Wednesday, March 20, 2019

Ƙungiyar Lauyoyi Ta Baiwa Kwamishinan Ƴan Sanda Na Jihar Kano Wa'adin Kwanaki BiyuƘungiyar lauyoyi ta ƙasa reshen jihar Kano ta bukaci kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano CP Wakili Muhmmad, da ya ba ta haƙuri nan da sa'oi 48 bisa cin zarafin da wasu yan sanda suka yiwa mambobinta yayin da suke gudanar da aikinsu.

Kungiyar cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun sakatarenta, Mujtaba Adamu Ameen tayi tur da matakin rundunar yan sandan na tsare lauyoyin a lokacin da suke tsaka da nazartar sakamakon zaɓen da hukumar zaɓe ta ƙasa ta amince da shi.

Ƙungiyar ta yi kira ga kwamishinan yan sanda da ya tsame kansa daga harkokin siyasa ta la'akari da yadda take bayyana cewa yana ketare doka wajen aiwatar da ayyukansa.

A ranar talatar data gabata ne dai wasu yan sanda su kusan 30 cikin motoci kirar Hilux suka yi dirar mikiya a sakatariyar kungiyar lauyoyin dake jihar Kano inda suka yi awon gaba da lauyoyin dake tsaka da aiki zuwa shelkwatar rundunar dake Bompai domin tsare su.

No comments:

Post a Comment

Popular Posts