Thursday, February 28, 2019

Obasanjo Ya Gudu Zuwa Kasar Ingila Jim Kadan Da Cin Zaben BuhariJim kadan bayan da hukumar zabe me zaman kanta ta sanar da nasarar shugaban kasa, Muhammadu Buhari a zaben Ranar Asabar din da ta gabata, sai gashi an hango tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo yana sauri-sauri ya fice daga Najeriya zuwa kasar Ingila.

Wani dan Najeriyar mazaunin kasar ta Ingila ya bayyana cewa ya ga Obasanjon acan kuma har suka dauki hoto, ya kuma tambayeshi me yasa baya son shugaba Buhari? Sai Obasanjon be kalle shi ba, ya kawar da kai kawai.

Obasanjo dai ya goyawa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP,Atiku Abubakar baya ne.
Sannan kafin zaben shugaban kasa,Muhammadu Buhari yayi alkawarin bincikar kudin gyaran wutar lantarkin Najeriya da akace an kashe dala Biliyan 16 a lokacin mulkin Obasanjon.

Ya Fatattaki 'Yan Gudun Hijira Daga Gidajensa Don Kawai Sun Zabi Buhari


Wanda ke takaran gwamna a jihar Zamfara a karkashin jam'iyar APGA, Sani Shinkafi ya kori 'yan gudun hijira da ya ajiye a gidajensa da ke karamar hukumar Shinkafi domin sun zabi Buhari. Dan siyasan dama tun can ya dauke wadan da hare-haren wasu sasdan jihar Zamfara ya rabosu da gidajensu, inda ya basu gidajensa domin su zauna har komai ya lafa.

A taron maneman Labaru da ya kira a birnin Gusau, dan takaran ya ce ya dauki wannan matakin ne domin a zatonsa wadannan mutane ba za su zabi gwamnatin da ta kasa wadata jiharsu da tsaro ba.  Ya kara da cewa, ya umarci 'yan gudun hijiran da su fice masa daga gidajenda ne domin a ganinsa ba su san a zafin kansu ba.

Ya ce duk da ya basu shawara da kar su zabi wannan gwamnatin,  amma su ka yi kunnen uwar shegu su ka sake zabanta. Shinkafi ya bayyana cewa sun bari an sayi 'yancinsu da kudi,  dan haka ya ga ya dace ya yi musu hakan.

Jam'iyyar PDP Ta Cire Hoton Atiku Daga Sakatariyar Jam'iyyar.Jam'iyar ta dau matakin Hakanne  bayan shi atikun yayi fushi ya fice daga taron da akeyi da shugabanni da masu ruwa da tsakin jam'iyar!

Jam'iyar na ganin raini ne ga shugabanni da iyayen Jam'iya!

A wata majiyar jam'iyar na ciccire sauran alluna gaba daya da suka danganci Atikun!

Atiku wanda ya sha mugunyar kaye a hannun shuagban kasa Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC, ya ce ba zai amince da sakamakon babban zabe ba kuma bugu da kari zai ribaci karfin shari'a a gaban kotu wajen kwatowa kansa nasara da a cewar sa shi ya cancanta.

Ganduje Ya Bayyana Dalilin Da Suka Sa Bai Iya Kawowa Buhari Kuri'u 5m ba.


Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa rashin fitowar al'umma ne ya sa bai iya cika alkawarin da ya yiwa ba na sai ya tabbata Buhari ya samu kuri’u miliyan 5 ba a Kano, Ya kuma ce duk wadanda suke da ja bisa yawan kuri’un da Buhari ya samu suna da karancin hankali sannan basu kaunar tsarin mulkin dimokaradiyya.

Sakamakon zaben shugaban kasa na jihar Kano ya nuna shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi da kuri’u 1,464,768 shi kuma Atiku Abubakar ya samu kuri’u 391,593.

Ko da yake an sami matsaloli a wasu rumfunar zabe dake kananan hukumomi 17 a jihar inda ya sa aka soke zaben da aka yi a wuraren, an yi zabe cikin kwanciyar hankali kuma bisa tsarin dokar zabe, A karshe gwamna Ganduje ya ce abin da ya faru a zaben ranar Asabar nuni ne na yadda jam’iyyar su za ta yi nasara a zaben gwamnoni da 'yan majalissar jihohi mai zuwa.

'Yan Tada Zaune Tsayen Dake Sakkwato Da Kaduna Su Kuka Da Kansu - Inji Buhari.


Biyo bayan samun nasarar sa, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya jajantawa 'yan uwan wadanda mummunan ta'addancin masu ta'ada y ritsa da su cikin garuruwan Sakkwato da kuma Kaduna a kwana-kwanan nan.

A kwana-kwanan nan mun samu cewa, mummunan ta'addanci masu ta'ada a jihar Sakkawato da kuma rikici na kabilanci da ya auk a jihar Kaduna ya salwantar da rayukan mutane da dama kamar yadda shafin jaridar Daily Trust y ruwaito.
Masu tayar da zaune tsaye a jihar
Masu tayar da zaune tsaye a jihar Sakkwato, Kaduna su kuka da kansu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin wata sanarwa da sa hannun mai magana, Mallam Garba Shehu, ya bayyana cewa, masu tayar da zaune tsaye gami da dabbaka ta'addanci akan al'umma su kuka da kawunan sa domin kuwa fushin hukuma ba zai rangwanta masu ba.

Cikin jawaban sa na jaddada muhimmancin rayuwar al'ummar kasar nan, shugaban kasa Buhari ya ce sauran kiris masu mummunar ta'ad su fuskanci makomarsu daidai da miyagun ababe da suke aikawata.

Biyo bayan samun nasarar sa ta lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23, ga watan fabariraun 2019, shugaban kasa Buhari ya ce daukan matakai masu tsananin gaske wajen tsananta tsaro na daya daga cikin ababe da sabuwar gwamnatin sa za ta bai wa muhimmanci.

Majiyarmu ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari cikin jawaban sa na bayyana farin cikin samun nasarar sa, ya ce gwamnatin sa za ta zag dantse wajen habaka tattalin arziki, tsananta harkokin tsaro da kuma tumke damara wajen yakar cin hanci da rashawa.

Tuesday, February 26, 2019

BUHARI YA TAFKA MURDIYA A ZABEN NAN - Inji Sheikh Ahmad Gumi


Babban Malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya soki Shugaba Muhamadu Buhari bisa nasarar da ya samu na lashe zaben shugabancin kasa na 2019 da aka gudanar a ranar 23 ga watan Satumba kuma aka sanar da sakamakon zaben a ranar 27 ga watan Fabrairu.

Sheikh Gumi ya koka kan yadda Buhari ya yi gadarar cewa shine zai lashe zaben tun kafin a fara kirga kuri'u da al'umma suka kada.

Kamar yadda muka samu rahoto daga Daily Nigerian, Sheikh Gumi ya ce, "Tun kafin a kirga kuri'u, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi imani 100% cewa shine zai lashe zabe. Ta yaya ya san shine zai lashe zaben duba da cewa kan 'yan kasar a rabe ta ke kuma ana fama da talauci da fatara?

Yace "Ba dai zai ce ayyukansa da cancantarsa bane suka sanya shi ya lashe zabe. Tattalin arziki, tsaro da rashawa duk sunyi katutu a kasar. Kasar na fama da karancin ayyukan yi, ana samun karuwar kashe-kashe na kabilu, ana samun karuwar sace mutane, talauci da rashawa a ko wane lungu da sako.
"Abinda kawai zai sanya shi ya bugi kirji ya ce shine zai lashe zabe itace karfin mulki da ya ke dashi a matsayinsa na shugaba wanda shi ake nufi da halastaciyar rashawa.

"Duba TraderMoni da aka kaddamar watanni kadan kafin zabe sannan ana amfani da EFCC wurin musguwanawa abokan hammaya, amfani da kudin gwamnati wurin shirya kamfe, mamaye gidajen talabijin da rediyo na gwamnati da kuma amfani da masallatai domin yin kamfen da amfani da sojoji domin razana masu zabe da sauransu, halastaciyar rashawar na da yawa." inji shi

Sheikh Gumi ya koka kan yadda jam'iyyar APC ta rika rabawa mata a kauyuka N500 domin su zabi APC tare da amfani yara wanda shekarunsu bai kai na zabe ba wurin kada kuri'a da kuma yim amfani da mimbarin malamai domin kamfe.

Babban malamin ya yabawa dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar saboda jajircewarsa. Ya kuma shawarce shi ya yi watsi da sakamakon zaben ya garzaya kotu domin a bi masa hakkinsa kamar yadda Shugaba Buhari ya yi a baya.

A karshe Ya kuma yi kira ga al'umma su cigaba da zama lafiya tare da biyayya ga doka da oda.

((Zaben 2019)) Atiku Yaki Ya Kira Buhari Ya Taya Shi Murna.Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar bazai kira Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya tayashi murna ba, kuma ta bayyana zaben da cewa fashi ne aka yi mata da rana tsaka.

Jaridar The Cable ta ruwaito daya daga jigo a tafiyar Atikun kuma tsohon me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar shari'a, Kanu Agabi yana cewa tuni har sun hada kwamitin lauyoyi da zai shigar da kara akan zaben.

Yace sun bukaci a bashi kididdigar na'urar tantance katin zaben da aka yi amfani da ita a jihohin Borno, Yobe da Nasarawa amma har yanzu ba'a bata ba.

Jawabin Da Buhari Yayi Bayan INEC Ta Bayyana Sunansa A Wanda Yayi Nasara


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jawabin farko tun bayan da hukumar INEC ta sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa daya gudana a ranar 23 ga watan Feburairu, inda ya bayyana godiyarsa ga Allah tare da miliyoyin yan Najeriya da suka bashi goyon baya.

Legit.ng ta ruwaito a daren Laraba ne shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ya sanar da Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a karo na biyu, inda ya samu kuri’u miliyan 15.19, yayin da Atiku Abubakar ya samu miliyan 11.26.

A jawabinsa nasa da yayi da sanyin safiyar Larabar nan, Buhari ya gode ma Allah daya baiwa yan Najeriya ikon ganin wannan lokaci da aka samu cigaba a Dimukradiyyar kasa, da kuma nasarar da jam’iyyar APC ta samu.

Yace - “Na godewa miliyoyin yan Najeriya da suka sake zabena a matsayin shugaban kasarku na tsawon shekaru hudu masu zuwa, ina kaskantar da kaina tare da gode muku da kuka ga dacewar zabata na cigaba da yi muku hidima

 “Ina mika gadiyata ga Asiwaju Ahmad Bola Tinubu da rawar daya taka a matsayinsa na shugaban kwamitin yakin neman zabena, da shugaban jam’iyyarmu Adams Oshiomole, daraktan yakin neman zabe Rotimi Amaechi da sauran mambobin kwamitin.

 “Ina kara jaddada godiyata ga wadanda suka taimaka mana da harkokin sufuri da zirga zirga har muka karade dukkanin sassan kasar nan a yakin neman zaben da muka yi.

“Ina kuma gode ma miliyoyin yan sa kai da duk wadanda suka bamu gudunmuwa a wannan yakin zabe da muka yi bisa sadaukar da lokacinsu da suka yi don ganin mun samu nasara, bani da isassun kalaman godiya a gareku.

“Duk da dai anyi zaben cikin kwanciyar hankali, amma wasu miyagu sun yi kokarin tayar da hankula a wasu jihohi, amma jami’an tsaro zasu tabbata an hukunta duk wadanda suka kama daga cikinsu.

“Na yi bakin ciki matuka da asarar rayukan da aka samu yayin zabukan, amma jami’an tsaro zasu kara zage damtse wajen ganin sun kare rayuka da dukiyoyin jama’a a zaben gwamnoni dake tafe

“Ina yaba ma jami’an tsaro bisa rawar da suka taka waken tabbatar da tsaron kasar a yayin zabe duk kuwa da cewa aikin yayi musu yawa.

“Ina kira ga masoya da magoya bayana dasu kada su ci fuskar abokan hamayya ko muzguna musu, nasarar da muka samu kadai ta isa sakayyar kokarin da muka yi.

“Mun gode ma masu sa ido akan zabe daga ciki da wajen kasarnan, musammab duba da gudunmuwar da suka bamu wajen tabbatar da nasarar zaben.

“Gwamnatinmu zata mayar da hankali game da matsalar tsaro, sauya fasalin tattalijn arzikin kasa, da yaki da rashawa. Mun shimfida tubali mai karfi, kuma zamu tabbata mun kammala duk aikin da muka fara, zamu tafi da kowanne bangare a gwamnatinmu.

“Nagode muku da goyon bayan da kuka bani, da fatan Allah Ya albarkanci kasarmu Najeriya.” Inji shugaban kasa Muhammadu Buhari .

BUHARI YA LASHE ZABEN 2019, YA SAMU KURI'U 15,191,847


Bayan sauraro dalla-dalla daga bakin hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC sakamakon zaben kujeran shugaban kasan Najeriya da aka gudanar ranar Asabar, 23 ga watan Febrairu, 2019,

Muna tabbatar muku da cewa shugaba Muhammadu Buhari ne ya lashe zaben.

Muhammadu Buhari ya samu kuri'u 15,191,847 a zaben inda ya kayar da sauran yan takara 73 a jihohi 19, kuma mai binsa,shine  Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP.

PDP Ta Bukaci INEC Ta Dakatar Da Fadin Sakamakon Zaben Shugaban Kasa


Jam'iyyar PDP ta yi kira ga Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Mahmood Yakubu da ya dakatar da sanar da sakamakon zaben Shugaban kasa.

Jam’iyyar tayi wannan kira ne a wani taron manema labarai ta bakin mataimakin daraktan kamfen din Shugaban kasa na PDP, Kabiru Turaki tare da sauran jami’an jam’iyyar a daren yau Talata, 26 ga watan Fabrairu a Abuja.

Jam’iyyar tace INEC ta dakatar da sanarwar har sai INEC ta saki adadin wadanda na’urar tantance masu zabe ta tantance a zabe.

PDP Tayi zargin cewa an soke kuri’un da aka kada a wuraren da take da karfi musamman a "Yobe, Nasarawa, Zamfara da Plateau.”

A baya mun ji cewa jam'iyyar PDP, ta ki amincewa da sakamakon zaben Shugaban kasa daga jihar Katsina kan zargin rashin bin ka’ida.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC) kuma dan asalin jihar ya samu kuri’u 1,232,133 inda ya kayar da Atiku wanda ya samu kuri’u 303,056.

(Zaben Jahar Kano) Kwankwaso Zai Dauki Matakin Shari'ah Domin Tabbatar Da Adalci.

Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi kira ga magoya bayansa da su guji tayar da hankali bayan zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin tarayya.

Sanata Kwankwaso, wanda shi ne jagoran jam'iyyar PDP a jihar ta Kano, ya yi wannan kira ne bayan jam'iyyar APC ta yi nasara a kujerun majalisar dattawa da ta wakilai da ma shugaban kasa a jihar.

Ya ce za su dauki matakai na shari'a domin tabbatar da cewa rashin adalcin da aka yi musu bai dore ba.

A cewarsa, "Ina so na jawo hankalinmu cewa zaman lafiya shi ya fi komai muhimmanci; ka da wani ya dauki doka a hannunsa a kan wannan zabe.

"Muna fata mutane za su ci gaba da shirye-shirye na zaben gwamna da na 'yan majalisar dokokin jiha."

Ya kara da cewa sakamakon zaben shugaban kasa na ci gaba da nuna cewa babu tabbas kan wanda zai yi nasara har sai an kammala bayyana sakamakon.

Sanata Kwankwaso ya yi kira ga magoya bayansa musamman a jihar Kano da su sake daura damara domin kayar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

BBC Hausa

(Kishin Kumallon Mata) Wata Mata Ta Jefo Mijinta Daga Bene Ya Mutu Bisa Zargin Soyayya Da Wata.


Wannan labarin dai yafaru a Unguwar Dorayi inda ake zargin Amaryar maisuna Rashida Said da hallaka mijinta maisuna Adamu Ali wanda malamine a makarantar FCE Kano

Tunda fari dai marigayi ana zargin yana yin waya da wata mata ne itakuma tazo tai yunkurin kwatar wayar shikuma yaki amincewa da hakan daga bisani kokawa ta harke tsakaninsu inda ake zargin ta hankadoshi daga saman bene

Nan da nan gida yacika da ihu daga bisani kaninsa mai suna Shuaibu Ali yadaukeshi a motarsa inda aka garzaya dashi Asibitin Aminu Kano kafin wani lokaci rai yayi halinsa inji dan uwan nasa

Mujallar Gidan Baka noma ta ziyarci gidan marigayin inda muka iske mutane jugun jugun a kofar gida

Tuni dai jamian tsaro daga ofishin yan sandan Gwale suka dakume matar kuma ana cigaba da bincike

Hakan yasa muka tanbayi kakakin rundunar ta Kano wato DSP Abdullahi Haruna yakuma tabbatar da faruwar lamarin.

Sakamakon Zaben Jihohin Borno da Yobe Yasa 'Yan Kudu Na Zagin 'Yan Arewa.


Sakamakon jihohin Yobe da Borno sun tayar dawa da mutanen Kudu, Musamman Inyamurai hankali inda su kai ta zagin yankin Arewa da kiransu da sunayen da suka saba na cin zarafi, irin su Almajiri da Malam da kuma fadar cewa wai 'yan Arewan ba su gaji da talauci da kashe-kashen da ake musu ba.

Lamarin yayi zafi sosai a shafukan sada zumunta, Musamman a Twitter, inda wasu ke cewa wai ba zasu kara baiwa almajirai 'yan Arewar sadaka ba, wasu kuwa cewa suke idan akayi kisa a arewar ba zasu sake nuna alhini ba tunda dai 'yan arewar sun zabi jam'iyyar APC.

Yan kudun Sun rika kiran 'yan Arewar da jahilai dadai sauransu.

Saidai wannan lamari da alama ba wai akan zabe bane kawai ya tsaya ba, dama can akwai wata a kasa,

Yobe dai Buharine ya lashe ta sannan da yawa daga cikin kananan hukumomin Borno ma shine yake kan gaba, sannan wai wani abin cewa, shin duk mutanen nan ba 'yan Arewa bane? Menene nasu idan 'yan Arewar suka zabi wani suka kuma ki zaban wani.kamar yadda Wasu 'yan Arewar sun rika mayar musu da martani.

Saidai abinda wannan abu ya kara fito dashi fili shine, idan dai ana maganar mulki na dimokradiyya a kasar nan to dolene fa sai an yi da dan Arewa, sannan zagin da suke wa 'yan Arewa yana kara kore sune daga samun damar mulkar kasar nan.

An Bawa Atiku Shawara Daya Rungumi Kaddara, Ya Kuma Kira Buhari Ya Taya Shi Murna.


Mawallafin jaridar ‘Ovation Magazine’ kuma daya daga cikin fitattun magoya bayan dan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya shawarce shi da ya kira shugaba Buhari, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, a waya ya taya shi murnar samun nasara a zaben da aka gudanar ranar Asabar.

Mista Momodu, fitacce a dandalin sadarwar zamani, ya bayar da shawarar ne da safiyar yau, Talata, a daidai lokacin da hukumar zabe ta kasa (INEC) ke cigaba da karbar skamakon zabe daga jihohin Najeriya.

Da ya ke bawa Atiku shawara a shafin san a (@delemomodu), Mista Momodu ya ce ya san cewar Atiku zai tuntubi shugabancin jam’iyyar PDP da iyalinsa kafin ya kira Buhari.

Ya kara da cewar yin hakan zai kawo zaman lafiya da kuma Karin kim ga Atiku.

A cewar Mista Momodu, “Ya mai girma Wazirin Adamawa, a matsayin ka na mai imani, na san cewar yarda cewar Ubangiji ke bayar wa ko kabar mulki. Ka yi rawar gani. Kar ka ji nauyin kiran shugaba Buhari domin taya shi murna. Hakan ba zai rage ka da komai ba .”

Mista Momodu na daya daga cikin jama’ar da su ka yi wa Atiku yakin neman zabe kuma su ka bayyana cewar su na da yakinin cewar zai lashe zaben shugaban kasa, musamman saboda gazawar gwamnati mai ci a bangarori da dama.

Ya bayyana cewar ya yi wa shugaba Buhari yakin neman zabe a 2015 amma ya dawo daga rakiyar gwamnatin sa bayan rashin gamsuwa da kokarin ta.

A yayin da INEC ke cigaba da karbar sakamakon zabe daga baturan zabe na jihohi, shugaba Buhari na cigaba da bawa Atiku ratan kuri'u ma su yawa.

Sai dai har yanzu INEC ba ta kammala karbar sakamakon ba balle ta sanar da wanda ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasa a tsakanin Atiku da Buhari.

Sakon Godiya Daga Sabon Sanatan Kano Ta Tsakiya Mallam Shekarau.


Da sunan Allah Ta'ala, mai rahama da jinkai, tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammadu SAW.

Ni Sanata Ibrahim Shekarau, mai wakiltar al'ummar jihar Kano Ta Tsakiya,, ina farawa da godiya ga Allah bisa wannan nasara da ya bamu ta cin zaben sanata a jam'iyyarmu ta APC.

Wannan nasara ta al'ummar mu ce gaba daya, don haka ina godiya garesu duka.
Ina amfani da wannan dama na godewa jama'ar Kano Central da suka ga dacewar su zabeni don na wakilcesu a majalisar dattijai ta Najeriya.

Ina godiya matuka ga jam'iyyar APC ta kasa da ta jihar Kano da babban kwamitin kamfe dina da suka yi dawainiya har aka zo wannan matakin.

Haka kuma ina mika godiya ta musamman ga gwamnan jihar Kano da 'yan majalisarsa da duk zababbunmu na APC masu komawa da sababbi da shugabanni zababbu na mulki da jam'iyya na Kano a kananan hukumomi.

Wannan nasara tamu ce gaba daya, kuma da yardar Allah, zamu ci gaba da amfani da ita don hidimtawa al'umma da basu wakilci na kwarai.

Nagode
Sanata Ibrahim Shekarau CON
Sardaunan Kano

An Kone Masa Wajen Sana'arsa Don Kawai Yana Goyen Bayan PDP


wasu Matasa Magoya Bayan Jam'iyyar APC sun Kona rumfar Wani Mai shayi a Garin Sule Tankarkar, Jahar Jigawa yayin da suke Zagayen murnar Cin Zaben Dan Majalissar Tarayya Mai wakiltar Kananun hukumomin Gagarawa Gumel Maigatari da Sule Tankarkar.Rahotanni sun nuna cewa matasan sun kone rumfar ne saboda Mai shayin yayi kaurin suna wajen goyon bayan Jam'iyyar PDP da Caccakar jam'iyyar APC .


Monday, February 25, 2019

SEN. BUKOLA SARAKI YAKI AMINCEWA DA SAKAMAKON ZABEN SA.


Jami'in zaben shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki ya ki amincewa da sakamakon zaben jihar Kwara ta Tsakiya da hukumar zabe wato INEC ta gabatar, inda ya ki yadda da ya sa hanu a takardar yadda da sakamakon wanda dan takaran nasa ya shakaye. Ya ce ba zai sa hanu ba domin akwai magudi a sakamakon zaben.

Sen Bukola Saraki. Da jam'iyyar ta PDP suna zargin da an tafka magudin a zaben da aka gudanar.

Ko me za ku ce game da hakan da ya yi?

((Sakamakon Zabe)) Buhari Ne Ke Akan Gaba A Jahar ObasanjoShugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu rinjaye a kananan hukumomi 12 daga cikin 18 da hukumar zabe ta sanar daga cikin 30 da jihar ta Ogun ke da su, shi kuwa abokin karawarsa Atiku Abubakar na jam'iyar PDP ke da 6.

Saura kanan hukumomi 14 da ba su kawo sakamakonsu ba.

Ga kananan hukumomi 18 da hukumar zabe ta sanar da sakamakomsu;

Abeokuta North
APC 22,044
PDP 7,528

Sagamu LG
APC 20,875
PDP 16,532

Remo North LG
APC 5,695
PDP 6,269

Odeda LG
APC 10,049
PDP 4,995

Imeko-Avon LG
APC 6,425
PDP 5,700

Ijebu North-East LG
APC 6,435
PDP 5,349

Ewekoro LG
APC 10,060
PDP 5,101

Ijebu Ode LG
APC 12,850
PDP 7,253

Ogun Waterside LG
APC 6,889
PDP 8,262

Yewa South (Egbado South) LG
APC 12,934
PDP 10,709

Obafemi-Owode LG
APC 16,243
PDP 7,938

Ikenne LG
APC 10,283
PDP 8,708

Abeokuta South LG
APC 26,462
PDP 13,853

Ado Odo-Ota LG
APC 33,348
PDP 20,352

Ifo LG
APC 23895
PDP 8968

 Ijebu North LG
APC 13,974
PDP 16,196

((Zaben 2019) APC Ta Lashe Gaba Daya Kujerun Jahar Kano.


A wani salo mai kama da abinda ya faru a 2015, Jam'iya mai mulki ta cinye dukkanin kujerun Dattijai da Wakilai.
 Abune mai wuya idan akwai wata mazaba da aka kayarda jam'iyyar a zaben da ya gabata.

Wannan abu yazo wa mutane da dama mamaki, duba da yadda shi Buhari bai ce ayi Sak ba,


Shin kuna ganin hakan yar manuniya ce akan zaben jaha da za ayi nan gaba?  Sai munji daga gareku!

#JaridarDala

Hon. Yakubu Dogara Shi Da Sen. Dino Malaye Sun Yi Nasarar Cinye Zaben Su


Kakakin Majalisar wakilai ta Najeriya, Honarabul Yakubu Dogara, ya samu nasarar lashe kujerarsa ta dan Majalisar Wakilai daga Jiharsa ta Bauchi.
.
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ita ta tabbatar da Yakubu Dogara a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaben dan Majalisar Tarayya mai wakilatar Kananan Hukumomin Bogoro da Tafawa-Balewa.
.
Honorabul Yakubu Dogara na Jam'iyyar PDP, ya samu kuri'u 73,609. da ta ba shi damar doke babban abokin hamayyarsa, Mista Dalhatu Kantana, na APC da ya samu kuri'u 50,078.Shima Sanata Dino Melaye ya yi nasarar lashe zaben kujerar sanatan shiyyar kogi ta yamma

Fitaccen Sanatan nan mai kaifin baki, Dino Melaye, ya yi nasarar lashe kujerar sanatan jihar Kogi ta yamma a zaben ranar Asabar din da ta gabata, inda hakan ke nufin shi zai koma zauren majalisar ta dattawa a matsayin sanata mai wakiltar al’ummar Kogi ta yamma.

Dino ya kayar da abokin karawarsa na kusa da kusa na jam’iyyar APC, Smart Adeyemi da kuri’a 85,395, inda Adeyemi ya samu kuri’a 66, 902

Kananan hukumomin da ke a karkashin mazabar Kogi ta yamma sun hada da: Lokoja, Kogi/Koton Karfe, Kabba/Bunu Ijumu, Yagba ta gabas da kuma Yagba ta yamma, inda Dino ya lashe kananan hukumomi 6 daga cikin 7.

Ga yadda sakamakon ya kama:

Karamar hukumar Lokoja
PDP = 24576
APC = 18800

Karamar hukumar ta gabas
PDP = 8638
APC = 5077

Karamar hukumar Mopa Amuro
PDP = 5112
APC = 3658

Karamar hukumar YAGBA TA YAMMA
PDP 8942
APC 6799

Karamar hukumar IJUMU
PDP 11,749
APC 8,517

Karamar hukumar KABBA/BUNU
APC 8,971
PDP14, 756

Karamar hukumar Kogi
APC 15,728
PDP 11,622

{Labarai} Hukumar DSS Ta Musanta Kama Buba Galadima


Hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, ta musanta rahoton da ake yadawa na cewa wai jami’anta sun cafke fitaccen dan adawan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Injiniya Buba Galadima, kamar yadda hukumar ta bayyana.

Majiyarmu ta ruwaito DSS ta musanta rahoton ne a daren Lahadi, 24 ga watan Feburairu, inda tace ba kamar yadda ake yamadidi a kafafen watsa labaru na ciki da wajen kasar nan ba, bata san ma inda Buba Galadima yake ba.

A jiya ne aka ruwaito guda cikin yayan Buba Galadima ta bayyana cewa wasu mutane cikin wata mota mara lamba sun cafke mahaifinta a unguwar Wuse 2 na garin Abuja, inda suka yi awon gaba dashi, don haka tayi zargin gwamnati ce ta kama shi.

A ranar Lahadin ne dai kaakakin yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari, Festus Keyamo ya bayyana bukatar ganin an kama Buba Galadima don kada ya kawo tashin hankali a Najeriya sakamakon wani bidiyo da yayi inda yayi zargin PDP ce kan gaba a zaben daya gudana a ranar Asabar.

Sai dai ko a lokacin da Buba yake wannan magana, hukumar INEC bata sanar da sakamakon zaben shugaban kasa a kowacce jaha ba, don haka APC ta zargi Buba Galadima da shirya makarkashiya tare da shirin tunzura jama’a su ki amincewa da sakamakon zaben idan har ba PDP aka sanar ta ci ba.

A jawabin Keyamo, “Mun samu labarin cewa PDP sun shirya tayar da hankali tare da jefa yan Najeriya cikin rudani ne kafin hukumar zabe ta INEC ta sanar da sakamakon zaben, don su nuna cewa Atiku ne ya samu nasara tun ma kafin a sanar.

“Daga nan kuma sai su fita da sunan shirya zanga zanga a wasu sassan kasar nan tare da yan daban siyasa da nufin janyo hankalin kasashen duniya domin su tausaya musu, don ganin kasashen duniya sun yi ma Najeriya abinda suka yi ma kasar Venezuela.” Inji shi.

Allah shi kyauta.

Sunday, February 24, 2019

((Breaking News)) Jami'an Tsaro Sun Kama Buba Galadima


Bayanai daga iyalen Dan hamayyar nan Alhaji Buba Galadima sun shaida wa BBC cewa an kama Buba din ranar Lahadin nan.

Wani makusancin sa ya ce suna zargin jami’an tsaron farin kaya ne na DSS suka kama Buba da rana jim kadan bayan ya fita daga gidansa.

Wani makusancin dan siyasar a kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugabacin Najeriya a jam’iyyar PDP da ya nemi a sakaya sunansa ya ce sun tura wakilansu zuwa ofishin DSS domin bincika dalilin kama Buba Galadima.

Sai dai har kawo yanzu babu wani bayani daga hukumar ta DSS kan zargin kama jigon na hamayya.

A ranar Asabar, Festus Keyamo da ke magana da yawun kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Muhammmadu Buhari ya yi kira a kama Buba Galadima, bisa zargin yan shirin bayyana sakamakon zabe na boge.

Buba Galadima dai shi ne shugaban R-APC wani bangare da suka balle daga jam’iyyar APC, kuma yana cikin masu magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar da ke takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP.
#NigeriaDecides2019 #BBCNigeria2019

'Yan Sanda Sun Kama Yaron Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido Da Kayayyakin ZabeFitaccen ɗan Jam'iyyar PDP,  kuma mai taimakawa tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido na yanar gizo Mansur Ahmed ya shiga hannun ƴan sanda a hanyar Birnin Kudu zuwa Chiyeku da kayayyakin Hukumar Zaɓe da suka haɗa da huluna, jaket, kuɗaɗe da alamar masu sanya ido akan zaɓe na Hukumar Zaɓe mai zaman kanta, da kuma lambobin mota da takardun zaɓe. 

Mansur Ahmed wanda yake tare da waɗannan kayayyaki domin ya samu damar shiga wuraren gudanar da zaɓe, ya shiga hannun jami'an ƴan sandan ne a yayin da suke gudanar da aikin su.

Mansur Ahmed wanda asalin ɗan Ƙaramar Hukumar Jahun bashi da wani alaƙa da Birnin Kudu, kuma akwatin zaɓen sa baya Birnin Kudu.

Auwal D. Sankara (Fica),
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)
24/02/2019

(Zaben 2019) Bukola Saraki Ya Sha Mummunan Kaye A Hannun Dan Takarar APC.


A labarin da muke samu Shugaban majalisar Dattawa Sen. Abubakar Bokola Saraki ya rasa kujerarsa inda Dan takarar Jam iyyar APC Dr. Ibrahim Yahaya Oloriegbe yayi nasara.

Bukola Saraki yasha Mummunan kaye a hannun dan takarar jam'iyyar APC. Inda ya bashi tazara mai yawa. Domin a yadda sakamakon ya nuna shine:

PDP = 87.032.
APC = 151, 763.

Gade wasu daga cikin sakamakon zaben na yan kuna 40 daga ciin 52 dake a Kwara ta tsakiya.
Friday, February 22, 2019

((Zaben 2019)) INEC Ta Karbi Sunayen 'Yan Takaran APC a Jihar Zamfara.

Hukumar zabe mai zaman kanta a sanarwa da ta fito dauke da sa hanun Komishinan yada labarunta da wayar da kan masu zabe, Festus Okoye ta amince da karbar sunayen 'yan takaran jam'iyar APC a jihar Zamfara. INEC ta ce wannan ya biyo bayan umarni da kotun daukaka kara na tarayya ta bayar a jiya Alhamis, 21 ga watan Feburairu, inda ta ce ita kuwa a shirye ta ke da bin umarnin kotu.

Sanarwar ya kara da cewa, hukumar zabe ta yi watsi da hukuncin babbar kotun tarayya da ta haramta wa hukumar karbar sunayen 'yan takaran a jihar. Sannan ta kara da cewa, yanzu ta amince tare da gabatar da jam'iyar APC a cikin jerin jam'iyu da za a dama da su a babban zaben shugaban kasa, gwamnoni da na 'yan majalisun jiha da na tarayya da za a fara daga gobe Asabar, 23/02/2019.

Sai de duk da haka wasu na zargin INEC akan saboda ta karbi 'yan takarar ne yasa ta dage zabe.

Wasu 'Yan Bindiga Dadi Sun Bude Wuta A Kan Tawagar Yemi Osibanjo A Jahar Kwara


Mun samu rahoton cewa wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton magoya bayan jam'iyar adawa ta PDP ne sun buda wa tawagar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo wuta a lokacin da ya kai ziyarar yakin neman zaben gida gida da ya ke bi a yau, domin sake da mai gidansa shugaban kasa Buhari. Sai dai an bayyana cewa Osinbajo ba ya cikin tawagar a lokacin da lamarin ya faru.

Rafiu Ajakaiye, kakaki ga dan takaran gwamnan jihar Kwara, Abdulrazaq Abdulrahaman, ya fitar da jawabin cewa, lamarin ya faru ne a garin Isale-Aluko. APC ta zargi PDP da daukan nauyin harin inda ta bukaci hukuma da ta dauki matakin gaggawar kan wadan da su ka kai wannan harin.

Sai dai a bangaren jam'iyar PDP, ta ce rikici ya fara kaurewa ne a lokacin da su ka ga tawagar APC na raba wa jama'a kudi a garin, sannan ta nesanta kanta da kai wannan harin.

Da Kwamishinan 'Yan Sanda Ya Bi Shawarata Da Duk Hakan Bata Faruwa Ba - Ganduje.


Gwamnatin jihar Kano ta bakin Maigirma Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta ce da a ce Kwamishinan 'Yan Sandan jihar Kano ya bi shawarar da Gwamna ya ba shi tun da farko, da cin mutuncin da a ka yi wa 'yan jam'iyyar APC wadanda su ka taru wajen yin addu'ar rokon samun zaman lafiya dangane da zabubbuka masu zuwa, bai faru ba. Wanda ta kai har wasu sun rasa rayukansu, bayan munanan raunuka da a ka yi ma wasu.

Duk da cewar 'yan jam'iyyar APC su na da taronsu a wajen da abokan adawa suke kokarin yin nasu zagayen kamfen din, an shawarci Kwamishinan 'yan sandan da ya janye damar da ya ba 'yan jam'iyyar adawa ta PDP.

Amma ganin haka ba ta samu ba, ta kai su 'yan APC din su ka janye nasu taron. Wanda a maimakon taron, su ka yanke hukuncin yin addu'o'i na neman samu zaman lafiya saboda tinkarowar babban zabe na kasa.

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da jama'ar garin Kofa na karamar hukumar Bebeji, wadanda a kai wannan balahira a garinsu, su ka kai wa gwamnan wata ziyara a ofishinsa da ke gidan gwamnatin jihar Kano.

Kamar yadda gwamnan ya ambata, gabanin wannan mummunan abu da ya faru, wanda ya jawo sanadiyar rasuwar mutane da jikkata wasu da kuma kone ababen hawa har guda arba'in (40), ya yi ta kokarin jan hankalin kwamishinan 'yan sandan ya nusasshe shi cewar za fa a iya samun matsala matsawar a ka ce za a ba wa jam'iyyu guda biyu mabanbanta su yi tarukansu a waje daya.

Amma ba abinda ya fito daga bakin kwamishinan sai cewa kawai ya yi ai ya rigaya ya ba wa 'yan jam'iyyar PDP damar yin taro. Bayan mu jam'iyyar APC an amince da janye taron na mu, sai kawai a ka je wani wajen da a ka hada yin addu'a ta musamman ta neman zaman lafiya. Amma haka kawai sai a ka kai musu farmaki ba gaira ba dalili.

A daidai wannan lokacin da su 'yan Kwankwasiyya ke yi wannan mummunan ta'annati da miyagun makamai, shi jagoran nasu Rabi'u Musa Kwankwaso ya na gani amma abin takaici ko uffan bai ce musu ba, wajen hana su. A nan ne fa a ka kashe wasu sannan a ka jikkata wasu, a ka bar su a kwance jina-jina.

A wannan lokaci ne kuma a ka yi wani ta'annatin kan gidan dan majalisar tarayya mai wakiltar Bebeji da Kiru. Ba gaira ba dalili. Wannan abin takaici har ina?

Maigirma Gwamna ya yi Allah wadai da wannan ta'asa ta rashin kyautawa da rashin mutunci. A dalilin haka ya yi kira ga hukumomin tsaro wadanda ke da wannan alhaki, su kwakwulo wadanda su ke da hannu kan wannan ta'asa.

Ya kara neman a kara kwakwulo marasa kyautawa din nan 'yan Kwankwasiyya wadanda ke yi wa jama'a kwacen wayoyin hannu da kuma farfasa gilasan motocin mutane duk lokacin da su ka yi zagayensu na kamfen. Har ta kai ba ma a nan kadai su ka tsaya ba, hatta da gidajen jama'a ma ba su tsira ba. Ya ce ya zama wajibi a kwakwulo su saboda a gurfanar da su gaban shari'a.

Sa Hannun
Malam Muhammad Garba
Kwamishinan Yada Labarai Na Jihar Kano
22 ga Watan Fabrairu, 2019

{Labari Da Dumi-Duminsa} 'Yan Sanda Sun Kama Dan Majalisar Kiru/Bebeji Hon. Kofa.


Rundunar yansanda ta Jihar kano ta yi caraf ta dam'ke Abdulmumin Jibril 'Dan Majalisar Kiru/Bebeji wanda yasa shine aka kaiwa Sanata Kwankwaso hari jiya a garin Kofa.
DA DUMI DUMINSA!!

A jiya ne dai aka kaiwa tawagar Sanata Rabiu musa Kwankwaso hari akan hanyarsa ta zuwa Karamar Hukumar Bebeji. An hallaka mutane da dama kuma an kona motoci goma 'kurmus.
Ku saurare mu da 'karin bayani anjima...

Buhari Ya Roki Masana Dasu Tattara Barnar Da PDP Ta Yi A Shekaru 16, Saboda 'Yan Baya


Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa akwai matukar muhimmanci masana tarihi da na tattalin arziki su tattara bayanan irin barnar da gwamnatin PDP ta yi a cikin shekaru 16, domin kada al’ummar da za ta zo nan gaba su maimaita irin wannan barnar.

Buhari ya yi wannan jamawbi ne a Fadar Gwamnati, a jiya Alhamis inda Kungiyar ‘Yan Takarar Shugaban Kasa suka kai maza ziyara. A ta su ziyarar dai sun ce sun ajiye muradin su na neman mulki, za su goyi bayan jam’iyyar APC ce.

Kakakin Shugaban Kasa, Femi Adesina ne ya bayyana labarin wannan taro da aka yi.

“Na yi murna da wannan irin kishi da ku ka nuna. Na san da kun so da kun hana ni kuri’un yankunan ku. Domin duk irin kaunar da jama’ar ku ke min, idan aka zo zabe, to a yankunan kun a san ku za su zaba.”

Amma Buhari ya ce ya ji dadi da ‘yan Najeriya suka fahimci muhimman matsaloli uku da ya sa a gaba, wato kawar da rashawa, matsalar tsaro da kuma inganta tattalin arziki.

Buhari ya shaida musu cewa an yi gagarimar asarar kudaden shiga a cikin shekaru 16 da PDP ta yi ta na mulki.

Ya tunatar da su yadda PDP ta bar titinan mota, hanyoyin jiragen kasa duk su ka lalace.

Ya ce da mulkin PDP ya gyara titina da sauran abubuwan da suka dace su yi, to da ‘yan Najeriya basu damu sosai ba. Kuma da ba su ma damu da ko wa ke shugabantar su ba.

“Ya kamata masana tarihin mu da masana tattalin arziki su tattara bayanan barnar da PDP ta yi a cikin shekaru 16, domin ‘yan baya su dauki darasi, yadda su ma ba za su mamaita irin abin da aka yi ba.

Shugaban Kungiyar mai suna Shittu Mohammed Kabir, wanda kuma shi ne daga jam’iyyar APDA, ya ce sun yanke shawara ne cewa ya kamata su goya wa Buhari baya saboda irin gagarimin ci gaban da ya samar a fannin tsaro, yaki da rashawa, samar da kayan more rayuwa, inganta harkar noma da sauran ci gaba a fannoni da dama.

Wadanda suka halarci ziyarar sun hada da: Edozie Madu, Independent Democrats; Danjuma Mohammed, Movement for Restoration & Defence of Democracy; Yusuf Nadabo Dantalle, Allied Peoples Movement; Ahmed Buhari, Save Nigeria Party; and Alhaji Isah B. Dansarki, Mass Movement of Nigeria.

Akwai kuma irin su: Ikechukwu Nwaokafor, Advance Congress of Democrats; Alista Soyode, Yes Party; Barrister Charles Ogbali, Advanced Nigeria Democratic Party; Kenneth Ibe Kalu, United Peoples Congress; Comrade Isiyaka Paul Femili, Nigeria Element Progressive Party; sai kuma Robinson Akpu, National Democratic Liberty Party.

Thursday, February 21, 2019

DALILIN DA YASA NA JAGORANCI MALAMAI 100 ZUWA WAJEN KWANKWASO - Inji Sheikh Daurawa.


Babban kwamandan hukumar Hisbah ta jahar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyan dalilin da yasa ya jagoranci Malamai guda dari zuwa gidan tsohon gwamman jahar Kano, Sanat Rabiu Kwankwaso a gidansa.

Daurawa ya bayyana ma jaridar Daily Trust dalilin ne a wata hirar wayar tarho da yayi da ita a ranar Laraba, 20 ga watan Feburairu, inda yace sun kai ma Kwankwaso ziyarar ne da nufin sulhunta tsakaninsa da wasu Malaman addinin Musulunci jahar.

Idan za’a tuna an samu cacar baki da musayar yawu tsakanin Sanata Kwankwaso da shugaban kungiyar Izala reshen jahar Kano, Sheikh Abdallah Saleh Pakistan akan dan takarar da yafi cancanta Kanawa su zaba a mukamin gwamna.

Duk da cewa akwai rade radin Gwamna Ganduje zai tsige Daurawa daga mukaminsa, amma a jawabinsa, Daurawa yace sun kai ziyarar ne domin kwantar da hankulan da suka tashi sakamakon wancan takaddama tsakanin Malamai da Kwankwaso.

“Mun samu labarin Malamai sun yanke hukuncin caccakar Kwankwaso  akan mumbarin huduba, haka zalika suma yan Kwankwasiyya sun dauki alwashin mayar da martani akan Maluman, don haka muka ga dacewar shiga tsakani a matsayinmu na Malamai.

“Mun samu nasara saboda yan Kwankwasiyya basu mayar da martani ba duk kuwa da cewa Malaman sun yi hudubar tasu.”

Kamar yadda Daura ya bayyana, sai dai game da sallamarsa daga aiki kuwa, Daurawa ya bayyana rashin wata masaniya game da hakan .

“Kafin na tafi Umarah, na mika makullin ofishina ga kwamandan Hisbah na biyu, kuma babu wanda ya kirani ya bayyana min wani abu game da kulle ofishina ko sauya ma sakatarena wajen aiki, kuma babu wata wasikar sallama da aka bani, muna ji muna gani muna kuma sauraron gwamnati.” Inji shi

Alah shi kyauta.

{Rikicin Kofa} Ganduje Yayi Alkawarin Ganin An Hukunta Duk Wani Mai Ruwa Da Tsaki A Tada Rikici A Garin Kofa.


Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi tir da Allah Wadai ga 'yan Kwankwasiyyar PDP wadanda su ka kai farmaki ga wasu 'yan jam'iyyar APC wadanda su ka shirya wata addu'a ta  musamman ta rokon Allah neman zaman lafiya a zabubbukan da ke tafe a wannan kasa.

Wanda a dalilin wannan farmaki ne da 'yan Kwankwasiyyar su ka kai har wasu su ka rasa rayukansu. Wasu kuma su ka samu raunuka daban-daban. Abin takaici da nuna rashin mutunci.

Wannan rashin kyautawa da ta'annatin da su ka yi sun yi shine a kan idon jagoransu Rabi'u Musa Kwankwaso, wanda su ke kewayen kamfen din su na siyasa na yakin neman zabe.

Sannan gasu dauke da makamai tsirararsu lokacin da suka kai farmaki kan masu addu'a wacce wakilin Kiru da Bebeji a majalisar tarayya, Abdulmumini Jibrin Kofa ya shirya,  Ana rokon Allah kan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. Musamman a lokutan zaben da ke tafe.

Wannan farmaki da ta'annati shine na baya-bayan nan da 'yan Kwankwasiyya ke kai wa jama'a haka kawai wai saboda su kawo cikas idan lokacin zaben ya zo. Tun yanzu sun fara hangowa kansu faduwa kasa wanwar. Ba su da wata makama ko mafita, sai kawai suka fake da ire-iren wadannan harkokin rashin kyautawa da rashin mutunci.

Maigirma Gwamna Ganduje ya bayyana cewar ya tabbatar da 'yan Kwankwasiyya kawai sun yankewa kansu hukuncin huce haushinsu ne a kan 'yan jam'iyyar APC da jama'ar gari saboda su tayar da hankulan jama'a dan su tsorata su su ki zuwa zaben dake gabanmu na wannan shekarar ta 2019.

Gwamna yana yi wa wadanda aka zalunta aka raba su da rayukansu ba gaira ba dalili, addu'ar Allah Ya jikansu da rahama. Yana kuma yi wa wadanda suka ji ciwo fatan samun lafiya da saurki.

Ya umarci jami'an tsaro da su yi duk mai yiwuwa wajen zakulo wadanda ke da hannu wajen wannan ta'asa da fatan a hukunta su daidai da laifukan da suka aikata. Gwamnan
ya sha alwashin ganin an hukunta duk wanda ke da hannu a wannan abin Allah Wadai.

Sa Hannun
Muhammad Garba,
Kwamishinan Yada Labarai Na Jihar Kano
21 ga Watan Fabrairu, 2019.

Kwamishin 'Yan Sanda Na Kano Ya Kama Wukake 6,750 Tare Da Tulin Kwayoyi.


Rundunar 'yan sanda ta kasa reshen Jihar Kano ta bayyana cewar ta kama wani mutum da take zarginsa da safar wasu wukake  6750 a Kwanar Dumawa  inda zai kai Jihar Katsina.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano Wakili Muhd ya ce suna bincike akan wukaken kafin daukar matakin da ya dace akan mutumin da ake zargi.

Haka kuma kwamishinan 'yan sandan ya tabbatar da cewar sun kama wani mutum da ya yiwo safarar madarar sukudai shida.

Kwamishina Wakili Ya ce rundunar ta cafke wata babbar motar dakon kaya wacce aka cika ta makil da miyagun kwayoyi zuwa Kano.


Ya kuke ganin kokarin Kwamishinan 'Yan sandan Jihar Kano musamman a wani lokaci a wannan lokaci da za a shiga zabe.


Mutanen Da Gawuna Ya Samawa Aikin KAROTA Sun kai masa Ziyara GodiyaMai girma Mataimakin Gwamnan jihar Kano *Dr. Nasiru Yusuf Gawuna* kenan lokacin da ya kar6i bakuncin kadan daga cikin sabbin jami'an tsaro na *KAROTA* wadanda suka samu aiki ta karkashin Ofishinsa da suka zo don yi masa godiya da fatan yadda ya tallafi rayuwarsu yake kuma cigaba da tallafawa al,umma shi da mai girma Gwamna *Dr. Abdullahi Umar Ganduje* suma Allah ya cigaba da zama gatansu...Amin.


Mataimaki Gwamna De yaji dadi wannan ziyara da suka kawo masa, kuma ya tabbatar musu da cewa zai cigaba da ganin ya samarwa da Al'umma aiki daga kowanne bangare idan bukatar hakan ta taso,


Laraba 20/02/2019.
Dab'i📸✍🏾:-- *Abbakar DK*
S.A na Mataimakin Gwamnan Kano.

Popular Posts