Friday, March 15, 2019

GASKIYA TA FARA FITOWA KAN YADDA ZABEN JIHAR KANO YA KASANCE


Kwamishinan kananan hukumomin jihar Kano, Alhaji Murtala Sulen Garo ya musanta zargin da ake masa na sa hannu cikin tayar da hankali a ofishin hukumar INEC ta karamar hukumar Nassarawa tare da mataimakin gwamna Nasiru Yusuf Gawuna da har ta kai ga sun yaga sakamakon zaben gwamna na karamar hukumar, Murtala ya bayyana haka ne a jiya Alhamis, 14 ga watan Maris a lokacin da yake ganawa da 'yan jaridu a ofishinsa, inda ya ambaci sunan tsofaffin 'yan majalisar wakilai, Farouk Lawan da Nasiru Sule Garo a matsayin wadanda suka kekketa sakamakon zaben mazabar Gama.


Sai dai a jawabinsa, Garo ya fadi yadda aka yi komai kuma ya ce jam'iyyar PDP ita ce ta shirya labarin kanzon kurege, inda yace magoya bayan PDP ne suka rirrikeshi da nufin hanashi shiga ofishin hukumar INEC, a dalilin haka ne suka kekketa masa riga.

Kuma ya kara da cewar shi da Gawuna sun isa ofishin ne a lokacin da suka samu labarin Farouk Lawan da Nasiru sun isa ofishin lokacin da ake tattara alkalumman sakamakon zabe da nufin tayar da hankali, har ma suka kekketa sakamakon zaben ba tare da wani yace musu uffan ba, hatta 'yan sanda basu yi musu komai ba. A karshe Murtala ya ce ba mu da cikakken yakini game da kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, saboda yana goyon bayan ta'adin da PDP ke shiryawa a jihar Kano, baya mana adalci.

4 comments:

 1. Makaryacin banxa,ya xaay Bayan sunsansu suke da nasara su yaga result,ka fadawa Kahului irinta uber an embarrassment to kano

  ReplyDelete
  Replies

  1. Makaryacin banxa,ya xaay Bayan sunsansu suke da nasara su yaga result,ka fadawa Jahilai irinka u ar an embarrassment to kano

   Delete
 2. Don Allah aringa fadar gaskiya banda son kai

  ReplyDelete
 3. Wannan Kadanne Daga Cikin Aikin Yan PDP Commander

  ReplyDelete

Popular Posts