Sunday, March 31, 2019

Har Yanzu Nijeriya Ba Ta Iya Ciyar Da Kan Ta - Inji Shugaban Kasa BuhariShugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce har yanzu Nijeriya ta na fuskantar kalubale ta fuskar ciyar da kan ta da kuma sama wa kamfanoni kayan aiki ta hanyar noma.

Buhari ya bayyana haka ne, a wajen bikin bude kasuwar baje-koli ta kasa da kasa karo na 40 a Kaduna, inda ce kalubalen har yanzu ya na nan duk da cewa noma ya na taimakawa da kashi 25 da rabi wajen bunkasar tattalin arzikin Nijeriya.

Bikin baje-koli da ake gudanarwa a kowacce shekara, ya na gudana ne har tsawon kwanaki goma a karkashin cibiyar masana’antu, da albarkatun kasa da noma ta jihar Kaduna KADCCIMA, inda ake baje-kolin sana’o’i da fasahohin cikin gida da kasashen waje.

Shugaba Buhari, wanda ya samu wakilcin ministan masana’antu, da kasuwanci da zuba hannun jari Okechukwu Enelama, ya ce kulla hadaka tsakanin noma da masana’antu zai cike gibin da ake samu na karancin abinci da kayayyakin masarufi.

A cewar sa, Niyeriya na ci-gaba da fuskantar matsalar cimma bukatun ‘yan Nijeriya ta fuskar abinci, da kayayyakin da masana’antu ke bukata domin gudanar da ayyukansu.

"Ni ba dan Najeriya ba ne" : Nnamdi Kanu ya mayarwa da kotu martaniA jiya Asabar  ne, shugaban kungiyar ma su kokarin kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya ba wa mutane da yawa mamaki, a lokacin da ya bayyana cewa shi ba dan Najeriya ba ne, kuma ba shi da wata alaka da Najeriya.

A lokacin da yake bayanin, a gidan Radiyon Biafra, Kanu ya ce zai kalubalanci kotun da ta ba da damar kamo shi a birnin Landan.

Idan baku manta ba, majiyarmu ta kawo muku rahoton cewa wata Kotun Koli da ke Abuja ta bayar da damar kamo Kanu a duk inda yake, saboda ya ki bayyana a gabanta.

A lokacin da ya ke magana da manema labarai, Kanu ya ce "duk wani yunkuri da gwamnati ta yi akan kamo ni a shirye na ke, kuma zamu kalubalanci kowacce kotu a birnin Landan ni da lauyoyina.

"Sannan kuma ni ba dan Najeriya ba ne, saboda haka shari'arku ba za ta yi aiki a kaina ba, kuma duk wanda ya ke so ya ji dalilina na kin komawa kotu to ya fara tambayar sojojin da su ka je gidana mai su ka je yi?

Saturday, March 30, 2019

Ganduje Ya Godewa 'Yan Social Media Bisa Gudunmawarsu A Zaben Da Akai

Maigirma gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, a cikin sakonnin yabawa da godiya da yake kan wadanda su ka taimaka wajen gudanar da zabensa da a ka yi ranar 23 ga Watan Maris cikin kwanciyar hankali da lumana, ya na kuma godiya ta musamman ga masu ta'ammali da kafafen sadarwa na zamani, wadanda a ka fi sani da 'Social Media' wajen ganin an yi zabe lafiya an kammala lafiya.Daga kan 'yan Social Media wadanda su ke a kungiyance da kuma wadanda suke da wasu farfajiyoyi na hadin gwuiwa da ma kuma wadanda suke ba a kungiyance ba, amma fa masu yin abinda ya kamata wajen tabbatuwar zaman lafiyar al'umma, gwamnan ya na mika godiya tare da jinjinawa wajen ganin ba a yi amfani da su wajen tayar da zaune tsaye ba.

Ya kara da yi musu godiya wajen kokarin da su ma su ka yi na ganin wannan gwamnati mai kawowa wannan jiha cigaban kasa, ta kara samun nasarar zabenta da a ka yi har na tsahon wasu shekaru hudu masu zuwa.

Gwamnan ya kara kira ga wadannan masu ta'ammali da wadannan hanyoyin sadarwa na zamani da su kara dagewa wajen ganin sun yi amfani da wannan dama da su ke da ita wajen kara wayar da kan al'umma ta hanyoyin da su ka dace, saboda cigaba da samun zaman lafiya a wannan jiha da kuma kasa baki daya.


Ya kara kira gare su, da su tabbatar kullum ba za su yada abu ba sai idan ya kasance gaskiya ne. Kuma abu ne wanda zai kara inganta rayuwar al'umma.

Anwar shine Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano

Daga Abba Anwar

Friday, March 29, 2019

Sarkin Kano Ya Tura Manya Hakimai Domin Su Bawa Gwamna Ganduje Hakuri
Daga Hassan Chikinza Rano

Yanzu da misalin karfe 5:30 na Jumaar nan 29 ga watan maris Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya tura manyan Hakimansa wajen Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje domin subashi hakuri ya yarda da zuwan Sarki fadar Gwamnati domin bada hakuri kan abubuwan da Sarki ya aikata lokacin zabe.

Sarkin Kano Wanda kiri kiri yafito yana goyon bayan Jamiyyar adawa ta PDP, sannan bayan rashin kammaluwar zaben aka jiyo sarkin yanata kokarin a soke wannan zaben domin bawa Jamiyyar PDP Wanda aka rawaito cewar Gwamna yasamu duk hirar da akayi da Sarki ta waya.

Tun a farkon wannan satin akace Sarkin yana son zuwa don taya Gwamna murna amma borin kunya yahanashi,sabida haka yasa manyan Hakimansa suzo don bawa Gwamna Hakuri kasancewar ansan Gwamna mutum me ganin mutuncin manya.

Zaben Kano: Duk wanda yace anyi kisa a zaben Kano, ya kawo Hujja – Gwamnatin KanoGwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Dr Abdullahi Ganduje ta musanta zarge-zarge da akeyi mata na samun hargitsi wanda har yayi sanadiyyar asarar rayuka sama da guda 5 a lokacin da aka gudanar da cike zaben Gwamna a jihar ta Kano ranar 23/03/19.

Da yake bayani a taron manema labarai, Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Muhammad Garba ya ce babu wani abu mai suna tada hankali a zaben da aka gudanar a jihar Kano.

Gwamnatin ta kalubalanci duk mai cewa anyi kisa ya kawo hujjar da zata tabbatar da haka.

“Babu wanda ya fito yayi zanga-zanga a jihar Kano bayan an bayyana sakamakon zabe a jihar Kano.”

Ranar zaben dai hotuna sukayi ta yawo a shafukan sada zumunta dama wasu manyan Jaridun Najeriya, sun nuna yadda akayi amfani da wasu matasa, majiya karfi tare da mugayen makamai wajen hana mutane yin zabe cikin nutsuwa.

Wasu majiyoyin sun rawaito cewa matasan har  duka suke yiwa wadanda suka zo zaben wata jami’iyya wacce su ‘yan daban ba ita suke yi ba.

An samu bidiyoyi dayawa wadanda mata suke korafin cewa an musu tsirara domin sunzo zabar wata jami’iyya ta daban, duba da yadda akace ‘yan daban sun mamaye akwatinan zaben.

Wednesday, March 27, 2019

Uba Ya Kori Dan Cikinsa Saboda Zagin Buhari Da Yake A Dandalin FacebookWani mutum a jihar Kano ya sallami yaron shi saboda zagin Shugaban kasa Buhari da yake yi a kafar sadarwar zamani wato Facebook.

A cewar mutumin tun bayan kammala zaben jahar Kano yaron ya buge da zagin Shugaban kasa Buhari a kafar sadarwa, duk da kiran shi da nayi naja masa kunne akan wannan dabiar amma bai daina ba, hakan yasa na yanke shawarar sallamar sa kasancewar ba zan iya cigaba da ciyarda mai zagin mahaifan wasu ba.

Ko ba komi Buhari ya girmeni ni kaina bare yaron da na Haifa, ba mutunci bane ace yaro karami kamar shi yana zagin manya kuma ni mahaifin shi na hanashi amma yaki hanuwa, tunda har ba zai iya jin magana ta ba gara na sallame shi ya koma wajen wadanda yake jin maganar su.

Alaramma Malam Ahmad Suleman Kano tare da abokan tafiyarsa sun kubutaMalam Ahmad Suleman Kano tare da abokan tafiyarsa sun kubuta daga hannun wadanda sukayi garkuwa da su a daren yau Laraba

Dukkan godiya ta tabbata Allah, duk wanda ya taimaka ta kowani bangare har su Malam suka kubuta muna fatan Allah Ya sakawa kowa da gidan Aljannah Madaukakiya.


GODIYA TA TABBATA GA ALLAH, SANNAN GA GWAMNATIN NIGERIA DA JAMI'AN TSARONTA:


1. Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki da Ya kubutar mana da Sheikh Ahmad Sulaiman tare 'yan tawagarsa lami lafiya ba tare da an ba da ko sisin kwabo ba.

2. Lalle godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki Ubangijin Annabawa da Manzanni, sannan ga Gwamnatin Nigeria bisa waklicin jami'an tsaronta musamman ma DG DSS, sannan jinjina ga Shugaban kungiyar Izalah na Kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau; saboda wannan nasara da aka samu na kubutar da Sheikh Ahmad Sulaiman tare da 'yan tawagarsa daga hannayen wadannan muyagun mujurumai.

3. Allah muke roko da Ya taimake mu Ya saftace mana kasarmu daga dauda da sharrin dukkan masu sharri. Ameen.

Tuesday, March 26, 2019

Bayan Tafiyar DIG Micheal Antony Ogbizi. CP Wakili Ya Dawo Bakin Aiki
Kwamishinan ‘yan sandar jihar Kano, CP Muhammad Wakili ya dawo bakin aiki, na kasancewa shugaban rundunar ‘yan sandan jihar Kano, jim kadan bayan tafiyar DIG Anthony Micheal Ogbizi daga jihar ta Kano a matsayin  jami’in da rundunar ‘yan sanda ta turo domin kula da zaben da bai kammala ba na Gwamna a Kano.

Kwanaki kadan dai rundunar ta turo wasu manyan jami’an ‘yan sanda domin tabbatar da gudanar da sahihin zabe cikin kwanciyar hankali.

Sai dai kungiyoyi dayawa na ganin zaben da aka gudanar ba zabe ne da akayishi bisa ka’i’da ba, duba daga yadda akayi magudin zaben da kuma hana jama’ar garin yin zaben ba.

Lamarin daya tada hargisti da tarzoma a fadin jihar Kano a lokacin gudanar da zaben.

Monday, March 25, 2019

Ina Godiya Ga Kanawa, Da Suka Sake Bani Dama A Karo Na Biyu - Inji GandujeGwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya godewa mutanen jihar Kano bisa dama da suka sake bashi ya jagoranci jihar a karo ta biyu.
Ganduje ya bayyana cewa mutanen jihar sunyi na’am ne da irin romon deimokradiyya da yake ta kwarara musu lungu-lungu, kwararo-kwararo shine ya sa suka ga yafi dacewa da ya shugabance su a jihar suka fito suka zabe shi.
Ya bayyana cewa lallai ba zai yi kasa-kasa ba wajen ganin ya sassaka wa dadanda suka zabe shi har da ma wadanda basu zabe shi ba sannan zai yi gwamnati ne na kowa da kowa.
Idan ba a manta ba a jiya ne a aka bayyana zaben gwamnan jihar Kano inda gwamna mai ci Abdullahi Ganduje ya yi nasara a zaben.
Ganduje ya samu kuri’u miliyan 1,033,695 inda ya ba abokin hamayyar sa na jam’iyyar PDP, Abba Yusuf ratar kuri’u 8000 da yan wani abu.
Wannan zabe dai an koka a kan sa cewa jami’an tsaro ba su yi adalci ba a zaben.
Zaben Kano Demokradiyya Ce Zalla, Wadanda Basu Ji Dadi Ba Suyi Hakuri - GandujeGwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya siffanta zaben jihar Kano a matsayin demokradiyya zalla.

Ya godewa dukkan magoya bayansa kan fitowa kwansu da kwarkwatarsu domin zabensa. Hakazalika yayi kira ga wadanda basu ji dadin sakamakon ba da su yi hakuri.

Yace: "Muna roko a kasance cikin zaman lafiya. Masu murna suyi murna cikin lumana domin gujewa barazana kuma wadanda basu ji dadi ba suyi hakuri."

"Amma abinda zan iya cewa shine wannan demokradiyya ce kuma muna bukatan juna. Na yi imanin cewa zamu kawo cigaba jihar Kano dubi ga irin ayyukan da mukayi."
"Ko shakka babu, idan ka samu nasara a zango na biyu, za kayi ne domin cigaban abubuwan da ka fara saboda kawowa jiha cigaba. Muna kira ga abokan hamayyarmu da mukayi takara tare su zo mu hada kai domin cigaban Kano."

An alanta Ganduje matsayin zakaran zabe a ranar Lahadi bayan ya samu jimillar kuri'u 1,033,695 inda ya zarcewa mai biye da shi, Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar PDP, wanda ya samu kuri'u 1,024,713.

Abba Kabir ya bayyana cewa jam'iyyarsa ta PDP bata amince da wannan sakamakon ba kuma zasu garzaya kotu domin kwato hakkinsu.

Yace: "Sakamakon zaben jihar Kano da INEC ta sanar da yammacin nan (Asabar) bamu amince da shi ba. Zamu hadu a kotu. "

Sunday, March 24, 2019

Zaben Kano: Manazarta Sun Ce Zaben Sahihi Ne, An Gudanar Da Shi Bisa Ka'ida
Yayin da ake gab da bayyana sakamakon zabe a Jihar Kano, alamomi na nunawa cewa Gwamna Dakta Abdullahi Umar Gabduje ne zai yi nasara. Domin sakamakon na nuna cewa yana gab da rangada Abba Kabir da kasa.

A makonni biyu da suka gabata, Abba Kabir na Jam'iyyar PDP ne ya zama zakara. To, amma a wannan karon, da alamu ba zai Kai labari ba.

Zaben da aka gudanar jiya na raba gardama, ya sami fitowar dimbin masu jefa kuri'a, musamman mata. Sai dai kuma, sabanin yadda a wancan karon kanawa suka yi yayin Abba Kabir.

A wannan karon kamar sun juya masa baya. Wannan yana fitowa fili ne yadda alkaluman ke nuna yadda suka yi zubargadar kuri'a ga Ganduje
Manazarta Siyasa na ganin cewa, zaben na jiya a Jihar Kano, yayi kama da abin da bahaushe ke cewa ta yaro kyau take bata karko


Wasu da muka zanta da su, sun zargi Sanata KWANKWASO da kokarin tada zaune tsaye a Jihar, da kuma ko ta halin kaka sai Abba Kabir surukinsa ya zama Gwamna. Wasu na fadin cewa sun ji dadi da kanawa suka hankalta,  suka sake tunani, suka zabi Ganduje.

"Abin da ya sa muka yanke shawarar mu zabi Ganduje, muna gudun abin da zai biyo baya Idan Abba ya zama Gwamna. Hakika sai yadda Kwankwaso ya juya shi.

Duk da cewa wasu majiyoyi sun ce 'Yan gani kashenin Kwankwasiyya ne suka soma tada kura a mazabu da yawa a jiya. Duk da haka, Jami'an tsaro ba su yi kasa a guiwa ba, wajen tabbatar da an gudanar da zabe mai sahihanci a Jihar Kano, ba tare da wata tashin-tashina ba.

Yanzu haka dai, kanawa sun kasa kunnuwansu kodayaushe daga yanzu domin jin an sanar da wanda suka zaba matsayin Gwamnan Kano

Wasu masu kishin Jihar Kano da muka zanta da su, sun yi Kira ga Sanata Rabi'u Kwankwaso da su rungumi kaddara idan har aka bada sanarwar zabe wanda ya saba da tunaninsu.

Saturday, March 23, 2019

Martani: Babu Wani Dalilin Da Zai Sa A Soke Zaben Kano Ba - Inji APC Rashen Kano
Jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta kalubalanci jam'iyyar PDP kan kiran da ta yiwa Hukumar Zabe na a soke zaben dake gudana a Kano a yau dinnan .

Shugaban jam'iyyar APC Abdullahi Abbas shi ne yayi kalubalen a taron manema labarai da jam'iyyar ta kirawo a nan Kano.

Abdullahi Abbas yace kamata yayi jam'iyyar PDP ta bari a kammala zaben kafin tayi korafi, inda yace suma a zaben da gabata basu korafi ba sai da aka kammala zaben.

Abdullahi Abbas yace bisa rahotannin da suka samu babu wani abu mai kama da zargin da PDP tayi na kada Kuri'a daga wadanda ba yan wuraren da aka sake zaben ba.

Shugaban jam'iyyar APC ya bukaci Al'ummar jihar nan dasu zauna Lafiya, kuma su jira sakamakon zaben da INEC zata bayyana.

Babu Wani Ɗan Daba Ko Ɗaya Da Ya Shigo Kano, Balle Har A Samu Tashin Hankali ---- In Ji DIG Antony MichealMuƙaddashin sufetan ƴan sanda na ƙasa DIG Antony Micheal Ogbizi, ya bayyana cewa jami’an tsaron ƴan sanda sun ɗauki matakan gaggawa wajen tabbatar da cewa komai ya tafi daidai a guraren da aka kusan samun tangarɗa a yayin gudanar da zaɓukan cike gurbi na jihar da a ke gudanarwa a yau Asabar.

Antony Micheal ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke  tattaunawarsa da manema labarai.

 “A mazaɓar gama da ke karamar hukumar Nassarawa an samu fitowar jama’a sosai kuma zabyen ya tafi lafiyar kalau."

Ya ƙara da cewa  a ƴan ƙalilan ɗin wasu guraren inda a ka samu ‘yar tunja-tunja, mun shiga tsakani, domin dawo da zaman lafiya.

Antony Micheay ya musanta zargin da ake na shigowar ƴan daba a rumfunan zaɓen da ke faɗin jihar Kano, da kuma cewa wai an kama wasu Kwamishinoni a lokacin zaɓen.

"Babu rahoton kawo ƴan daba a zaɓen ba. Mu na da isassun jami'an ƴan sanda. Jita-jitar cewa an kama wasu kwamishinoni ƙarya ce tsagwaronta.”

A ƙarshe ya ce kawo yanzu dai komai ya lafa, bayan da jami’an tsaro su ka hana bangarori biyun tayar da ƙayar baya a rumfunan zaɓen da ake da matsaloli watakila saboda ganin alamun faduwa.

Friday, March 22, 2019

Zaben Kano: An Zabi Dino Melaye A Matsayin Mai Sanya Idanu ( Observer)
Masu hikimar magana sun ce "gani ya kori ji". Wannan hotunan Sanatan Kogi ta tsakiya ne, Dino Melaye ya shigo Jihar Kano a matsayin mai sanya ido kan zaben cike gurbi da za a gudanar gobe Asabat, 23/3/2019.

Rahotannin da mu ka samu, ba wai Dino Melaye ne kadai zai zo Jihar Kano ba, har da wasu karin jiga-jigan jam'iyyar PDP matakin kasa inda za su zo domin marawa dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP baya.

Kenan wannan zai zama wata mahangar da za ta kore laifin duk wani kusa a jam'iyyar APC idan ya zo Jihar Kano domin kare martabar Gwamna Ganduje da jam'iyyar APC. Tunda su ma PDP mutanensu sun zo.

Wata Sabuwa: Ana Zargin Kwankwaso Da Daukar Nauyin Lika Hotunan BatanciAwanni kadan ya rage a yi walle-walle a Kano, tsakanin PDP mai kokawar sai ta kwace mulki, da kuma APC da ke tsayuwar dakan sai ta sha da kyar.

A dai dai lokacin ne wasu kanawa ke zargin Sanata Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso da daukar nauyin saka hotunan batanci ga Shugaba Buhari da wasu 'yan jam'iyyar APC.

Sauran  wadanda aka saka hotunan nasu, sun hada da Bola Tinibu, Nasir El-Rufa'i, da Adams Oshimole; wadanda a jikin hotunan na su aka rubuta maganganu na cin fuska.
Hotunan, wadanda aka like su a wasu muhimman wurare a birnin Kano, suna bayyana wadannan mutane a matsayin makiya Arewa, sannan an caccaki Muhammad Buhari da sunan maras godiyar Allah da butulci.

Haka nan kuma, an bi an yiwa fuskokinsu da jan fenti, aka rubuta "Mu Kanawa ba ma yin ku. An kuma rubuta a jikin babban hoton Buhari, ana cewa, " Da mun san haka za ka yi mana Buhari, da ba mu zabe ka ba"

A daren jiya ne wadansu wadanda wasu suka je dai-dai shataletalen Tal'udu, suna manna wadannan hotuna. Yayin da aka fafare su, suka ranta ana kare. Amma an yi sa'ar damke daya. Kuma tuni an yi lulaye da shi Abuja domin bin ba'asi.

 Wanda aka damke, shi ne ya tabbatarwa da Jami'an tsaro cewa abin da suke yi na like hotunan, aiki ne da Kwankwaso ya ba su

Mun yi kokarin jin ta bakin bangaren Kwankwasiyya. Amma har zuwa hada wannan labarin ba mu iya samunsu ba.

Thursday, March 21, 2019

(Zaben Kano) INEC Ta Fadi Guraren Da Za Ta Sake Gudanar Da Zabe


A ranar Asabar ne hukumar zabe (INEC) za ta sake yin zabe a wasu mazabu a Kano, bayan sanar da cewa ba kammala zaben jihar ba da aka gudanar a ranar 9 ga Maris.

Za a sake zabukan ne a rumfunar zabe 212 da ke kananan hukumomi 29 a fadin jihar, inda masu kada kuri'a 131,199 za su sake jefa kuri'unsu a akwatinan zabe 285.

Adadin rumfunar zabe a kananan hukumomin da za a sake zaben:

Albasu 5
Bebeji 1
Bichi 3
Bunkure 1
Dala 28
Danbatta 1
Dawakin Kudu 1
Doguwa 7
Gabasawa 4
Garin Malam 1
Gaya 6
Gezawa 1
Gwarzo 5
Karaye 7
Kibiya 11
Kura 5
Madobi 5
Makoda 1
Minjibir 8
Nasarawa 62
Rano 6
Rimin Gado 6
Rogo 4
Sumaila 3
Takai 10
Tofa 4
Tudun Wada 12
Warawa 2
Wudil 2
Siyasar Kano na ci gaba jan hankali, saboda girman hamayya tsakanin manyan jam'iyyun siyasa guda biyu APC da PDP da ke yakin lashe kujerar gwamna.

Fafatawar a zaben da za a sake a Kano ta shafi 'yan takarar manyan jam'iyyu biyu ne gwamna Ganduje na APC da kuma babban mai hamayya da shi Abba Kabir Yusuf na PDP.

Jam'iyyun biyu na bin dubaru na janyo ra'ayin jama'a don su zabe su.

Mallam Salihu Sagir Takai Yace A Zabi Ganduje A Zaben Ranar AsabarMai Girma dan takarar Gwamna na Jam'iyar PRP wato Mallam Salihu Sagir Takai ya umarci magoya bayan sa da su zabi Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR na Jam'iyar APC a zaben karashe na gwamna da zaa gudanar ranar asabar mai zuwa In Allah Ya kaimu.

Mallam Takai ya sanar da haka ne yayin da yake ganawa da magoya bayan sa a jiya. Ya shaida musu cewa Gwamna Ganduje ya nemi shi sun tattauna kuma sun cin ma masakahar cewa wannan shine zai zamanto alheri ga jihar Kano. Kuma ya kara da cewa akwai kyakyawar alaka mai karfi tsakanin sa da Ganduje.

Dan haka yake kira ga magoya bayan sa na Jam'iyar PRP da su fito kwansu da kwarkwata domin su kadawa Gwamna Ganduje kuri'un su a ranar asabar mai zuwa, 23 ga watan nan.
Mallam Takai ya samu kuri'u kimanin dubu dari wato 100,000 a zaben da aka yi a baya, kuma yawan kuri'un da zaa jefa a zabe mai zuwa adadin wadanda suke katin zabe a gurin ya kai kimanin dubu dari da arbain Sato 140,000.
Alhamdulillah.

Salihu Tanko Yakasai
Special Adviser Media
Government House Kano

Wednesday, March 20, 2019

Gwamnatin Kano Ta Rabawa Mata Masu Juna Biyu Tallafin Kayan Haihuwa A Mazabar GamaA yau ne 20/03/2019 Mai girma  mataimakin Gwamnan jihar Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilci Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR (Khadimul Islam) wajen bikin kaddamar da bada tallafin kayan haihuwa (Delivery Kits) ga mata masu juna biyu su guda dubu biyu (2,000) wanda aka gabatar a asibitin da ake kira asibitin Bitinariya dake unguwar Gama cikin karamar hukumar Nassarawa Kano.

Matan da suka amfana da wannan tallafin sun nuna farin cikinsu, tare da yin godiya ga maigirma gwamna, tare da mataimakinsa, sannan sun nuna zabe mai zuwa zasu fito domin zabar maigirma Gwamna tare da mataimakinsa.

Taron bada tallafin wanda ya gudanar a mazabar gama dake karamar hukumar nasarawa, ya samu halartar Manyan Mutane, Malamai da 'Yan Siyasa, daga ciki akwai Sanatan Kano ta Arewa Hon. Jibril Maliya. Da Kwamishinan Lafiya. dade Sauransu.


Ayau Laraba 20/03/2019.
Dab'i📸✍🏾:-- *Abbakar DK*
S.A na Mataimakin Gwamnan Kano.

Ƙungiyar Lauyoyi Ta Baiwa Kwamishinan Ƴan Sanda Na Jihar Kano Wa'adin Kwanaki BiyuƘungiyar lauyoyi ta ƙasa reshen jihar Kano ta bukaci kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano CP Wakili Muhmmad, da ya ba ta haƙuri nan da sa'oi 48 bisa cin zarafin da wasu yan sanda suka yiwa mambobinta yayin da suke gudanar da aikinsu.

Kungiyar cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun sakatarenta, Mujtaba Adamu Ameen tayi tur da matakin rundunar yan sandan na tsare lauyoyin a lokacin da suke tsaka da nazartar sakamakon zaɓen da hukumar zaɓe ta ƙasa ta amince da shi.

Ƙungiyar ta yi kira ga kwamishinan yan sanda da ya tsame kansa daga harkokin siyasa ta la'akari da yadda take bayyana cewa yana ketare doka wajen aiwatar da ayyukansa.

A ranar talatar data gabata ne dai wasu yan sanda su kusan 30 cikin motoci kirar Hilux suka yi dirar mikiya a sakatariyar kungiyar lauyoyin dake jihar Kano inda suka yi awon gaba da lauyoyin dake tsaka da aiki zuwa shelkwatar rundunar dake Bompai domin tsare su.

Atiku ya tanadi fiye da shaidu 400 domin kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasaA yayin ci gaba da kalubalantar sakamakon zabe, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu, ya shirya gabatar da shaidu fiye da 400 wajen shigar da korafin sa a gaban Kuliya.

Jam'iyyar PDP da dan takarar ta na kujerar shugaban kasa a babban zabe da ya gudana makonni uku da su ka gabata, sun tanadi tarin shaidu domin kalubalantar sakamakon zaben a gaban kotun daukaka kara.

Majiyarmu ta rawaito cewa, Atiku da jam'iyyar sa ta PDP na ci gaba da yin zaman dirshan kan kujerar naki ta kin amincewa da sakamakon zaben shugaban da hukumar INEC ta tabbatar da nasarar dan takara na jam'iyyar APC, shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A ranar litinin ne a cikin farfajiyar kotun daukaka kara da ke garin Abuja, Atiku da jam'iyyar PDP sun bayyana shirin su na daukar mataki domin kalubalantar sakamakon zabe da sanadin babban Lauya, Mista Emmanuel Inoidem, mashawarcin su akan harkokin shari'a.

Majiyarmu ta ruwaito cewa, Lauya Enoidem ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai bayan da jam'iyyar PDP ta kammala shigar da korafin ta a gaban kotun daukaka kara da a Yammacin na ranar Litinin.

Enoidem ya yi tuni da cewa, manyan lauyoyi fiye da ashirin za su jagoranci wakilcin shigar da korafi domin kalubalantar sakamakon zabe a madadin Atiku da jam'iyyar PDP.

A yayin da a Jiya Talata bayan kwanaki 21 da bayyana sakamakon zaben shugaban kasa, jam'iyyar PDP ta cika sharuddan shigar da korafi na kalubalantar sakamakon zabe bisa ga tanadi da kuma shimfidar dokoki na shari'a.

Ba ya ga rashin bai wa jam'iyyar PDP dama ta bincikar kayayyakin zabe kamar yadda umurnin kotu ya yi tanadi, kwarewa da sanin makamar aiki ya sanya jam'iyyar PDP ta kammala shigar da korafin ta duk da rashin samun hadin kai daga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC.

Tuesday, March 19, 2019

Jam'iyyar APC Ta Kori Tsohon Shugaban TETFUND Dr. Baffa Bichi.

Jam'iyyar APC ta mazabar Bichi karkashin shugabancinta ta kori tsohon shugaban hukumar TETFUND Dr. Abdullahi Baffa Bichi daga Jam'iyyar APC a yau talata 19/03/2019

Jam'iyyar Tayi ta kori shine Saboda Dimbun laifuka da yake ta aikatawa Jam'iyyar  APC Tun daga matakin mazaba har kasa baki daya

Jim kadan da wannan zama itama uwar  Jam'iyyar APC ta karamar hukumar Bichi ta kori Dr. Abdullahi Baffa daga Jam'iyyar APC kuma ta Amince da matakin da Jam'iyyar APC ta dauka ta mazaba na korarsa daga Jam'iyyar.

A nasa jawabin Shugaban Jam'iyyar APC na karamar hukumar Bichi Hon. Abdullahi Magaji Lamba yace " tun tuni ya kamata a kore shi Saboda irin Abin da yake yiwa Jam'iyyar,
"Baya Taimakonta, baya so a taimake ta yana fada da masu taimakon Jam'iyyar APC Har takai yana yi mata zagon kasa, yanzu dai Baffa ba Dan Jam'iyyar  APC Bane." a cewar sa.

Daga Al-kassim Musa Bichi

Gwamnatin Kano Za Ta Dauki Mataki Ga Masu Tada Hankalin Jama'ahGwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi gargadin cewa a matsayinsa na lamba daya a jihar Kano, gwamnatinsa ba za ta tsaya ta na kallon duk wani wanda yake son tayar da hankalin jama'a ba, ta ma kowace irin siga ne.

Ya ce "A matsayi na na gwamnan Kano ba zan iya bacci ba muddin jinin mutum daya ma ya zuba a wannan gari namu mai albarka na Kano."

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne a lokacin da wasu kungiyoyi sama da 300 su ka kai masa ziyarar yabawa da yadda yake kokarin samar da zaman lafiya a jihar Kanon. Sun je wajen nasa ne karkashin inuwar Jakadun Zaman Lafiya, wato 'Kano Peace Ambassadors.'

Su wadannan dimbin jama'ar da sun kai sama da su dubu goma sun yi tattaki ne daga fadar Sarkin Kano zuwa fadar Gidan Gwamnati, su na sowa su na cashewa su na ta fadin cewa "Mu zaman lafiya kawai muke nema a Kano! Ba mu yarda da kokarin da wasu ke yi na tayar da hankulan jama'a ba!

Gwamnan ya ci gaba da cewa "Duk wani wanda yake son tayar da hankalin jama'a, ya kamata ya tabbatar da cewa gwamnati ba za ta bar shi ya tafi haka a banza ba. Dole ya kamata kowa ya san da cewa akwai gwamnati fa."

Ya ce jihar Kano jiha ce da take da zaman lafiya. Kuma dole ne cikin taimakon Allah ta ci gaba da zama jihar zaman lafiya da lumana. Ya ce "Ya zama wajibi ga kowa da ya bayar da ta sa gudummawar ta samuwar tabbatataccen zaman lafiya a wannan jiha ta mu."

Daga cikin wadanda su ka jagoranci wannan tafiya akwai irinsu Abubakar Muhammad Janaral, da kuma shugaban Kungiyar Daliban Jihar Kano na Kasa, Aliyu Maikasuwa Rano da kuma shugaban Majalisar Matasa Na Kasa reshen jihar Kano, Kabiru Ado Lakwaya, da sauransu.

Dukkansu wadannan da ma wasu da su ka yi magana a gaban gwamna Ganduje, sun yabawa gwamnan wajen yadda yake kokarin ganin jihar Kano ta dore da zaman lafiya.

Kuma su ka yi watsi da wasu kalaman tayar da hankula da wasu shugabannin siyasa da kuma wasu shugabannin al'umma ke yi saboda tunzura jama'a, kamar yadda su ka ce.

Anwar shine Babban Sakataren Yada Labarai Na Gwamnan Kano.

Daga Abba Anwar

2023: Ana Ayyana Osinbajo Da El-Rufa’i A Matsayin ‘Yan Takarar Shugabancin KasaA kafafen soshiyal Midiya musamman bangaren Jihar Kaduna suna danganta Matemakin Shugaban kasa Yemi Osibanjo da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El’rufai, a matsayin Yan takarar Shugaban kasa a zabukan 2023 dake tafe nan da shekaru hudu Masu zuwa.

Yadda masu hasashen ke ayyanawa suna bayyana Yemi Osibanjo a matsayin Shugaban kasa Malam Nasiru Elrufai kuma a matsayin matemakin shugaban kasa.

Rai da buri yaushe aka kammala zabukan bana bare har a fara batun zabukan shekarar 2023 dake tafe?

Dama chan wata majiyar data bukaci a sakaya sunanta ta bayyana cewar akwai wata kullalliyar yarjejeniya a tsakanin Shugaban kasa Muhammad Buhari, da yankin Yarabawa, kan basu damar fitar da Dan takara daga yankin Yarbawa a zabukan 2023, wasu ma har suka ce Bola Ahmed Tinubu ne dan takarar a karkashin Inuwar Jam’iyyar APC.

To sai dai a wani bangaren ana ta shan alwashi daga bangaren Arewaci kan cewa daga yanzu zuwa zabukan 2023 dake tafe Jam’iyyar APC bata da sauran Gurbi a Najeriya dama chan Jam’iyyar Buhari ce zai kuma tsallaka da kayar sa Daura.

Anya Najeriya zasu yadda da Osibanjo da El’rufai a matsayin shugabanni a zabukan 2023 a karkashin inuwar Jam’iyyar APC?

Daga Jamilu Daya-malam Gama 

Monday, March 18, 2019

Al'ummar Mazabar Gama Sun Gayyaci Ganduje Don Jaddada Goyon Bayansu
Al'ummar mazabar Gama, daya daga mazabun da za a sake zaben gwamna ranar Asabar 23 ga Watan Maris sun gayyaci gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da ya je su nuna jaddada goyon bayansu, a zaben mai zuwa.

Jama'a dubunnai ne suka tare shi tun daga Bompai har zuwa Kwanar Tudunwada zuwa Gama A da Gama B da Gama C da Gama D da Gama Tudu da Gama Fulani da kuma Gama Barebari.

Saboda dimbin jama'ar da su ka tari gwamnan a mazabar ta Gama sai da gwamnan ya debi misalin awanni hudu ya na kewaya mazabar.

Gwamnan ya yi musu godiya saboda zaben da su ka fito su ka yi wa shugaba Muhammadu Buhari a karo na biyu. Tare da gode musu wajen fitowa da su ka yi lokacin zaben gwamna da a ka yi wanda ba a kammala ba.

Ya ce "Mu na yi muku godiya saboda namijin kokarin da kuke yi wajen zabenmu. Sanin kan ku ne cewa lokacin zaben gwamna da na 'yan majalisar jiha, 'yan jam'iyyar adawa ta PDP sun yi aringizon kuri'u tare da tafka magudi.

Wanda hakan ne ya sa hukumar zabe ta kasa ta soke zabubbukan wasu wurare wanda za a yi a wannan Asabar din mai zuwa."

Ya yi kira gare su da su fito kwansu da kwarkwatarsu su sake jefa masa kuri'a saboda ya ci gaba da yi musu ayyukan raya kasa da kuma tallafawa rayuwar al'umma.

Lokacin da dandazon samarin mazabar ta Gama su ka nemi Gwamnan da ya yi wani zuwa na musamman kafin zaben ranar Asabar din, saboda ganawa da kungiyoyin kwallon kafa da na wasanni daban daban da ke wannan katafariyar mazaba.

Sai gwamnan ya tabbatar musu da cewa zai kara komawa ranar Alhamis saboda a rabawa wadannan samari kayan wasanni na kulob-kulob din su a wannan mazaba da makwotansu.

Danzazon jama'ar wannan mazabar sun kara da cewa su na bukatar gwamna Gandujen ya ci gaba da zuwa wannan mazaba ta su, daga yau Litinin har zuwa Alhamis lokacin da za a rufe yin kamfen na cikon zaben gwamna a jihar Kano din.

A daidai lokacin da gwamna ke wa jama'a jawabin muhimmancin ayyukan raya al'umma wanda a ke kwarara musu ayyukan tituna da rijiyoyin burtsatse sai kawai jama'a suka cashe da sowa da murnar zuwan nasa wannan mazaba.

Jama'ar mazabar Gama da ma makwabtanta sun yi dafifi sun kara tabbatarwa da gwamna cewar suna tabbatar masa da kuri'unsu ba tare da wata wahala ba da taimakon Allah. Sun gaya masa kar ma ya yi wani dar kan maganar wannan zaben da za a karasa.

Gwamnan ya samu rakiyar mataimakinsa Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas da kwamishinoni da masu ba gwamna shawara da kuma dattawan jam'iyya.

Anwar shine Babban Sakataren Yada Labarai Na Gwamnan Kano

Daga Abba Anwar

KANO TAFI KARFIN DAN KOYO, SAI KWARARREN DIREBA - Inji Haji ShehuTa inda zaka gane cewar gwamna Ganduje ya gagari masu bakar adawa shine, har yau babu wani dan adawa da ya fito yace rashin aikin gwamna Ganduje ne yasa suke adawa da shi.

Duk aikin da yakamata gwamna ya aiwatar a jahar sa, gwamnatin gwamna Ganduje tana aiwatar wa. Izuwa yanzu Babu gwamnan da yakai gwamna Ganduje aiki duk gwamnonin jihohin Ƙasar nan.

Masu adawa da gwamnatin Ganduje suna yi ne saboda iyayen gidan su bawai don cigaban jahar Kano ba, duk mai son cigaban jahar Kano yasan gwamnatin Ganduje tana gina jahar Kano kuma ba zai so karbar sitiyarin gwamnatin jihar Kano daga hannun gwanin Tuki zuwa hannun Dan - koyo ba

Jita-Jita: Gwamnatin Kano Bata Yiwa Masarautar Kano Barazana Ba.Gwamnatin jihar Kano,  ta nesanta kanta dangane wani labari da wata kafar yada labarai  a Facebook take yadawa cewa Idan Allah yasa Maigirma Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje,  ya ci Mulki to zai tsige Maimartaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II.

Mataimaki na musamman a kan kafafan yada labarai ga Mai girma Gwamna Alhaji Salihu Tanko Yakasai ya bayyanawa manema labarai cewa Wannan shipchin jizone ake yadawa dan wasa hankulan jama'ar jihar Kano masu daraja.

Haba "Idan mafadin Magana wawane ai majiyinta bazai zama wawaba" Gwamnatin jihar Kano tana da kyakkyawar alaka da Masarautar Kano. In ji SA

Inda ya ci gaba da cewa, Sabo da haka Mai Martaba Sarki Jagorane, Kuma Mai Ilimine, sannan Ubane shi ga kowa, Kuma shi badan siyasa bane.

A duk Najeriya Babu jihar data more jarumin Sarki Mai tausayi da jikan talakawansa Kamar Kano.

Allah ya ja da ran Sarki!

Daga Ali Adamu Jauro 

((HOTUNA)) GWAMNA GANDUJE YA KAI ZIYARAR AIKI A MAZABAR GAMA

Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR yakai Ziyarar duba aikin Titi a Unguwar Gama wanda Gwamnatinsa ke Gabatarwa. Yau,Litinin. 18/3/2019
Dandazon dubunnan al,ummar maza6ar Gama kenan rankata-kaf har da mai martaba Maigarin Gama Rabi'u Isyaku* duk daga kwanar Tudun Wada domin tarar Mai girma Gwamnan Kano *Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR* da mataimakinsa *Dr. Nasiru Yusuf Gawuna* don zuwa duba aikin sabon titin da Gwamnatin Kanon ta gabatar acikin satin nan tare da gaisar da sauran al,ummar 6angaren.
Yau Litinin 18/03/2019.

📸📝:-- *Abbakar DK*
S.A na Mataimakin Gwamnan Kano.
Aikin Duba Idanu Da Bada Magunguna Kyauta Daga Gwamna GandujeAna cigaba da duba lafiyar masu larurar idanu a asibitin Filin Kaya dake maza6ar Gama cikin karamar hukumar Nassarawa tare da bawa masu larurar magunguna kyauta sannan wadanda idanunsu suke bukatar sai anyi musu aiki suma nan take ake yi musu akuma basu magunguna wasu a hada musu da gilasan ido don suke sawa agida wadda Gwamnatin jihar Kano ta Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR (Khadimul-Islam) tasa a gabatar daga yau zuwa gobe, don haka duk mai larurar ido yai maza ya garzaya asibitin don duba lafiyar nasa idanun.


Ana duba masu larurorin ido kamar na juyewar gashin gira dake komawa cikin ido (Trichiasis) da larurar yanar ido (Cataract) d.s.s.
Dab'i :--

 Abbakar DK
S.A na Mataimakin Gwamnan Kano.

Masu Garkuwa Da Alaramma Ahmad Sulaiman Sun Bukaci Da A Basu Miliyan 300


Shugaban kunguyar izalar Najeriya Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce Mutanan da Sukayi Garkuwa da Alaramma Ahamad Sulaiman Sun Nemi Abasu kudi har Naira miliyan dari uku 300 kafin Su Sake Shi.

Wani na kusa da wannan Malamin, mai suna Ismail Bunyaminu ya bayyanawa ‘yan jarida cewa wadanan Miyagu sun sa masu kudi har Naira Miliyan 300 kafin su sake Malan

A Yanzu dai za.ayi kokarin hada kudin domin ceto Rayuwar Malan daga hannun Masu garkuwa da mutane

 Ismail Bunyaminu yace Iyalin Malan sun zauna game da lamarin inda suke neman wadannan mutanan da su rage kudin da su ka sa ka Domin Asamu A tattara kudin daga shugabannin kungiyar Izala da kuma gwamnatin jihar Kano.

Saidai su Jami’an tsaro a na su bangare, sun ce ba su san da batun biyan kudi ba, amma sun yi alwashin ceto Rayuwar Malan.

Mudai Munanan Muna Addu a Akan Ubangiji Allah yakubutar da Malan daga hannun Azzalumai.

GANDUJE YA BADA UMARNIN DAGA DARAJAR SHUGABANNIN MAKARANTU
Domin samar da guraben ci gaba ga malaman makarantu, Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ba da umarnin daga darajar shugabannin tsofaffin makarantun sakandire  [principals] zuwa Daraktoci abinda ya haifar da cigaban wasu shugabannin makarantu 67 zuwa Daraktoci.

Wannan mataki da gwamnatin ta dauka ya karfafa gwuiwar Malaman Makarantu kwarai da gaske.

Abisa wannan dalili ne muke sake jawo hankalin al’ummar Jihar Kano da su yiwa kansu karatun ta nutsu, musamman wuraren da za gudanar da zaben raba-gardama da su fito fitar dango su sake kadawa Abdullahi Umar Ganduje kuri’unsu domin tsamar da Jami’an Ilmi daga halin kaka-ni-kayi da ake neman jefa su ciki ranar 23 ga watan Maris, 2019.


Ya ku jama’ar Jihar Kano, ku ceci ‘ya’yanku da zuriyarku mai zuwa daga gwamnatin ‘yan gangan, gwamnatin ‘yan kyashi da hassada domin ci gaban Jihar Kano da alummarta.

Ku zabi Abdullahi Umar Ganduje, Ganduje na Kowa, Dattijon Kanawa.

Daga Abdulaziz Tijjani

Sunday, March 17, 2019

APC Ta Zargi CP Wakili DA Taimakawa PDP Wajen Yin Magudi A Zaben KanoJam'iyyar APC mai mulki ta zargi Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Muhammad Wakili da hannu dumu-dumu wurin taimakawa jam'iyyar PDP tafka mugudin zabe a zaben gwamna na jihar Kano.

Sakataren jam'iyyar na kasa, Malam Lanre Issa-Onilu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi inda ya ce kwamishinan 'yan sandan ya janye masu tsaron kwamishinan jihar Kano kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Yace "Ba boyeyen abu bane yadda kwamishinan 'yan sandan jihar Kano yana da hannu wurin taimakawa jam'iyyar PDP yin magudin zabe a cikin birnin Kano ta hanyar baiwa magoya bayan Kwankwaso kariya yayin da ya janye masu tsaron kwamishinan jihar Kano," inji shi.

"Nasororin da da jam'iyyar APC ta samu karkashin gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje sun isa su bashi nasarar a zaben da za a maimaita.

"Kuma za a maimaita zaben ne a kauyukan da jam'iyyar APC ta ke da magoya baya sosai da karamar hukumar Nasarawa inda mataimakin Gwamna Nasiru Yusuf Gawuna ya fito. Babu shakka, jihar Kano tana daya daga cikin jihohin da APC ke da karfi kuma har yanzu mu ke da jihar," inji Issa-Onilu.


Ana dai ganin Wakili shine jarumin babban zaben 2019 saboda 'yan sanda karkashin jagorancinsa sun kama mataimakin gwamnan jihar Kano, Dr Nasiru Gawuna da Kwamishinan Kananan hukumomi, Alhaji Murtala Sule Garo da shugaban karamar hukumar Nasarawa, Alhaji Lamin Sani da aka ce wai ya yaga sakamakon zabe a lokacin da ake kidiya kuri'un na karamar hukumar Nasarawa.

Shugaba Buhari Ya Koka Kan Yadda Ake Siyasantar Da Komai A Kasar Nan


A jiya, Asabar, ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari tare da kasha mutane 10 a garin Nandu-Gbok dake karamar hukumar Sanga mai iya da jihohin Nasarawa da Filato a jihar Kaduna.

Dakta Hadiza Balarabe, sabuwar mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna; Malam Nasir El-Rufa’i, ‘yar asalin karamar hukumar Sanga ce.

An kona gidaje fiye da 30 a harin kamar yadda dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kaduna a jam’iyyar PDP da mai wakiltar yankin a majalisar wakilai ta suka tabbatar.

Samuel Aruwan, babban mai taimakawa gwamnan jihar Kaduna a bangaren yada labarai, ya tabbatar da kai harin a cikin wani jawabi da ya fitar domin mika sakon jajen gwamnati ga jama’ar yankin da harin ya shafa ko ya ritsa da ‘yan uwansu.


“Lamarin kai hare-hare da kisan rai da zubar da jinni na matukar damu na, na kasa fahimtar yadda wasu mutane ke kisa haka kurum ba tare da la’akari da girma ko muhimmanci ‘rai’ ba ,” a cewar shugaba Buhari ta bakin babban mai taimaka ma sa bangaren sadarwa da yada labarai.

Sannan ya cigaba da cewa; “babu wani shugaba mai kishin jama’ar sa da zai kwanta cikin farinciki yayin ‘yan kasar sa ke kasha kan su saboda banbancin kabila ko kuma addini.”

“Matukar babu wani bangare da zai iya hakuri a kan banbancin dake tsakaninsa da abokan zamansa, ba za a daina samun irin wadannan kai hare-hare ba .”

Shugaba Buhari ya kara da cewa gwamnati na cigaba da neman hanyar da zata bi don kawo karshen wannan matsalar tare da yin kari da cewar, “wadanda matsalolin suka shafa basa bawa kokarin gwamnati hadin kai ta hanyar siyasantar da duk yunkuri da gwamnati ta yi domin kawo karshen matsalar.”

“An siyasantar da komai a Najeriya, hatta kokarin gwamnati na tabbatar da adalci a tsakanin jama’ar kasa .”

ASIRIN MAKUSANTAN GANDUJE DA SUKE CIN AMANARSA YA FARA TONUWABabbar matsalar da Ganduje ya fuskanta itace rashin tantance masoya na hakika, ya amince da wani munafuki wanda yazo yake ingiza shi yana ma shi dadin baki, sannan daga gefe yana recording din shi domin ya tozarta shi daga baya.


Na sani anyi ba daidai ba, amma na so ace mutanen Kano zasu auna Ganduje a sikelin adalci, shin da ayyukan raya al-ummah da yayi a Kano da sharrin da yayi wanne yafi yawa? Kar mu mance cewa dukkan mu a wannan tsarin muke burin Allah ya auna mu, to me zai sa mu gaza auna kawunan mu a hakan?

Bai kamata mu biyewa yan siyasa su rika yaudarar mu ba. Mutane da su ma tabbas dukiyar da ke aljihun su ba gadonta suka yi ba, hasali ma da chan duk tare da shi suke karbar rashawar, sannan tabbas mun san su ne suka kitsa mashi munafurcin domin su kaskantar da shi a idanun mu, yau ache sune zasu rika yi mana wa'azi wai Ganduje ya saci dukiya? Su tasu dukiyar ina suka samo ta?

Kowa na da damar zabin abunda ya ga ya dace da shi, amma ba daidai ba ne mu biyewa mutane su rika bakanta wani domin muradun su na siyasa.

 Daga Sharif Almuhajir

Saturday, March 16, 2019

CP Muhammad Wakili Ya Kaiwa Shugaban Izala Na Jahar Kano Ziyara Domin GirmamawaA yau Asabar, 16-3-2019 ne, Kwamishinan ÿan Sanda na Jihar Kano Muhammad wakili ya kai ziyarar ga shugaban Kungiyar Izala na jihar Kano, Dr. Abdullahi Saleh Pakistan.

CP wakili, ya kai wannan ziyara ne domin girmamawa da kuma samun kwarin gwiwa a ayyukan da yake gabatarwa a wannan jiha tamu mai albarka.

A yayin ziyayar, Dr. Abdullahi Saleh Pakistan ne ya fara gabatar da jawabai na nasiha da jan hankali ga Cp wakili akan ya rike aikinsa hannu biyu-biyu, kuma yasan cewa Allah zai tambayeshi akan dukkan abinda ya gabatar.

" ka sani cewar dukkan aikin da mutum yakeyi, zai iya wakiltar musulunci a wajen, kayi iyaka kokarinka wajen kare musulinci da aikin da kakeyi. Kuma kayi Adalci a aikinka, domin Allah zai tsayar dakai yayi maka hisabi a kiyama...''
- Inji Dr. Pakistan

Dr. Abdulmudallib Muhammad, shima ya dora da nasiha ga CP wakilin, duk dai don fita hakkin shari'a akansa.Shima a nasa bangaren, Cp Wakili yace yaji dadin nasihun da malaman suka gabatar masa, inda yace, dama yana bukatar nasiha domin ya samu kwarin gwiwa a inda yake yin daidai, ya kuma gyara inda yake da kusakurai.

''Ni bana siyasa, bani da Jam'iyya, kuma bazan siyar da lahirata akan duniyata ba, balle na siyar da lahirata akan duniyar wani, kunga babbar asara kenan...''
- Inji CP Waliki.


CP wakili ya bukaci malaman Kungiyar Izala, su tayashi addu'a domin dacewa a aikinsa, sannan ya bukaci a koyaushe idan yayi kuskure to a gyara masa.

"in nayi abinda ba daidai ba, ku kirani a waya ku gyara min, ko ku aika min da sako, ko kuzo, ko ku aiko ni nazo" Inji Wakili.

A karshe, Dr. Pakistan ya gabatar da kyautar Alqur'ani mai girma, da littattafai na addinin musulunci da Kwamishinan ÿan sandan na Kano.

A madadin Jagororin kungiyar Izala a matakin jiha, muna fatan alkhairi ga kwamishina, kuma muna rokon Allah ya bashi ikon yin adalci tsakanin al'umma.
Awaisu Al'arabee Fagge.

Director, JSM Kano State.

Arzikin Shugaban Kasa Buhari Ya Ragu Daga Yadda Yake A 2015 - Inji Osinbajo


A daren ranar Alhamis 14 ga watan Maris ne mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce arzikin shugaban kasa Buhari ya ragu idan aka kwatanta da abinda ya mallaka a 2015.

The Nation ta ruwaito cewa mataimakin shugban kasar ya yi wannan furucin ne a wurin wata liyafar cin abinci da aka shirya a fadar Aso Villa domin karrama wadanda suka taimaka wa jam'iyyar APC neman kuri'u lokacin yakin neman zaben 2019.

Ya ce: "Na duba takardar bayyana kadarori na shugaban kasa a shekarar 2015 inda na gano na fi shi arziki kuma na ce masa, "Shugaban kasa, Na fi ka arziki sosai, wannan abin kunya ne."
"Sai ya amsa da cewa, "Ni fa soja ne, kai kuma babban lauya ne saboda haka ya dace ka fi ni arziki."

"Maganar gaskiya shine arzikinsa sun ragu akan yadda na gani a 2015 a yayin da na sake ganin takardan bayyana kadarorinsa."inji Osinbajo


A yayin da ya ke tsokaci a kan zabukan da za a maimaita a wasu jihohi shida a ranar 23 ga watan Maris, Osinbajo ya bukaci 'yan Najeriya su zabi jam'iyyar APC.

"Har yanzu ba mu kammala zabe ba.
"A ranar 23 ga watan Maris akwai zaben da za muyi a wasu jihohi shida kuma muna da 'yan takara.
"Ba zai yiwa mu nade hannu mu ce mun gama aiki ba, har yanzu akwai sauran aiki," a cewar Osinbajo

Zaben Kano Babu Wani Inconclusive Karyace Kawai - Inji Sheikh Abduljabbar Nasiru KabaraShehin Malamin Yayi Kira Ga Shugabanni Kamar Haka Inda Yace...Ina Kira ga Baba Buhari Kayiwa Allah Ka Dubi Kanawan Dabo Kasa Baki A Wanan Lamari dake neman Har gitsa kano kaja Ganduje Ajikinka ka Bashi Wata Kujerar ya Hakura da Wannan Dan Samun Zaman lafiyar Al'ummarmu....

Ina Kira ga Mai Girma Gwamanan Kano Kayiwa Allah Ka Rungumi kaddara Sai Allah Ubangiji Yayima Sakayya da Abinda yafi kujerar Gwamna...

Ina Kira ga Sanata Rabi'u Kwankwaso Kuyiwa Allah karku binciki Abunda Wannan Gwamanati tayi Kodan Samun Kwanciyar Hankali Al'ummarmu...


Manyan Kano kuyiwa Allah Ku Zauna da Mutanan ayi yarjejeniya dasu Wanda Yaci Zaben Nan A Bashi Amma ayita da Wajewa Kar ya binciki Abunda ya Wuce Mutane aiki kawai suke so ba fitina ba Amma Wani Inconclusive duk karyace:--dr Abduljabbar Kabara.

Madogara Kwankwasiyya Reporters:Kwankwaso Ya Kafa Kwamitin Gano Filayen Da Za a Kwacewa Talakawa Idan Abba Ya Hau MulkiAllah wadai da wannan mummunan tanadi da Kwankwaso yakewa mutanen Kano, wai tunanin PDP Kwankwasiyya zata sake dawowa kan kujerar gwamnatin jihar Kano.

Dan kuwa labarin sirri da yake samunmu yanzun nan ance jiya Jumaa da daddare ne ya kafa wani kwamitin da zai bi wurare a cikin Kano domin gano ko me aka yi da filayen da ya kwacewa mutane, wanda zuwan gwamna Abdullahi Ganduje ya mayarwa mutane da mallakar filayensu.

Ance Kwankwason yana ta zage zage jiya har yana cewa duk shegen da yake da hannu wajen dawowa da jamaa filayensu zai masa mummunar illa idan Abba Gida Gida ya samu cin zaben gwamnan Kano a zaben cike gurbi da za a yi ranar Asabar mai zuwa.

Kwamitin karkashin shugabancin Baba Umar yaba shi wa'adin kwanaki hudu da yazo masa da cikakken rahoto kan filayen da aka mayar da gine-ginensu da kuma filayen da har kawo yanzu masu mallajar filayen basu samu damar ginewa ba.

Jiya an ga yan kwamitin a sukwane tsakar dare suna bin titin daya tashi daga Kabuga zuwa titin Kofar Ruwa suna ta aune-aune da wasu injiniyoyi marasa kishin jamaa. Har ma labarin namu ya gano yadda shugaban kwamitin Baba Umar ya bugawa Kwankwaso waya da tsakar daren yake gayawa madugun nasu yadda jamaa suka dawo da gine-ginensu.


Sannan an ga wadannan yan kwamitin a wasu bangarorin cikin birnin Kano daga can bangaren Mariri Hotoro da wajejen su Tishama, suna duba ko akwai yiwuwar su kara gano wasu filayen ko gidajen da gwamnatinsu idan wai sun ci zasu kwacewa mutane da sunan wai zaa yi wasu ayyukan jamaa.

Allah Ya raba mu da wannan mugun mutum, Allah Ya saka mana kan wadancan filayen daya kwacewa mutane haka kawai. Wanda hakan ne ya jawo mutuwar wasu bayin Allah ba gaira ba dalili. Saboda sun samu ciwon hawan jini nan take.

Kar Allah ya ba Kwankwaso damar samun mulkin Kano, amin summa amin.

@Zainab Abdul Fika Muhd.
16/03/2019

Friday, March 15, 2019

GASKIYA TA FARA FITOWA KAN YADDA ZABEN JIHAR KANO YA KASANCE


Kwamishinan kananan hukumomin jihar Kano, Alhaji Murtala Sulen Garo ya musanta zargin da ake masa na sa hannu cikin tayar da hankali a ofishin hukumar INEC ta karamar hukumar Nassarawa tare da mataimakin gwamna Nasiru Yusuf Gawuna da har ta kai ga sun yaga sakamakon zaben gwamna na karamar hukumar, Murtala ya bayyana haka ne a jiya Alhamis, 14 ga watan Maris a lokacin da yake ganawa da 'yan jaridu a ofishinsa, inda ya ambaci sunan tsofaffin 'yan majalisar wakilai, Farouk Lawan da Nasiru Sule Garo a matsayin wadanda suka kekketa sakamakon zaben mazabar Gama.


Sai dai a jawabinsa, Garo ya fadi yadda aka yi komai kuma ya ce jam'iyyar PDP ita ce ta shirya labarin kanzon kurege, inda yace magoya bayan PDP ne suka rirrikeshi da nufin hanashi shiga ofishin hukumar INEC, a dalilin haka ne suka kekketa masa riga.

Kuma ya kara da cewar shi da Gawuna sun isa ofishin ne a lokacin da suka samu labarin Farouk Lawan da Nasiru sun isa ofishin lokacin da ake tattara alkalumman sakamakon zabe da nufin tayar da hankali, har ma suka kekketa sakamakon zaben ba tare da wani yace musu uffan ba, hatta 'yan sanda basu yi musu komai ba. A karshe Murtala ya ce ba mu da cikakken yakini game da kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, saboda yana goyon bayan ta'adin da PDP ke shiryawa a jihar Kano, baya mana adalci.

Popular Posts