Wednesday, March 6, 2019

Duk Wanda Allah Ya Bawa Nasara, Zan Taya Shi Murna - Inji GandujeA yaune gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yayin saka hannu a yarjeniyar zaman lafiya game da zaben gwamnoni mai zuwa yace idan har ya fadi zabe zai kira wanda yayi nasara a waya yayi masa murna.

Gwamna Ganduje ya kara da cewa shi mulki na Allah ne indai har ya fadi zai yarda da kaddara ya amince da duk wanda Allah ya baiwa nasara.


A Ranar asabar mai zuwa ne za a gudanar da zaben Gwamnoni da 'yan majalisun jaha ako wacce jaha dake fadin kasar nan, inda a nan jahar kano za'a fafata da Gwamna mai ci wato Dr. Abdullahi Umar Ganduje, tare da Abba k. Yusif. Bakwankwashen da ake wa take da (Abba gida gida). A daya bangare kuma akwai Mallam Saihu Sagir Takai, Da kuma Muhammed Sani Abacha.

Wannan zabe de lokaci ne kawai zai nuna wanda zai yi nasara a tsakaninsu.

Fatan mu de Allah yasa ayi zabe lafiya a kuma gama lafiya.

2 comments:

Popular Posts