Friday, March 15, 2019

Kwankwaso ya umurci Abba Gida-gida kada ya biya mafi karancin albashi N30,000


Jagoran jam'iyyar PDP kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya ce gwamnatin PDP da zata hau mulki ba zata biya mafi karancin kudin albashin N30,000 ba.

Ya ce gwamnatin surukinsa Abba Gida Gida ba zata iya biya ba saboda da alamun zata tarar da gwamnatin Ganduje ta wawure dukkan kudin baitul malin jihar.

Kwankwaso, wanda yayi jawabi da gungun mabiyan Kwankwasiyya a jihar Kaduna ya ce PDP na da tabbacin samun nasara a zaben zagaye na biyu da za'ayi kuma ba zata biya kudin albashi N30,000 ba kamar yadda Ganduje yayi alkawari.

Yace: "A matsayina na jagoran jam'iyya a Kano, na umurci Abba Kabir Yusuf, da kada ya biya mafi karancin albashi saboda shirin APC ne kuma ba mu yarda da shi ba"
"Duk da cewa zamu tabbatar da cewa ma'aikata sun samu albashi kafin ranar 25 na kowace wata, amma ba zamu biya mafi karancin albashi."


A yanzu haka, hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta sanar da cewa ba'a samu kammala zaben jihar Kano ba, Abba Yusuf Kabir na PDP yana da kuri'u 1,014,474 yayinda Abdullahi Umar Ganduje na APC ya samu 987,819.

Tazarar dake tsakaninsu 26,655 amma tazarar bai kai yawan kuri'un da akayi watsi da su ba wanda hakan yasa ba za'a iya alanta zakara ba har sai an sake zaben wadanda akayi watsi da kuri'unsu.

No comments:

Post a Comment

Popular Posts