Saturday, March 23, 2019

Babu Wani Ɗan Daba Ko Ɗaya Da Ya Shigo Kano, Balle Har A Samu Tashin Hankali ---- In Ji DIG Antony MichealMuƙaddashin sufetan ƴan sanda na ƙasa DIG Antony Micheal Ogbizi, ya bayyana cewa jami’an tsaron ƴan sanda sun ɗauki matakan gaggawa wajen tabbatar da cewa komai ya tafi daidai a guraren da aka kusan samun tangarɗa a yayin gudanar da zaɓukan cike gurbi na jihar da a ke gudanarwa a yau Asabar.

Antony Micheal ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke  tattaunawarsa da manema labarai.

 “A mazaɓar gama da ke karamar hukumar Nassarawa an samu fitowar jama’a sosai kuma zabyen ya tafi lafiyar kalau."

Ya ƙara da cewa  a ƴan ƙalilan ɗin wasu guraren inda a ka samu ‘yar tunja-tunja, mun shiga tsakani, domin dawo da zaman lafiya.

Antony Micheay ya musanta zargin da ake na shigowar ƴan daba a rumfunan zaɓen da ke faɗin jihar Kano, da kuma cewa wai an kama wasu Kwamishinoni a lokacin zaɓen.

"Babu rahoton kawo ƴan daba a zaɓen ba. Mu na da isassun jami'an ƴan sanda. Jita-jitar cewa an kama wasu kwamishinoni ƙarya ce tsagwaronta.”

A ƙarshe ya ce kawo yanzu dai komai ya lafa, bayan da jami’an tsaro su ka hana bangarori biyun tayar da ƙayar baya a rumfunan zaɓen da ake da matsaloli watakila saboda ganin alamun faduwa.

No comments:

Post a Comment

Popular Posts