyi.

Kakakn rundunar a nan Kano DSP Abdullahi Haruna ne ya bayyana hakan a yau, yayin tattaunawar sa da wakiliyar mu Aisha Shehu Kabara.

Ya ce rundunar ta kame masu laifin ne a sumamen da ta Kai sassa daban-daban na jihar Kano.

Zaben Kano: Shugaba Kasa Buhari Ya Yi Magana Akan Zaben Jahar KanoDubunnan mutane da manyan kungiyoyi, sun yi ta maganganu daban-daban akan sakamakon zaben gwamnan jihar Kano, inda wasu suke kalubalantar shugaba Buhari da cewar ya yi shiru akan zarge-zargen da ake yi na amfani da 'yan daba dan ta da tarzoma a zaben da aka yi na jihar

Mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya yi wa manema labarai bayani, a wata hira da suka yi da shi kan lamarin.

Ga bayanin da Malam Garba Shehu ya yi kamar haka :

"Kira da ake ta yi na cewa wai shugaba Buhari ya binciki zaben Kano, ko shugaba Buhari ya soke ko kuma ya dauka ya bawa wani, shugaban kasa ba shi da ikon yin hakan a dokar kasa.

Kuma kada a manta cewa shi kansa shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin Allah ya bashi wannan matsayi, sau uku ya na yin takarar nan ta shugaban Najeriya ana cewa an kada shi, duk san da aka ce an kada shi zai dauki maganarsa ya kai kotu, tun daga kasa har sai ya kai kotun koli ta Najeriya."

"Mai yasa wadanda suke ganin sun fadi, ko kuma ba ayi musu adalci a zaben Kano ba, ba za su dauki maganar su je kotu kamar yadda doka ta ce ba.? Idan shugaba Buhari ya ce wani abu akan wannan, ko ya kafa bincike, idan aka kawo masa sakamakon binciken ya zai yi? "

"Ba shi da ikon ya ce ya soke zabe, ba shi da ikon ya ce a dauki nasara a hannun wane a bawa wane, kotun nan dai da aka ce aje, idan mutum yana da shaida sai ya dauka ya je ya gabatarwa kotu shaidunsa. Ba wai ka tsaya kana zargin shugaba Muhammadu Buhari ba, mu abinda mu ke zato shi ne, so ake a narkar da matsayi da kimar shugaba Muhammadu Buhari ya ke da ita a idon al'umma, saboda bukatar gabatar da hakan ba ta yanzu ba ce.
"Gani ake yi idan ya gama mulki a 2023, duk wanda ya dauko ya ce ayi za ayi, saboda haka tunda yanzu bukata ba ta biya ba, bari nan gaba a hana shi tasiri,"
in ji Malam Garba Shehu.

Monday, April 1, 2019

Bazan Taba Butulcewa Kanawa Ba, Kuma Bani Da Nufin Cutar Da Kowa - Inji Ganduje
Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatinsa ba ta zo da nufin cutar da kowa ba walau dan siyasa ko kuma ma'aikacin gwamnati. Wannan na kunshe ne a wani takarda da komishinan yada labarun jihar, Alhaji Muhammad Garba ya fitar.

Ya bayyana cewa, gwamna Umar Ganduje ya ce ba zai butulcewa Kanawa ba kuma gwamnatinsa ba za ta wulakanta kowa walau ma'aikata ko kuma mazauna jihar. "siyasa ra'ayi ce kuma kowa na da ikon bayyana ra'ayinsa kuma an yi an gama, dan haka mu na da babban aiki a gabanmu kuma sai mun hada kai domin Kano tamu ce baki daya" inji gwamnan.

Daga karshe Komishinan ya sanar a cikin takardar cewa gwamnan ya bayyana zai ci gaba da bai wa duk wanda ya cancanta girmansa musammam duk wanda ya nemi da su yi aiki tare da niyyar ci gaban jihar Kano.

Abinda Aka Baiwa Masu Garkuwa Da Mutane Kafin Su Sake Ni - Sheikh Sulaiman
Sheikh Ahmad Sulaiman, fitaccen makarancin Qura,ani, ya yi hira da kamfanin jaridar Daily Trust inda ya bayyana halin da ya shiga bayan ya shafe kwanaki 13 a hannun wasu masu garkuwa da mutane da suka sace shi a kan hayar Sheme zuwa Kankara a jihar Katsina.

Da yake amsa tambaya a kan adadin kudin da masu garkuwa da mutanen suka karba kafin su sake shi, sai Shehun malamin ya ce; "na ji an ce sun nemi miliyan N30, amma kudin da aka kawo masu basu cika.

"A daren da za a sake mu, sun zo sun umarce mu da mu gaggauta saka takalman mu, mu fito saboda sun ji labarin cewar ana shirin kawo masu hari saboda mu.

"Bayan mun isa wani wuri bisa rakiyar wasu daga cikinsu da babu nakami a hannun su, sai suka fahimci cewar mutanen da suka zo ba abokan gabar da suke tsammani bane, mutanen da suka zo da mahaifiyar shugaban masu garkuwar da suka kama mu ne domin yin musayar mu da ita.

"Haka aka karbe mu; a gefe guda masu garkuwa da mutane, a daya gefen ga jami'an tsaro da suka kawo mahaifiyar shugaban wadanda suka yi garkuwa da mu, haka aka yi musayar mu da dattijuwar a gaban dakarun soji a Danmusa da ke jihar Katsina.

"Daga baya ne mu ka fahimci cewar mahaifiyar shugaban masu garkuwar ta shafe tsawon kwanaki bakwai a hannun jami'an tsaro saboda ta ki amsa cewar dan ta'addar dan ta ne. Daga karshe dai ita ce ta zama silar samun 'yancin mu.

Martani: Mu Hadu A Kotun, Allura Ce Zata Tono Galma - Sakon Ganduje Ga PDP
Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyaa cewar a shirye ya ke domin fuskantar jam'iyyar PDP a gaban shari'a, wacce tayi ikirarin kalubalantar nasarar da ya samu a gaban kotu

Da yake magana a kauyen Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa yayin karbar dubban masoya da suka yi tururuwa domin taya shi murna, Ganduje ya ce, "kafin a gudanar da zabe na biyu da muka lashe, sun tafka magudi da sauran laifukan zabe da muka gano daga baya
" Su na son haka kabarin da za a binne su ne a ciki ba tare da sun sani ba.

"Dole yanzu a gudanar da bincike a kan kuri'un da suke ikirarin sun samu, hakan kuma zai tona asirin irin magudin da suka tafka a wasu wuraren yayin zaben gwamna da mambobin majalisar dokoki ."

Ganduje ya bayyana cewar an gudanar da zabe sahihi na adalci a zagaye na biyu, zaben da gwamnan ya ce jam'iyyar PDP ba ta samu damar yin cushe da aringizon kuri'u ba kamar yadda tayi a zaben farko.

Da yake bawa jama'a tabbacin cewar zai cigaba da gudanar da aiyukan gina Kano da ya fara a zangon sa na biyu, Ganduje ya yi tinkahon cewar: " duk wanda ya zo Kano zai shaida yadda garin ke bunkasa.

" Zamu dora sannan mu rubanya a kan aiyukan da muke yi .

Gwamnan ya yi godiya ga dandazon jama'ar da suka zo domin taya shi murnar nasarar da ya samu a zabe tare da basu tabbacin cewar gwamnatinsa zata cigaba da aiki domin mayar da Kan daya daga cikin jihohi mafi zaman lafiya a kasa.
 " Muna godiya ga wadanda suka zabe mu, da wadanda basu zabe mu ba da ma wadanda basu yi zabe ba gaba daya, " a cewar Ganduje.

Popular Posts