Thursday, January 31, 2019

Alarammomi A Jhar Kano Sun Yiwa Gadar Sama Saukar Alqur'ani Maigirma.A daren jiya Laraba ne wasu Alarammomi a jahar Kano sukai Saukar karatun Alqur'ani Maigirman a saman gadar Sabon gari wacce ke a titin Murtala Muhammad Way.

 Alarammomi de sun yi wannan saukar ne domin neman Albarka tare da amfanar da mutanen jahar Kano,Gadar Sabon Gari itace katafariyar Gadar nan da babu irin a wannan kasa, wacce Tsohon Gwamnan Kano Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso ya faro aikin ta, inda bayan Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya hau sai ya dora da aikin ta.

A yau Alhamis Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai zo Jahar Kano domin kaddamar da yakin neman zabensa na 2019.

Wannan gadar tana daya daga cikin ayyyukan da shugaban kasar Buhari zai bude, yayin da yazo jahar kanon, akwai kuma Gadar Kasa dake kan titin barikin Sojoji na Bokavo. Dade sauran Aikace-Aikace Wanda maigirma Gwamanan Kano yayi.

Tuesday, January 29, 2019

Ko Kun San Babban Abin Alkhairin Da Buhari Yake Shukawa 'Yan Arewa Kuwa?Alkairin Baba Buhari A Arewa, Wanda iya shi yaci ace mun sake bashi dama a karo na biyu.

Wannan na daga cikin Ayyukan Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sanya na kudurta a zuciyana zan sake zaben shugaban kasa Buhari karo na biyu.

Kamar yadda kuke gani cikin wannan Hotuna, wajen aikin nemo danyen Manfetur ne da akeyi a karamar hukumar Alkaleri na jihar Bauchi, tun dalewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan karagar mulki aka fara wanga aiki kuma kawo yanzu ana irin wannan aiki a jihohin Gombe da Maiduguri duk domin inganta tattalin arzikin yankin Arewa. Samarda danyen manfetur a yankin mu na Arewa zai kawo karshen cin fuskar da kudanci ke mana.

Babu irin sunan rashin mutuncin da mutanen kudanci basa kiran mu dashi sakamakon suke da danyen manfetur a yankinsu, a wasu lokuta sukan kiramu da cima zaune, wasu lokutan ma tsageran yankin har tada jijiyoyin wuya suke akan a raba Najeriya, sunayin hakanne saboda tinkaho da danyen manfetur dake fitowa daga yankinsu.

Da zarar an kammala wannan aiki da Shugaban kasa Buhari ya kudarta kuma yake kanyi, tabbas zamu huta da ire-iren wadannan cin fuska da suke mana Muma tattalin arxikin yankin mu zai habaka fiye da yadda yake yanzu.

Samun nasarar wannan aiki shine mu sake bawa shugaba Buhari goyon baya, akasin haka kan iya haifarda tsayuwar wannan aiki domin dayawan manyan kasarnan ba son aikin suke ba. Kamar yadda tarihi ya nuna, shekaru da dama da suka wuce anfara aikin a jihar Gombe amma daga karshe aka wofintar dashi.

Domin haka ya kamata muyi karatun ta nutsu, mu kuma bawa tsohon dama domin cigaba da ayyukan alkhairin da yake yiwa wannan yanki namu na arewa, Kada mu sake kasarmu ta kuma fadawa hannun maciya amanar kasa, domin sunyi Shekara 12, ba tare damun amfana da komai ba, face tashin hankali da fatara da talauci tare da cin Hanci. Don haka ya kamata mu fahimta.

Kukan kurciya de.....

Gwamnatin Jahar Kano Za Ta Bunkasa Noman Rake Don Bunkasa Tattalin Arziki.Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada kudirin ta na bunkasa noman rake don bunkasa tattalin arziki.

Mataimakin Gwamnan Kano Dakta  Nasiru Yusuf Gawuna wanda kuma shine Kwamishinan Harkokin noma da albarkatun kasa ne ya sanar da hakan a yayin da ya ziyarci Kamfanin Sarrafa rake don samar sukari dake garin Kauran Mata a yankin Karamar Hukumar Madobi.

Dakta Gawuna  wanda ya bada tabbacin cewa nan bada dadewa ba wannan Kamfanin zai fara aiki ka'in da na'in, ya kuma bayyana cewa Kamfanin zai bunkasa tattalin arziki musamman a tsakanin manoma da matasa wadanda zasu sami aiyukan yi.

Mataimakin Gwamnan wanda mai bashi shawara akan harkokin noma *Alh. Hafiz Muhammad* ya wakilta yace sanin muhimmacin da noma yake dashi yasa Gwamnatin Jihar Kano take hada gwiwa da babban banki na kasa CBN ta cikin hukumar  NIRSAL don inganta lamuran da suka shafi harkar noma tun daga bada tallafi da jari da kuma da samar da kayan bunkasa sana'ar ta noma.

Da yake jawabi Shugaban Kungiyar masu noman rake dake garin Kauran Mata, Alh. Haruna ya bayyana godiyarsu bisa wannan tare da bada tabbacin hadin kansu ga gwamnatin jihar kano don bunkasa noman rake.
Ayau Talata 29/01/2019.

Abbakar DK
Daga Ofishin Mataimakin Gwamna.

MAHAIFIN KWANKWASO YAYI KIRA GA AL'UMMA DASU SAKE ZABEN GANDUJE A KARO NA BIYUAlh. Musa Sale Kwankwaso. Shine Mahaifi ga tsohon Gwamnan jahar Kano, Kuma sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya Wato Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, kuma shine Hakimin Karamar Hukumar Madobe yayi kira ga Al'umma da su sake zaben Dr. Abdullahi Umar Ganduje a karo na biyu.

Mahaifin Dr. Rabiu Musa Kwankwason. na fadin haka ne yayi da Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kai masa ziyara ta girmamawa yayi da yake kaddamar da yakin neman zabensa a karamar hukumar ta Madobi.

 Mahaifin Kwankwaso Yace "Hakika Duk wata Irin Karramawa ta Duniya Hakika Ganduje Yayi Masa A Rayuwa Da Hakane Yayi Kira Ga Al'ummar jihar Kano Dasu Sake Zaben Dr Abdullahi Umar Ganduje Kadimul Islam A Matsayin Gwamnan Jihar Kano A Zaben 2019 Mai Zuwa".

Daga Karshe mahaifin Kwankwason yayi wa Ganduje alkawarin zai aiki da dukkan Shugabannin al'umma dake l yankin nasa, domin tabbatar da nasara maigirma Gwamna.

Shima a nasa jawabin Maigirma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Yayi Alkawarin idan ya koma a karo na biyu, zai yiwa yankin aiki wanda yafi na baya.

Da alama de wannan kalamai na Mahaifin Kwankwaso yayi wa magoya bayan Ganduje dadi, domin suna ganin wannan kalamai wata babbar nasara ce a tattare dasu.

Monday, January 28, 2019

(Kudin Kamfen) WASU 'YAN FIM SUN YI AWON GABA DA MILLION 25. - Inji Ummi Zeezee.Da alama de a iya cewa baraka ta kunno kai a cikin 'yan kannywood magoya bayan Alhaji Atiku Abubakar. Dan Takarar Shugabanr Kasa a karkashin tutar jam'iyyar PDP biyo bayan Basu wasu makudan kudade da yayi domin su raba, amma da alama wasu tsiraru sun yi kashe mu raba da kudin, Kamar yadda aka jiyo Jaruma Ummi Zeezee na bayyanawa.

Waka de a bakin mai ita tafi dadi, gade abin da Umme zeezeen take cewa:

"Zuwa ga fati mohd, Sani danja, Zaharaddeen sani, Al'amin buhari da director eemrana....a ranar JUMA'AR data gabata mai girma dan takaran shugaban kasa na jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar. ya shirya wani taro da zai yi da yan fim da kuma mawaka na kannywood dan gane da siyasarsa sai dai kuma Allah bai bashi ikon zuwa ba sai ya wakilta Sir Bukola Saraki. Wanda daya zo taron ya bada kyautan makudan kudi miliyoyi ga jarumai da kuma mawakan kannywood, Wanda suke PDP suke kuma yiwa Wazirin Adamawa kamfen, ammah sai gashi saboda son zuciya irin taku kuda na lissafo sunayenku kuka raba kudin a iya tsakaninku, kawai ko wanne acikin ku ya dau naira million hudu da rabi saboda zalinci tsantsa.

To shi ai bukola sarakin ba ku kadai ya bawa kudin ba da zaku rabashi kawai a tsakanin ku shi cewa yayi ya bayar ga duk yan PDP na kannywood masu yin Atiku, wai ammah sai kuka fara kawo uzurin karya cewar wai acikin ku ko wani mutum ya gaiyato mutum hamsin ne domin taron shiyasa kuka raba kudin a tsakaninku Wanda kuma karya ne ba wasu mutane hamsin hamsin da kuka kawo taron domin nima na je taron kuma a matsayina na babbar yar PDP mai manyan mukamai har biyu baku bani nawa kudin ba. Sai bayan an tashi daga taron ne na kira actor Zaharaddeen Sani a waya ina tambayar nawa kudin wai shine dan renin hankali ya aikomin da naira dubu 25k kawai sai kace ya daukeni yar jagaliyar siyasa koko ince ya daukeni matsiyaciya ko yar yunwa.

Dan haka wannan wasika na muku ne domin in muku gargadi. Wallahi, Wallahi, Wallahi, in aka sake hada taron daya shafi Atiku Abubakar kuka raba kudi bani aciki to duk sai na kulleku a DSS na abuja baza a barku ba har sai kun biyani kudina domin na tabbatar acikinku ba mai connection din da nake dashi a Nigeria kuma ko wannan kudin ma dakuka dannemin rabo na naso na rufeku duka shine da nayiwa mamana waya na gayamata ta hanani tace rigima ba dadi in barku da Allah kawai zai sakamin shiyasa na rabu daku bawai dan ina tsoronku ba domin naga sauran mutanen da sukaje taron kuka hanasu hakkinsu tsoro ya hanasu magana.dan haka acikinku in akwai dan iska to dan Allah in an sake bada kyautan kudi akan siyasar atiku mutum yaci nawa yaga me zai faru! macutan banza kawai!!"

Sunday, January 27, 2019

MA'AIKATA MILIYAN 1.5M INEC KE DA BUKATA DOMIN GUDANAR DA ZABEN 2019Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa INEC ta na bukatar akalla jami’an gudanar da zabe da jami’an tsaro a kalla milyan 1.2 dominn gudanar da zaben 2019 a fadin kasar nan.

Yakubu ya bayyana hakan ne a Kano, inda ya jaddada cewa INEC na bukatar akalla jami’an tsaro 360 da za su kula da rumfunan zabe a lokacin da ake gudanar da zabuka a ko’ina cikin kasar nan.

Shugaban na INEC ya yi wannan bayani ne ta bakin Sa’ad Idris, Shugaban Cibiyar Zabe ta Kasa da ya wakilce shi.

An shirya taron ne a Kano domin sanin makamar aiki lokacin zabe ga jami’an tsaro.

Tare da hadin guiwar Cibiyar Tallafa wa Zabuka ta Kungiyar Tarayya Turai aka shirya taron.

Kasancewa Najeriya na da masu jefa kuri’a har milyan 84, Yakubu ya ce Najeriya ce ta biyu a yawan masu jefa kuri’a a kasar da ake dimokradiiya a duniya.

Yakubu ya hori jami’an tsaro su yi aiki tsakanin su da Allah kamar yadda doka ta tanadar domin a tabbar da samun ingantacce, sahihi kuma karbabbe.

Zaben 2019 zai zama ma’aunin kwarewar jami’an tsaron Najeriya

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ya bayyana cewa zaben da za a gudanar kwanan nan a Najeriya zai kasance wani ma’aunin auna zurfin kwarewar jami’an tsaron Najeriya.

Yakubu ya yi wannan jawabi ne a wajen wani taron sanin makamar aiki da kara wa juna sanin hanyoyin kula da daukar matakan tsaro a lokutan zabe.

An shirya taron ne a ranar Juma’ar da ta gabata da hadin kai Cibiyar Tallafa Harkokin Zabe ta Turai, domin tabbatar da an yi zaben 2019 lami lafiya.

Taron dai ya samu halartar wakilai daga Dakarun Sojojin Najeriya, Sojojin Sama da kuma Sojojin Ruwa.

Akwai kuma jami’an Kwastan na Kasa, akawi na shige da fice kuma akwai jami’an hana tu’ammali da kwayoyi.

Akwai kuma wakilai daga DSS, akwai FRSC da kuma NSCDC.

”Ita dai INEC ke da alhakin shirya zabe, amma su kuma jami’an tsaro aikin su tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umma da kayan zabe har zuwa bayan kammala zaben.

Yakubu ya ce ya na sane da babban kalubalen da ke tattare da jamai’an tsaro a Lagos, kasancewa ita ce jihar da ta fi sauran jihohi yawan masu jefa kuri’a har milyan 6, 570, 291.

Shugaban na INEC ya ce ya na da yakinin jami’an tsaro za su gunadar da aikin su tukuru domin su fitar da kasar nan kunya kuma su kara wa kan su kima a idon duniya baki daya.

SHIN KO KUN SAN "RAYUWA BAYAN MUTUWA" KUWA?Da yawa  daga cikin mutane suna Daukar cewa idan sun mutum aka binne su
shikenan rayuwa kuma ta kare daganan.

Wannan fahimta an gina ta akan kuskure babba kuma mummuna. Mutum bayan ya mutu yana shiga wata sabuwar rayuwa. Akwai rayuwa ta zaman Qabari da rayuwa ta bayan hisabi.

Zan dan yi tsokaci cikin littafin Allah da hadisai ingantattu a kan wannan al'amari. Tare da fito da al'amarin a fili na abin da zai kasance bayan mutuwar.

Idan mutum ya mutu farkon abin da zai fara fuskanta shine fitinar _Qabari_

Hadisi ya tabbata a cikin Bukhari da Muslim daga Anas dan Malik_ . Manzon Allah (S A W) ya ce: Idan bawa ya mutu aka sashi a cikin kabarinshi yana jin takun takalman wadanda suka binne shi. Sai mala'iku su zo masa: Masu tsananin kallo da harara. "Me za kace dangane da wannan mutum? To mumini sai ya ce: Na shaida haqiqa shi bawan Allah ne
kuma Manzon sa ne. Sai ace kalli hagu in ya duba sai yaga mazauninsa na *Wuta* sai ya razana, sai ace kwantar da hankalinka yanzu ancanja maka sai a nuna masa dama nan zai ga mazauninsa na aljanna.

Sannan duk zai gansu lokaci guda. za a bude masa *Qabarinsa* tsawon zira'i saba'in Sai ya ce wa: Mala'iku ku barni in koma gida in gaya wa dangina na samu *aljanna*, dangi da ya baro a duniya. Sai Mala'iku su ce: ka kwanta kayi barci, barci irin na ango.

 Kafiri kuma ko munafiki za a ce dashi, Me za kace dangane da wannan mutum? Sai yace: Kawai nima ina fadan abin da naji mutane suna fada. Sai ace ba ka sani ba, kuma ba ka karanta ba? Sai a doke shi da wata guduma ta karfe, zai yi wata Qara mai karfi wanda duk wata halitta zai ji ta banda mutum da aljan. A haka zai ci gaba da zama yana shan azabar
kabari har ranar da duniya za ta tashi.

Ya Allah muna rokon ka da ka kare mu da duk wata nau'i na azabarka Ameen.

Allahumma ajir-ni min-fitnatil-qa abar.

YA KAMATA KOWA YA SAN DA WANNAN AKAN DAKATARWAN DA AKA YIWA TSOHON ALKALIN ALKALAI NA NIGERIA - Datti Assalafiy


Abubuwa takwas (8) wanda shugaba Muhammadu Buhari ya fadi akan dalilan da ya sa ya dakatar da tsohon alkalin alkalai na Nigeria Mr Walter Onnoghen, ga abubuwa takwas da shugaba Buhari ya fada a jawabinsa:

1. Zargin boye wasu dukiyoyin da ya mallaka ba bisa ka'ida ba:
Shugaba Buhari yace: " Kasar nan ta shiga cikin rudani kan zargin tsohon babban alkalin Nigeria da rashawa tun lokacin da wata kungiyar fafutuka ta fallasa shi."

2. An gano wasu kudade daban da ya boye:
Shugaba Buhari ya ce bayan zargin rashin bayyana wasu asusun bankinsa, an gano wasu cinikayya da yayi na miliyoyin dala wanda bai bayyanaba bisa doka.

3. Onnoghen ya gaskata zargin da ake masa:
Shugaba Buhari ya ce gaskata zargin da akayi masa na daya daga cikin manyan dalilan da yasa aka sallame shi.

4. Kin murabus bayan tabbatar da zargin da ake yi masa:
Shugaban Buhari yace : "Abinda mukayi tunani shine bayan hannunsa yayi dumu-dumu cikin rashin gaskiya da kuma gaskatawan da yayi, Walter Onnoghen kamata yayi ya kare mutuncin bangaren shari'a ta hanyar sauka daga kujerarsa amma baiyi hakan ba."

5. Kokarin kotuna daban-daban na kare Walter Onnoghen:
Shugaba Buhari ya zargi Walter Onnoghen da yin amfani da kotuna daban-daban domin kare kansa da kokarin hana kotun CCT gurfanar da shi

6. Walter Onnoghen bai fi karfin doka ba:
Shugaba Buhari yace: "Nigeria kasar demokradiyya ce kuma babu wanda yafi karfin doka.

7. Ya kasance yana wanke wadanda aka kama su dumu-dumu cikin laifuka:
Shugaba Buhari ya zargi Walter Onnoghen da laifin amfani da karfinsa wajen wanke wasu mutane da aka kama da kashi a gindi cikin rashawa.

8. Umurnin kotun CCT:
Shugaba Buhari yace: " An nada sabon shugaba Alkalan ne bisa ga umurnin da kotun hukunta ma'aikatan Najeriya wato CCT tayi inda ta umurci shugaban kasa ya nada babban Alkali a kotun koli a matsayin shugaban Alkalai kuma shugaban majalisan shari'a."

Hukumar bincike ta ma'aikatan kudi a Nigeria, 'Nigerian Financial Intelligence Unit' ta binciko wasu asusun banki wadanda mallakan alkalin alkalai ne wanda shugaban Kasa Buhari ya dakatar.

Asusun da aka ganosu ta BVN guda hudu ne da ke dauke da kudade daban-daban kamar haka:
1- USD Account daga October 2012  zuwa September 2016  aka saka kudade dalar Amurka miliyon daya da dubu dari tara da ashirin da biyu da daru shida da hamsin da bakwai ($1,922,657.00), idan aka lissafa a kudin Nigeria kimanin naira Miliyan dari shida da saba'in da biyu da dubu dari tara da dari biyu da tara da naira dari tara da hamsin (N672, 929,950)

2- GBP Account daga 2012 zuwa September 2016 an saka kudade Pound dubu dari da talatin da takwas da dari hudu da talatin da tara (£138,439) idan aka lissafa a kudin Nigeria kimanin Naira Miliyan sittin da biyar da dubu dari bakwai da saba'in da takwas da dari biyar da ashirin da biyar (N65,758,525)

3- Euro Account a September 30, 2016 aka saka kudade Euro dubu hamsin da biyar da daro da hamsin da hudu (€55,154.00) idan aka lissafa a kudin Nigeria kimanin Naira Miliyon ashirin da biyu da dubu dari shida da sha uku da naira dari da arba'in (N22,613,140)

4- Naira Account daga september 2005 zuwa October 2016 an saka kudi Naira Miliyon casa'in da daya da dubu dari tara da sittin da biyu da dari uku da sittin da biyu  (N91,962,362)
.
Wadannan kudaden duk suna account din korarren Alkalin alkalai na Kasa Mr. Walter Samuel Onnoghen da yace mantawa yayi wai ko kuma kuskure yayi lokacin da zai bayyana kadarorinsa bai hada da su ba.

Shi dama maciyin amana ko a ido ana iya ganeshi, jama'a dole mu dage da addu'ah domin akwai manyan jibga-jibgan maciya amana masu satar dukiyar 'kasa cikin mukarraban shugaba Buhari, mu dage da addu'ah akan Allah Ya raba shugaba Buhari da maciya amana wadanda suke masa zagon 'kasa, zakuga Datti Assalafiy yana yawan yin addu'ah cewa Allah Ka raba shugaba Buhari da maciya amana

Wasu maciya amanar sai ranar da shugaba Buhari ya kammala mulkin Nigeria aka canza gwamnati asirinsu zai tonu, don haka tun ma kafin a kai ga wancan lokacin mu dage da addu'ah Allah Ya tonawa duk wani maciyin amana asiri

Saturday, January 26, 2019

ALHERIN ALLAH YA KAI GA JAN GWARZO SHUGABA BUHARI - Datti AssalafiyWannan sabon Alkalin Alkalai na Nigeria (CJN) Justice Ibrahim Tanko Muhammad Malami ne masanin addinin musulunci, Mahaddacin Qur'ani ne tsantsa, ya rubutu Qur'ani da hannunsa, kwararre ne a harcen larabci gashi kwararren 'dan Boko digiri uku (Phd) yake dashi a karatun lauya, yana da lambar girmamawa na CFR

A Mahaifarsa dake garin Doguwa karamar hukumar Giade Jihar Bauchi akwai wani babban masallaci dake bakin hanya, shi ya gina masallacin, kuma duk watan azumi shi yake tafsirin Qur'ani Maigirma a masallacin

Tabbas yanzu Baba Buhari ya samu CJN, bai da wasa, kuma yana da zafi, ga sanin Allah da riko da addinin musulunci tsantsa, ina mai tabbatar muku jama'a ku sa ido kuga aiki wajen wannan bawan Allah, zuwansa kan wannan kujera rahama ne daga Allah domin Allah Ya taimakawa shugaba Buhari wajen yaki da cin hanci da rashawa a Nigeria

Hankalin makiya addinin Allah kuma makiya cigaban Nigeria da Manyan jibga-jibgan barayin Nigeria maciya amana wadanda sukaci amanar Nigeria da 'yan Nigeria, da wadanda suka mayar da ta'addancin Boko Haram hanyar neman kudi; hankalinsu yayi mummunan tashi bisa nadin da shugaba Buhari yayiwa wannan bawan Allah a matsayin sabon babban alkalin alkalai na Nigeria

Jama'a ku dubi wani rahoto da BBC Hausa ta wallafa a shafinta na facebook, ga (screenshort) sun kawo rahoton cewa gwamnatin Amurka da Birtaniya sun nuna damuwarsu akan nadin da shugaba Buhari yayiwa wannan bawan Allah, sunce wai suna shakkun a samu sahihin zabe a Nigeria

Jama'a kuji zancen banza daga 'kasashen banza, ina ruwansu da zaben Nigeria, ko dai suna so su tabbatar mana cewa akwai boyayyen shirin da sukayi tsakaninsu da tsohon alkalin alkalai kan abinda ya shafi zaben Nigeria? tunda yanzu an koreshi boyayyen shirin nasu ya rushe kenan!,

Bayan haka, na ga tsageri 'dan ta'adda shugaban kungiyar masu rajin kafa 'kasar Biafra (IPOB) Nnamdi Kanu wanda yake zaman mafaka a haramtacciyar 'kasar Isra'ila ya bayyana cewa canza sabon CJN yana da nasaba da kokarin murda zaben 2019 wanda gwamnatin Buhari ke shirin aiwatarwa

Shekaran jiya na karanta rahoton da babban makiyin arewa da musulunci bakin arne bamaguje kuma tsohon ministan sufurin jiragen sama na Nigeria Mr. Femi Fani Kayode ya wallafa a shafinsa na Facebook (ga screenshort) a dalilin canza alkalin alkalai da shugaba Buhari yayi, nan take Femi Fani Kayode ya addinantar da al'amarin, ya fito ya caccaki shugaba Buhari, haka itama kungiyar kiristoci ta CAN ta addinintar da lamarin


Amma Alhamdulillah ina da niyyar nayi raddi da zaran na samu lokaci, kawai sai naga babban Malaminmu Ash-sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo har yayi raddi kamar haka:
HALAYYAR MUNAFURCI ABIN TAKAICI NE:

1. A ranar 20/2/2014 Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya yi wa Gwamnan babban bankin Nigeria Malam Sanusi Lamido Sanusi daga jihar Kano korar wulakanci daga kujerarsa, amma kuma karkatattun 'yan kudu, da masu akidar kin Musulmi da 'yan kanzaginsu na cikin gida da wajen Nigeria ba su ce kome ba; ba su ce an saba ka'ida ba, ko kuwa an nuna bangaranci da saba tsarin mulkin Nigeria ba!!

2. A cikin watan May 2012 National Judicial Council ta yi muraja'ar dakatarwar da aka yi wa Justice Ayo Salami daga jihar Kwara daga kan mukaminsa na President of the Nigerian Courts of appeals sannan ta yi umurnin a maida shi a kan mukaminsa nan take, to amma Goodluck Ebele Jonathan ya ki mayar da shi a kan mukamin nasa, kuma abin takaici karkatattun 'yan kudu, da masu akidar kin Musulmi da 'yan kanzaginsu na cikin gida da wajen Nigeria ba su ce kome ba; ba su ce an saba wa tsarin mulkin Nigeria, ko an nuna bangaranci ba!!

3. Don Allah in banda yin awu da sikeli biyu menene zaisa a soki Shugaban kasa Buhari don ya yi aiki da umurnin kotun da'ar ma'aikata ya dakatar da Justice Onnoghen daga kan mukaminsa har zuwa lokacin da za a yanke masa hukunci a gaban alkalin da'ar ma'aikata?? ~Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

Don Allah jama'a mu yiwa kawunan mu tambaya, wai shin mai yasa mutanen kirki a Nigeria basu soki wannan mataki da shugaba Buhari ya dauka na canza sabon CJN ba? amma me yasa hankalin mutanen banza, masu kaunar ruguza Nigeria ya tashi a kan wannan batu?
Tabbas akwai wata kullalliya a 'kasa, kuma daga dukkan alama Allah Ya wargaza kullalliyar da makiya suka 'kulla

Allah Madaukakin Sarki muke roko Ya taimaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a kan wannan babban aiki da ya sanya a gaba na yin yaki da manya-manyan masu cin hanci da rashawa da maciya amana a cikin wannan Kasa tamu Nigeria. Ameen.

YADDA NA TSINCI KAINA A HANNUN YAN DAMFARA - Daga Tasi'u Gumel.Wata Rana ina zaune a daki mamarmu ina dan hutawa bayan na hada kaya na da niyyar zanyi wanki, sai wani bawan Allah ya kirani awaya.

Maganar farko da ya fara yimin sai ya kira sunana yace (malam Tasi'u) kwana biyu gaisawa tayi wuya, ni kuma na amsa masa da cewa wlh yanayin rayuwane sai ana hadawa da uziri, muka gaisa cikin raha da nishadi, bayan mungaisa sai yake tambayana na ganesa kuwa,
Ni kuma nace masa a'a sai ya min bayaninsa, sai yace nine fa malam Ibrahim nace dashi gaskiya banganekaba, ya kara cewa Ibrahim nefa sai nace dashi Haryanzu banfa gane wayeba, sai ya kara cewa nine engine IBRAHIM, da naga ya dage da haka sai kawai na nuna kamar nasansa muka cigaba da gaisawa, bayan mungama gaisawa sai yace dani wani alherine yasa nakiraka, sabo da kusanci da yake tsakanina dakai naga ya dace kaima nasaka cikin wanan alherin.

Sai na gyara zama nace to ina jinka, sai ya fara dacewa "kasan nayi zaman gumel kuma ina aiki a kamfanin wutar nepa, to yanzu anyimin transfer zuwa manbila jahar adamawa, ina cen ina aiki a wani guri da ake aikin hakko wutar lartakilartaki", sai nace dashi Masha Allah to yanxu me kakeso namaka.

Sai yace yawwa wata harkallah zamu buga dakai na kasance ina aiki a karkashin wanan kamfanin namu kuma any time idan za'a siyo kaya nine nake siyowa amma yau oga ya nunamin cewa banine zan siyo kayanba kuma ni bazanso hakaba sabo da ina samun wani abu a duk lokacin da nazo siyan kayan bana so oga ya gane haka ya dena aikana, shiyasa nakeso katemakamin, zancewa oga kaine manager wanan kamfanin,zanfadama farashi yadda zamu samu wani Abu kuma zanhadaka da Shugaban kamfanin zai baka kayan cikin sauki idan oga ya baka kudi ta account naka, sai katurawa kamfani nasu abinda yayi saura bamune kadauki 30% ka turomin 70% .

Sai nace dashi banki ta takaba amma ni da bakowa, ba komaiba, kuma ni wanan harkan ba aikina bace tayaya zan iya tsara wanan planning? sai yace dani karkadamu nine zan tsarama komai, haka dai mukayi tayi harma ya nemi naturamasa recharge Card. Na 500 wai inda yake jejine bavu masu kati, wai gwamnatice take turamsu kati basiya sukeba gashi nashi ya kusa karewa kuma time na turowa beyi ba.

Haka dai na siyi kati natura masa, nan fa ya turomin number mai kamfanin yace min sunansa Alhaj yusif, ya tsaramin yadda zan masa bayani nayi masa abin mamaki babu shakka babu kokonto ya nuna ya amince zai siyarmin kaya, amma abinda ya fara bani tsoro da mamaki shine irin makudan kudaden da za'ayi amfanin dasu, domin yacemin abinda za'a siya katon (cartoon 50) kuma ko wane katon ana siyar dashi dubu dari biyar  Damn goma ,amma kuma idan ogansa yazo zancemasa farashin naira dubu dari shida da ashirin, kaga ko wane katon muna da ribar Dari da ashirin  12000 , Nanfa na fara sake sake ina zansa kudi sama da million biyar ni da koh dubu dari bantaba rikewaba. Haka dai mukayi tayi muna waya dashi Ibrahim, da mai kamfani alhj Yusif, da oga alhji aminu.

Muna magana da Alhaj aminu shine ya nunamin cewa bazasu yadda subani kudiba har sai sunga irin sinfurin kayana domin su tabbatar da qualities nasa, sabo gudun cucuwa nanfa na sanarwa alhj Ibrahim, yace na nemi alfarma agun alhj yusif mai kamfani, alhji yusif yace ya amince amma sai na ajjemasa deposit na kudi tukunna zai bani kaya sabo da dokar kamfanice haka, in takaicemuku karshe sun so su cuceni su wawushemin dan abinda Allah ya bani.

 Allah cikin ikonsa ya kiyayeni sai dan abinda baza'a rasaba.

Wanan shine takaiceccen abinda ya faru tsakanin da wannan Azzalumam mutanan, ina rokon Ubangiji Allah ya kare dukkan musulmi da fadawa cikin tarkonsu, sukuma idan masu shiryiwane Allah ya shiryesu, ida baza su shiryuba Allah kai kafimu sanin yadda zakayi dasu.
 Ina jan hankalin yan uwa muhankalta sosai da irin mutanan da zamuke mi'amala dasu acikin gida da waje, sabo da wasu a fuska suke mutane amma cikin zuciyarsu Allahne kadai yasan abinda yake ransu.

Wanan screenshot shine hoton numbobin da sukayi amfani dasu wajen yaudarata, sai kuma account number gashinan, dayan hoton kuma sunan abinda yace zamusiya da kuma recharge Card da naturamasa. Don haka yan uwa mukiyaye ubangiji Allah ya kara kiyayayemu da kiyayewarsa ameen.SHIN KO KUN SAN TASIRIN BUHARI KUWAGagarimin goyon baya da ake bashi a dukkanin zabubbukan da ya tsaya a baya har zuwa zaben shugaban kasa na shekarata 2015 dama bayansa, nasara ce wacce daidaiku ke samu a tarihi idanma akwai wanda ya taba samu bayan shugaba Muhammadu Buhari. Mutane suna masa biyayya tamkar su bauta masa.

Wannan irin goyon baya da biyayya daya samu yasa za'a iya yi masa da lakabi da  mutum na talakawa kuma jagoransu ko kuma ace masa Jan gwarzo. Mutum ne wanda akidarsa ta kubutar da shi daga dukkan wani laifi ko zargin almundahana.

Dukkan nasarorin Buhari ya cimma a rayuwarsa bashi da wani Uban gida daya tsaya masa.

Shin taya mutum bashi da dabi'u nagartattu zai iya cimma wannan nasara a siyasance?

Taya ya iya samun wannan yarda ta gaskiya har zabensa ba tare da yayi takidin wasu makuden kudade ba?

Taya ba tare da irin ginshikan siyasar da aka saba gani ba ya sami zunzurutun kuri'u da goyon baya a duk zabukan da ya tsaya har lokacin da yayi nasara?

Babu wani dan siyasa a Afruka da ya taba samun irin wannan nasara a baya, me yasa shi ya samu?

Ya shallake dukkan wani tsari ko binkice da ake dora ilimin gudanar da siyasa a kansa, shin me yasa?

Me yasa Sai Buhari?

Me nene tasirin Buhari?

Tasirin Buhari ya bawa talaka muryar magana.

Tasirin Buhari yana toshe dukkan wata kafar cin hanci da rashawa.

Tasirin Buhari shi ne rushe tsarin mutane tsiraru suna daukar dukiyar kasa tasu ce.

Tasirin Buhari ya kawo sauki duk rintsi.

Tasirin Buhari shi ne ayi biyayya ta gaskiya ba tare da neman sakayya ba.

Tasirin Buhari shi ne samar da yanci.

Tasirin Buhari shi ne samar da aikinyi.

Tasirin Buhari shi ne bunkasa ayyukan gona.

Tasirin Buhari shi ne kawo daidaito a duk wata kafar gudanar da mulki.

Tasirin Buhari shi ne kawo bunkasar duk wata kafa ta tattalin arzikin al'umma.

Tasirin Buhari shi ne dawo da tsaro.

Tasirin Buhari shi ne hakkin dukkan 'yan kasa ne ciyar da ita gaba.

Tasirin Buhari shi ne muradin Najeriya na gaba.

Tasirin Buhari tilo ne da ke burin kawo sauki ga kowa da kowa.

Wannan shi ne Tasirin Buhari.

Wannan shi ne alfanun tasirin Buhari.

Kamar yadda zaben shugaban kasa yake kara gabatowa, mun tabbata tasirin Buhari zai mamaye dukkan wani lungu da sakon da ka/ki ke.

Mun Amintu da Tasirin Buhari.

#Tasirin Buhari
#Mun Amince
#Mun Yarda da Shugabancin Buhari
#Yunkurin Mun Amince
#4 a kara da 4
#Mataki na Gaba
#BurinMu
#Matakin Najeriya na Gaba
#Shugaba Buhari Mai Gyaran Kasa

Friday, January 25, 2019

SABON KAKAKIN RUNDUNAR YAN SANDAN JIHAR KANO YAFARA AIKIRundunar 'yansandan jihar Kano ta nada DSP Abdullahi Haruna a matsayin sabon jami'in hulda da jama'a na rundunar.

sanarwar mai kunshe da sa hannun sa da aka rabawa manema labarai a yau.

DSP Haruna an haife shi ne a ranar 2 ga watan Fabrairu na shekarar 1984 a karamar hukumar Kiyawa dake jihar Jigawa, ya kuma kammala karatun digiri dinsa a jami'ar Abubakar Tafawa Balewa dake jihar Bauchi inda ya karanci Technology in Mathematics Education ya kuma yi bautar kasa a a jihar Abia.

ya kuma yi karatun sa na Masters a jami'ar  kimiya da fasaha ta Wudil a nan Kano.

ya kuma fito daga makarantar horas da 'yansand ta ta Wudil  a ranar 9 ga watan Yuli na shekarar 2012 wanda ya fito da matsayin ASP. ya kuma yi aiki a ofishin 'yansanda  na Mandawari da na Wudil.

Allah ya bashi ikon sauke nauyin da aka dora masa.

A SHIRYE GWAMNATI TAKE WAJEN CIGABA DA TALLAFAWA MATA - Dr. Hafsat Ganduje.Matar Gwamnan Kano Hafsat Abdullahi Ganduje ta jaddada cewa gwamnatin Kano ashirye take wajen cigaba da tallafawa dukkan harkokin mata ajihar nan...

Mai girma mai dakin mataimakin Gwamnan Kano *Hajiya Hafsat Nasiru Gawuna* ce ta bayyana hakan inda ta wakilci mai dakin gwamnan awani taron bada tallafin shinkafa da robobi ga mata guda (250) da tsohuwar babbar sakatariya ta ma'aikatar mata Hajiya Hafsat Muhd Kawu ta shirya amakarantar mata ta Dangana dake maza6ar Tudun-Wada cikin karamar hukumar Nassarawa.

Taron ya samu halartar mataimakin shugaban karamar hukumar Nassarawa Hon. Muhammad Shehu, Maigarin Tudun Wada, Hajiya Balaraba Abdullahi Ganduje, Hajiya Amina Abdullahi Ganduje, Saratu Gidado (Daso), wakiliyar kwamishiniyar harkokin mata, wakiliyar kwamishiniyar Ilimi, shugabar matan APC ta Nassarawa Yar Baba Tudun-Wada d.s.s.


Abbakar DK.
Daga Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano.

ILMIN MATA A JIHAR KANO YAKAMATA GWAMNATIN KANO TA BADA SHI KYAUTA. - Daga Auwal Dabai Unguwa Uku


A matsayina Na mai amfani da wannan kafa ta sada zumun ta Facebook Na ga yadda Na Kira ga Gwamnatin kano karkashin jagorancin mai girma Gwamnan kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, a gaskiya KARATUN yaya mata Yana da matukar amfani, domin kuwa idan ka ilmantar da Ya mace ka ilimantar da Al,umma.

A wannan yanayi Na tsadar rayuwa wanda a Yan zu haka mutane da dama basa iya cin abinci sau BIYU a rana, wani ma sau dayan sai ankai Ruwa rana. Walhi walhi walhi Allah iyayen Yara basa iya binyin school fees Na makaranta.

A makarantar dana ke kowarwa 99% Na daliban Sun kasa Biyan kudin makaranta saboda IYAYEN SU ba su da KARFI, a makarantar da Na ke koyarwa a kwai sama da Yara 50 wadanda har Yan zu basu dawo makaranta ba saboda rashin #800. Wasu rashin kudin dinka uniforms. Munyi iya korarin mu Na biya wasu sannan principal ta iya korarin ta Na yafewa wasu,

Na rantse da Allah MUNYI FIRST TERM Yan zu Muna cikin SECOND TERM sati Na Hudu har Yan zu ba'a kawo wasu daliban ba duk saboda kudin makaranta, walhi muna  zaune a ofis din principal wata mata ta kawo yarinyar ta, aka tambaye baba mai yasa Baki kawo ta da Wuri ba sai uwar ta ce kudin ne basu haduba Yan zu haka ma basu Hadu ba #400 walhi bamu da ciko a temaka mana walhi abun tausayi.

A gaskiya yakamata masu madafi'in iko da masu kudi mu rika temakawa akan harkar Ilimin mata a jihar kano.

KO kuma a tilastawa gwamnati ta mayar da ilmin mata kyauta a fadin jihar kano

#weNEEDfreeEDUCATION
#INKANOespeciallyMATA.

GAWUNA YA GWANGWAJE KUNGIYAR GAWUNA SOCIAL MEDIA SUPPORTER DA MOTAR HAWA.Maigirma Mataimakin Gwamnan Jahar Kano Dr. Nasiru Yusif Gawuna. Ya gwangwaje 'Yan Kungiyar (Gawuna Social Media Supporters - Kano State) da tsaleliyar Motar Hawa (Sharron) Domin cigaba da aikace-Aikacen Kungiya a korarin da take na tabbatar da 4+4 a jahar Kano Da Kasa Baki Daya.Kungiyoyi da dama suma sun samu wannan ta gomashin inda Inda Maigirma Mataimakin Gwamna yasa a gwangwaje su da Motoci, domin su je su cigaba da gudanar da aikacens.

Alokacin da yake mika musu mukullayen motocin mataimakin gwamnan wanda Alhaji Musa Yusuf Yawale (Tafidan Gama) ya wakilceshi yace su tabbatar sunyi tuki cikin nutsuwa ba na ganganci ba, su kuma guji shiga duk wajen da doka ta hana.

Wasu daga cikin Kungiyoyin sune Kamar Haka:--

* Ganduje Gawuna Youth Campaign Team.
* Ibrahim Ibro APC group
* Kano State Media Ambassadors Forum.
* Gawuna Social Media Supporters.
* NYG Loyalist Kano State Project.
* Ganduje Gawuna Kano State Collection Forum.

Dafatan Kungiyoyin da aka bawa za suyi amfani da ita yadda ya kamata,

Daga karshe ina tayya su murna.

DALILIN DA YASA AKA CIRE NI DAGA HUKUMAR TETFOUND. - Dr. Bichi


Dokta Baffa Bichi yace baya tsoro ya fito ya bayyana wasu abubuwan da minista keyi na cin amanar kasa,

Tsohon shugaban hukumar bayar da tallafi ga manyan makarantu ta Najeriya wato TETFUND, Dokta Baffa Abdullahi Bichi ya yi zargin cewa rashin jituwa ce tsakaninsa da ministan ilimi Malam Adamu Adamu ta kai ga sauke shi daga mukaminsa.

A wata hira da yayi da kafofin yada labarai Dokta Baffa yayi zargin cewa a daren wata Juma'a aka sanar da shi cewa ministan ilimi ya kai takardar kara gaban shugaban kasa inda ya bukaci a sau ke shi, kuma wannan ba shi ne karon farko da ake samun irin hakan ba.

A cewarsa, yana fuskantar suka sosai a tsawon wata da watanni a gaban shugaban kasa, amma ba wai saba ka'idar aiki ba.

Yace ko a lokacin da aka kira shi cikin dare domin sake tabbatar masa cewa za a cire shi daga mukaminsa, sai da ya tambaye laifin me ya yi, amma sai aka ce masa minista ya kai kara a kansa cewa ''wai baya iya samu na a waya, na biyu kuma wai bana daukan umarninsa na uku kuma wai ina magana da 'yan jaridu ba tare da sahalewarsa ba.''

Dokta Baffa Bichi yace shi ministan ilimi ya san cewa samunsa ya fi komai sauki domin kullum suna tare, kusan aiki biyu ma ya ke yi wato aikinsa na hukumar TETFUND da kuma aikin minista a ma'aikatarsu.

Ya kuma kar yata batun cewa ya taba karba kudin kwangila daga makarantun da hukumarsa ke bai wa kudi.

Dokta Baffa ya ce soke shi bai zo masa da mamaki ba domin tsawon shekara guda da rabi da yayi yana aiki yana cikin matsi saboda wasu ka'idojin minista da yake bijirewa.

Allah ya kyauta mai faruwa ta faru

Auwal Wadata Sansan

Thursday, January 24, 2019

(BIDIYO) AN YIWA ATIKI IHU A JAHAR KADUNA

Al'ummar Jahar Kaduna Sun yiwa Dan Takarar Shugaban Kasa a tutar Jam'iyyar PDP Alh. Atiku Abubakar, ihu yayin da ya shigar Jahar domin Yaki neman Zabensa.

Yayin da tawagar Atikun ta shiga jahar ta Kaduna, Jama'ah sunyi dafifi tare da fadin "Bamayi" "Sai Baba" dade sauransu, Domin kallon Bidiyon sai ku danna Link dake Kasa.

Shiga Nan Domin Ka Kalli Bidiyon.


Wednesday, January 23, 2019

KARAMAR HUKUMAR GWARZO ZATA BAWA GANDUJE KURI'U 1,100,000,00. inji Kwamishinan Lafiya Dr Kabiru Ibrahim Getso


inji Kwamishinan Lafiya Dr Kabiru Ibrahim Getso.

Ina da Tabbaci Matasa Mu na Wannan Karamar Hukumar Gwarzo Matasa ne Masoya Gwamna Kuma zasu zabi APC Daga sama Har Kasa
Ina Mai Tabbacin cewa Maigirma Gwamna da Gen Buhari sunci zabe sungama musamman a wannan karamar Hukuma Tamu.

Kwamishinan yaci gaba da cewa:

Maigirma Algon  Gwarzo Munci Zabe Mungama, Maigirma Gwamna Yayi Alkawari zai Kawo wa Maigirma Ge Muhammad Buhari Kuria 50000000 mu Iya Karamar Hukumar mu zamu Kawo 10000000 da 10000 Karamar Hukumar Bagwai  sunce suma zasu kawo 10000000 Kaga Maigirma Algon In muka Hada Kaga Milyan Dubu Biyu da Dubu Goma  Kaga iya wanna Kananan Hukumomin Guda Biyu Gwamna zai samu wayannan Kuriun Ragowar 390000000
Zaisamu a Ragowar 42Lg AJihar Kano

Maigirma Kwamishinan Lafiya Dr Kabiru Ibrahim Getso Jagoran Gandujiyya na Karamar Hukumar Gwarzo yana wannan jawabin ne a Wajan Taron Matasan Neman Yakin Buhari da Ganduje.


Ahmed Prince
Gandujiyya

Tuesday, January 22, 2019

BIYORA YA DAU ALWASHIN ZAI MAI DAWA ATIKU MOTARSA DA DALOLIN DAYA BASHI.


Biyora ya ce "Zan Mayarwa Da Atiku Mota Da Kudaden Da Ya Ba Ni Domin Yi Masa Yakin Neman Zabe,

"Zai kasance babban kuskure gare ni na cigaba da amfani da motar da aka bani don na yi kamfen, tunda dai na bayyana cewa ba zan yi kamfen din ba.


Hatta 'yan kudaden kashewar da aka bani duk suna nan a lissafe kuma zan mika su in sha Allah zuwa gobe.

Ba zai yiwu in hana mutane hasashe akan wannan lamari ba, sai dai dole akwai cikakkiyar gaskiyar lamarin da ni Biyora na sani suma wadanda suka bani daga gidan dana koma a kwanakin baya suka sani.

Na yanke shawarar dawowa tafiyata ta baya ne saboda wasu dalilan da nake ganin ta haka ne kawai zan fi samun saukin gudanar da rayuwata, koda kuwa naci gaba da yawo akan babur dina ne, tuni na saka an gyara mun shi don cigaba da zirga zirga akansa kamar yadda na saba a baya.

Kalubale dole na sake fuskantarsa a yanzu kamar yadda na fuskanta a baya kila ma ya fi na baya yawa.

In sha Allah bayanai za su fito ta yadda kowa zai fahimci dalilin da ya sa na yanke wannan sabuwar shawarar.

A shirye nake na jingine siyasa gaba dayanta idan har mutane ba su fahimta ba".

Monday, January 21, 2019

YAN SOCIAL MEDIA MAFI YAWANSU MAZINATA NE - Dr. Ahmad Gumi


Cikin karatun Muwatta Malik da ya gabatar ranar Asabar 19/01/2019 a cikin babin da yake magana game da DAGA SAUTI WURIN YIN TALBIYA.

Malam ya karanta Hadisin da ke magana game da haramcin daga muryar mace domin yin Talbiya sai dai ta jiyar da kanta.

Da wannan ne malam ya kawo hadisin da Manzon Allah SAW ya ce MACE DUKKANTA AL'AURA CE.

Akan haka malam ya jawo hankalin mutane musamman mata da suke daura hotunansu da mazan da suke daura hotuna da video na tsaraici da cewar Manzon Allah SAW ya ce dukkan gabobi suna yin zina, farji yake gaskatawa.

Wannan karatu yana da kyau mu watsa shi kowace kafa domin mu kubutar da yan uwanmu musulmi a duk inda suke musamman masu sha'awar daura hotuna "Half Naked".

Idan an ki jin maganar Malam, to aji ta Manzon Allah.

Danna nan domin ka kalli bidiyon.

Salisu Hassan Webmaster
08038892030
21/01/2019

[Abin Al'ajabi] YADDA 'YAN TSIBBU SUKA MAI DA WATA MATA TA KOMA KURA.
Hotunan wata mata kenan da ake zargin yan tsibbu ne suka barbade ta da hoda inda nan take ta koma wannan kura.

Lamarin da ya faru a unguwar Kofar Naisa dake nan Kano yaja hankali, domin zancen nan da nake daku caji Ofis din yan sanda na Gwale da aka garkame mutanen da ake zargin ya cika makil, haka kuma ita ma kurar an ajiye ta a nan zuwa abinda hali zai yi.

Wasu ganau da abin ya faru akan idan su sun hakikance cewa a gaban idanun su wadannan mutane suka bade baiwar Allan da hoda kuma babu shakku kan abinda sukace.

SHIN KO KUN SAN MAHIMMANCIN "VPN" KUWA?


Wasu dayawa basu san muhimmin amfanin VPN ba, kawai sundauka cewa ana amfani da shine wajen yin subs din bb akan android ko makamancin hakan.

Kasan dalilin samuwar vpn kuwa?

Da can kafin samuwar vpn manyan hackers ko kuma wasu gungun mutane dake aikata manyan aiyuka a internet to suna fuskantar matsaloli kadan daga cikin matsalar kuwa itace, akan zo a mamayesu har inda suke wato akamasu kenan.

Ana gano inda suke ne ta hanyar bin sahun bayanin dake boye a jikin browser din da sukayi amfani da ita.

Nasan zakuce to tayaya kenan? Baka taba shiga wani site ba kaga ance daga kasa kaza kake kuma ga ip da details dinkaba?

Kasashen da sukabawa tsaro kulawa ta musamman to sukan kama mai laifi wanda ya aikata laifin a internet, ta hanyar bin sahun details na browser din daya aikata laifin.

Wannan kamun da akeyimusu ne yasa suka fito da wata dabara, dabarar itace idan kana wani garin to idan kanaso ka aikata wani laifin sai katashi daga garinka katafi wani garin can kaje ka aiwatar, haka sukaringayi har dabarar samar da vpn tazo musu.

VPN dinma dai sai ya zamto kamar dai dabararsuce ta karshen, wato kana gari kaza sai katashi kaje gari kaza ka aikata laifin, koda anbi sahun details na browser dinka to garin za'aje inda ka aikata laifin alhalin kai kuma kabar garin.

To idan kaduba tsarin vpn zakaganshi akwai servers dayawa akansa, misali idan kabude DROIDVPN zakaga servers kamar na kasashen USA da ENGLAND da NORWAY da dai sauransu.

Amfanin hakan shine, idan kana nigeria to zaka activating din server ta kasar USA to kome kayi da wannan browser din taka to kawai daga USA kayi, kaga koda anbi sahun details na browser dinka to za'a USA kawai kuma koda anje can to kai kana nigeria abinka.

Wannan ne dalilin dayasa suka samar da vpn domin saukakawa kansu wajen wahalar tashi sutafi wani garin ko wata kasar yayinda suke kokarin aiwatar da wani aiki na laifi a internet.

Wani amfani kuma daban dayake tattare da vpn shine, idan kasar da kake xaune sun kulle wani site da wanzuwa akasar to takan vpn zaka iya bude wannan toshashshen site din, misali ace anan nigeria sai hukumomin kasar nan sukaga ai kawunan talakawa yana wayewa da zarar suna amfani da Facebook, sai sukace antoshe facebook gabadaya a nigeria, to fa inhar antoshe din to badama ka iya bude facebook, to amma idan kasan meye vpn to takansa zaka iya, domin da xarar kabude vpn dinka sai kaxabi wata server din walau ta usa ko england kawai, to kanayin hakan zaka iya hawa facebook din sbd ai bada server din nigeria kake using ba, kayi replacing din server din nigeria da ta wata kasar.

Akwai vpn dayawa kuma kala - kala, akwai na symbians dana androids da kuma na system wato na computer kenan.

Manyan kwari dayawa na duniya basa hawa internet batare da vpn ba sbd kare kansu daga tarkon fadawa tarkon hacking, zai kareka daga tarkon hacking sbd kana nigeria amma kuma kana makale da server din USA kaga ka wahalar da wanda zaiyi kokarin hada maka tarkon.

Inafata yanzu kasan wasu abubuwa kadan daga cikin amfanin VPN ko? Vpn din dayafi dadin sha'ani musamman ni awajena shine DROIDVPN

Wednesday, January 16, 2019

SAKO MAI MUHIMMANCI GA MASOYA HON. SHA'ABAN SHARADA daga Umar Ibrahim


Sakamakon shiga rudani da kuma kiraye-kirayen waya da masoya suke ta yi bisa hukuncin da kotu ta yanke a safiyar yau game da zaben fidda gwani na jamiyar APC da ya gabata a watannin da suka gabata cewa sunan muntari ishaq ne ya kamata ya kasance a matsayin Dantakara ba Hon. Shaaban na. Ina so nayi amfani da wannan dama na sanar da ku cewa har yanzu Hon. Shaaban Ibrahim Sharada ne halattaccen Dantakara bisa dalilai kamar haka:

Na farko dai kuna sane da cewa a watannin baya kune kukayi fitar dango wajen dangwalawa Hon. Sha'aban Sharada har ya zama dantakara da jami'an zaben da suka jagoranci zaben suka tabbatar.

A halin da ake ciki yanzu kuma sunansa ne a dukkanin ofishin hukumar zabe, na kasa, jiha da karamar hukuma a matsayin wanda jama'ar Municipal suka zaba da ya wakilcesu a zabe mai zuwa.

Kuma, ba wai fa shikenan don kotu ta yanke wancen hukuncin an gama ba kenan muntari ya zama dantakara. A'a, muna da dama muma ta daukan matakai daban-daban. Wanda kuma cikin matakan da za mu dauka mune da nasara inshaallah.

Don haka, ina kira da masoya ku kwantar da hankalinku kuma ku ci gaba da yada yada manufofin Sha'aban Sharada na alkhairi da yake yi, ya kuma ke son ci gaba da yi.

Monday, January 14, 2019

KYAUTAR JAMB DAGA SALIU MUSTAPHA FOUNDATION


Assalamu Alaikum!

Wannan gidauniya ta fito da tsarin taimakawa Dalibai wadanda suke da bukatar zanaa jarabawa Jamb, kuma basu da hali. Don haka wannan kungiya ta fito da tsari domin taimakawa,

Wannan kungiya ta fito da tsari domin masu bukata su samu su nemi wannan tallafin cikin sauki, tsari kuwa shine yin rijista ta hanyar Online, Domin duk mai bukata zai shiga Website dinsu ne zai ga Form sai a cike, da zarar mutum ya cike, su kuma zasu duba idan ka chanchanta su biya maka,

Duk da abun yazo a kurarren lokaci, naga bari na sanar da yan uwa ko Allah zai sa wani ya dace da wannan tallafi, domin gobe suka ce zasu rufe wannan rijistar, don haka sai ayi kokari a cike ko Allah zai sa da rabo.

Domin yin rijistar sai ku shiga inda aka rubuta (Shiga nan dom....). Da zarar ka danna zai kai ka wajen fom din sai ka cike. Kar a manta ayi amfani da Browser ko chrome wajen cikewa.

Shiga nan domin yin Rejistar

Allah yasa a dace.

Sunday, January 6, 2019

(GLO) YADDA AKE SIYAN DATA 1288MB DA #200 KACAL...


Assalamu Alaikum!
Biyo bayan lambar yabo (award) da kamfanin glo ya samu kwanan nan, yanzu haka sun kirkiri wani sabon data bundle da zai baka damar samun GLO 1.2GB a Naira dari biyu kacal.
Datar bata da restriction ma'ana zaka iya yin komai da ita a kowane lokaci ba wai iya Facebook, whatsapp, Instagram, YouTube ko kuma weekend ko night kawai zaka iya amfani da ita ba.

Wanda yake bukata sai ka fara loda katin 200 a wayarka sannan ka danna wadannan lambobin: *777# sai ka danna kira. Menu zai bude maka sai Zabi Lamba 1, (Buy Data) ka danna OK na wayarka, wani fejin zai bude maka sai ka sake zabar lamba 1 (Buy 3G - 4G Data Plan) ka kuma Danna OK/SELECT sannan sai ka Sake zabar lamba 5, (Special Data Offer) sai ka danna Ok, Sai ka kuma zabar lamba 2 (1.2G #200 3days) kana danna OK anan take zasu kwashe 200 daga wayarka su kuma baka 1.2GB wato MB 1288 kenan.

Validity din data din kwana uku (3) ne saboda haka ka tabbatar ka cinye  ta cikin kwana uku daga ranar da kayi subscription din. Idan baka cinyeta ba to zasu kwashe kayansu ne.

Wanda yake da tambaya, ko bai gane wani abun ba sai yayi bayani.


Dafatan de kowa ya fahimta.

Popular Posts