Tuesday, March 12, 2019

An Gano Yadda Jam'iyyar PDP Ta Shirya Yin Magudi A Zaben Jahar KanoDaga: Comrade Haruna Sardauna

Kungiyoyin saka ido a al'amuran zabe na ciki da wajen Najeriya sun gano alaqaluman yadda jam'iyyar adawata  PDP ta shirya yin magudi a zaben gwamna jihar Kano.

Bayan bayyana irin magudin da jam'iyyar adawa ta PDP ta shirya ne, Hukumar zabe na kasa ta gaggauta sauke zaben wasu mazabbu da aka gano a kananan Hukumomi 21 cikin 44, inda ake saka ran Hukumar zata cire sabon ranar da za'a gudanar da zaben yankunan da aka gano sun shirya magudi.


Jam'iyyar APC mai mulki a jihar tayi kira ga magoya bayanta kan cewa, su kwantar da hankalin su, kar su yi rikici ko tada tarzoma, akwai yiwar Hukumar zabe zatayi adalci kamar yadda ta Kungiyoyin saka ido a al'amuran zabe suka gano yadda jam'iyyar adawata PDP suka shirya yin magudi domin murde zabe.

No comments:

Post a Comment

Popular Posts